👩👩👧👧 WASU MATAN 👩👩👧👧
@2021
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
Story and Writting
by
Zainab Sardaunerh
🔔📚
JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
⚜️©J.A.W📚🖌️
Assalamu Alaikum sunana Ummu Maleek
Muna siyarda kayayyaki masu kyau da inganci
munada maganin Ni’ima macce duk rashin ni’imarta Insha allahu rabbi zataji ni’ima tamkar korama ±💃💃💃💃
Muna da maganin infection ko wanne iri duk nacin infection Insha allahu rabbi kikayi amfani dashi zai rabu dake
munadasu Tsumin kala kala Munada gumbar nonon rakumin munadata dabino
Akwai mallakar miji masu zamu🔥🔥wanda inki kayi amfani dashi mijinki ko dutsene shi saiya tanka
Munada Emergency thghting duk yadda kika kai da budewa zaki hade tsaf Insha allah’ akwai hips Elargenment akwai breast Elargenment
Munada kayayyakin mata kala da iri masu zafi🔥🔥tamkar boom😻😻sha yanzu magani yanzu
Duk abinda kake da bukata zaka iya nemana ta👉07037112549
©️♤♡ Zeesardaunerh
Page 91~~92
INDIA,NEW DELHI
Duk wani bincike da ya shafi DR A.M A ga me da wuraren da yake zuwa time din da yake fita etc Dr Ayshert Mas'ud mai nera ta gabatar tare da taimakon kawarta Shyla Kumar.
Ako ina yake tana da kusa da shi except makaranta da kuma gidansa,da ace da hali ko gidan nasa da tashiga but security na chan ba dai suke da na nan ba,gidansa nada matakan tsaron da ba yadda za'ayi ta shiga ciki but duk hakan ba laifi tunda zata iya ganinsa daga nesa har ta shaki kamshin sa.
***********
KABEER
kamar yadda abokanan sa suka bashi shawara ya dage da Addu'a da kuma sadaka yayin da yake saka malamai suna yi masa Addu'a da kuma saukar Al-qur'ani.
MARYAMA
Ba yadda ta iya dole ta dauki shawarar mahaifiyar ta ta lura duk wani jidali,fitina da kuma haukar da zata yiwa Kabeer baya kulata gashi ya maida gidansu gurin zuwa ko da yaushe yana chan wani lokacin ma idan ya fita tun safe sai dare yake dawowa amma ta shirya tsaf domin maida KABEER a tafin hannun ta kamar yadda yake ada sai abunda tace yake yi.
Don haka yau yana fita tasaka Ummanta ta turo mata kanwarta Nafeesat tayi mata gyaran gida tare da girki.
Ba karamar wuya Nafeesat taci ba domin gidan yayi kahurar daud'ar tsiya wacce ba tada misali musamman dakin Anty Gimbiya(Maryama) domin shi na Kabeer yana gyaransa lokaci zuwa lokaci.
Kitchen ba magana wasu kwanukan ma har sunyi tsutsa wasu kuma sun bushe cikin ran Nafeesat take cewa "wlh Anty Gimbiya ba karamar kazama bace yaseen yah K.B yana da hakuri"
Haka Nafeesat ta kwashe lokaci tana gyaran gidan sai biyu ta kammala sai kuma ta dawo d'aura girki,tuwo da miyar ganye ta girka gidan sai kamshi yake tashi.
Misalin 6:30 ta kammala ta zuba a warmers tajera kan madai_daicin dinning table na su. turaren wuta tafara yiwa gidan da dakunan Maryama ta amashe tana cewa "
Jeki kitchen ki dibarwa Umma abincin ki biya muku dashi "
Nace" toh Anty Gimbiya" tare da wucewa kitchen a raina nasan ba aikin Allah da Annabi bane tayi mun.
Bayan tafiyar Nafeesat Maryama ta warware kullin da ke zanenta ta fito da kullin turarukan da Ummanta ta amso mata da gurin boka Dajjal ta zuba turare har kusan kala ukku acikin kaskon turaren tayi dakin Kabeer duka ta turareshi har toilet dinsa sannan ta fito pallon ta turareshi shima tare da sakar gidan.
Tana cikin turaren Nafeesat ta fito daga kitchen, cikin toshe hancin ta da mayafin kanta take cewa "
Haba haba Anty gimbiya Fissabilillah wannan wane irin banzan turare ne haka don Allah,abu ba dad'in kamshi idan kasha keshi sai kanka ya tsara.
"bansani ba don Ubanki kinsan dai banason shishigi a lamurana Nafeesat don haka ki kama kanki"
"Allah baki hankuri Anty Gimbiya, daga tambaya sai zagi Allah huci zuciyar ki amma gaskiya na fada kuma yanzun barmiki gidanki duk abunda zakiyi kiyi"
"It's better for u"
Gyara jikinta tayi ta dauki jakarta tare da kulolin da tasaka abincin a ciki ta sallama da Maryam ta wuce.
Napep ta tara bayan ta shiga ta yi masa kwatancen gidan su ya tafi.
Bayan Nafeesat ta tafi Maryama ta zauna tana chart tare da karanta pages din da aka tura a group na littafin da take bibbiya na kud'i mai suna NAFI KARFIN KISHIYA bayan ta kammala karanta page dayan da aka tura ta hau yin comment.
Duk cikin littafan da take karantawa tafi son wannan book din domin yana bada wuta sosai.
Sai misalin takwas da rabi ta tashi ta shiga wanka tayo Alwala ta fara salla, magrib tayi sannan Isha'I domin lokacin da akayi magrib tana karanta littafi ne baza ta iya ajewa ba(Allah ya shirya)
Bayan ta kammala Sallar wacce ko minti biyar ba tayi tana yinta ba ta shire hijab ta wuce gaban mirror gaba daya ta game jikin ta da turen gurin boka dajjal sannan tayi na tsugunno sannan ta saka wata arniyar sleeping dress ta dawo parlour ta hakimce tana taunar cingom tana danna waya.Mantawa tayi bata saka magani a cikin abincinsa ba ta yi sauri taje ta bar_bada sannan ta dawo ta zauna.
Ko minti talatin da zama ba tayi ba tayi kukan motarsa ya dawo gyara zaman rigar ta tayi tana dan janye ta kasa yadda za su d'an fito su dauki hankalinsa.
Da bismillah ya shigo gidan tare da Addu'ar shiga gida wani irin kamshi wanda bazai iya tantace tsakanin kamshi ko wari ya bugi hancinsa sai da kansa ya tsara cikin sauri ya lalibo Addu'a ya rinkayi yana ida shiga harabar gidan.
Mamaki ! al-ajabi duk sun cika zuciyar Muhammad Kabeer addu'ar ma ta subuce a bakinsa sai a zuci yake yi wai yau gidan sa ne ko kuwa ya yi b'atan hanya mai kammala tunanin ba yaji Maryama a jikinsa ya yin da baisan time din da ta iso ba kawai ji yayi tayi hugging dinsa tana cewa.... "welcome home my Habiby"
Zeesardaunerh ce
( Y'ar karamar su babbar su👧🥰🤩)
# comment
# like
# share
comment and vote d'inku shike Karamin kafin guiwar typing💋
YOU ARE READING
WASU MATAN✔
Short Storyبسم الله الرحمن الرحيم WASU MATAN Littafi ne da ya kunshi halayen matan mu na yanxu ko nace matan zamani,halaye masu kyau da ma akasin su. Wannan littafi ya kunshi Kishi,kiyayya,tausayi,dama sauran su. INA ROKON UB...
