👩👩👧👧WASU MATAN 👩👩👧👧
@2021~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
Story and Writting
by
Zainab Sardaunerh🔔📚
JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
⚜️©J.A.W📚🖌️DIYAH
{ Short story }Labari ne mai cike da ban tautsayi tare da soyayya mai zafi
Wannan littafi na kuďi akan farashi Naira #300 kachal.zaku biya kudin ta wannan account number 2136300504 Sanusi A nura U B A,sai kiyi screen Short ki turo ta wannan WhatsApp number 09066484295 ko kuma 08104093636.Za ku iya turo katin MTN na dari uku ta wannan number 09066484295 domin karin bayani sai ku tuntubeni ta wannan number 09066484295
©️♤♡ Zeesardaunerh
Thanks for the prayers Fan's Allah ya saka muku da mafificin Alkhairinsa Thanks alot
Page75~~76
Da safe bayan sun kammala shirin zuwa makaranta suka dibi kunu da niyar su karya dashi kafin su tafi,kurbawa Salmat tayi taji kunu salaf ba sugar ta dubi inna Saude da ke fitowa daga dakinta tace,
"innarmu ya naji kunun ba sukari? "
"banida kudin siyensa"
Cewar inna"amma ai dazu da nafito daga wanka naga lokacin da Baffa ya miko miki kudin sugar kafin ya fita"
"to karyar da na saba yi miki ce ya bani hana wa ne nayi kada Allah yasa kisha"
tafada tana shiga kitchen din ta debo nata itama tazo inda su Agla ke zaune ta ajiye kunun ta shiga daki da niyar ta dauko sauran sikarin da ta rage jiya.Ajiye kunun Salmat itama ta mike ta shiga dakinsu,naira dubun da ta ajiye tabawa inna Saude ta dauko ta yi waje,Aliya na tambayar ta ina ta yi amma bata tsaya bata amsa ba ta fita.
Wurin mai siyar da kosai ta nufa ta siyo na Naira dari biyu sannan ta wuce shagon malan Abu ta siyo sikarin dari madara pick sachet ukku ta dawo gida.
ko da tadawo inna Saude nata banbamin fadan ta ajiye sikari bata gani ba.
Dariya Salmat tayi tare da cewa inna,
"kisha abinki hakan mana inna,kila kusu ne ya santale miki sikarin mukam dai baza musha abu salaf ba"
ta karisa tare da fiddo sikarin ta zubawa kanta da Agla,sannan ta fito da madarar ta bawa Agla sachet daya ita ta zuba dayan ta ajiye daya.Spoon ta dauko guda biyu itada Aliya sannan ta buda ledar kosai ta ajiye tsakiyar su tana cewa,
"Adda Agla muyi sauri mu karya lokaci na tafiya kar muyi latti"
Da "to" Aleeya ta amsa mata ya yin da inna ta kame kamar status ta kallon bakin Salmat da ke shan dadi.
Duk kallon nan da takewa Salmat tana lure da ita,Aliya bata wani sha sosai ba ta mike kosan ne kawai taci da d'an yawa sai a sannan ta lura da inna wacce ta tokare bakin kofa tana kallon su.
Ta so ta tambayi Salmat ina kayan inna amma tana gudun aras ta fado kanta gashi dama a gidan inna bata bari suna zance da turanci cewa take zaginta ne sukeyi.

YOU ARE READING
WASU MATAN✔
Short Storyبسم الله الرحمن الرحيم WASU MATAN Littafi ne da ya kunshi halayen matan mu na yanxu ko nace matan zamani,halaye masu kyau da ma akasin su. Wannan littafi ya kunshi Kishi,kiyayya,tausayi,dama sauran su. INA ROKON UB...