👩👩👧👧 WASU MATAN 👩👩👧👧
@2022
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
Story and Writting
by
Zainab Sardaunerh
🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
⚜️©J.A.W📚🖌️
بسم الله الرحمن الرحيم
Da sunan Allah mai rahama mai jinkai
Ya ALLAH YADDA NAFARA WANNAN LITTAFIN LAFIYA KA YARDA NA KAMMALA SHI CIKIN KOSHIN LAFIYA.
SADAUKARWA
WANNAN LITTAFIN SADAUKARWA NE GA FADILA SANI BAKORI,HAFSAT ZUBAIRU SAMBO(Autar mama)AMINA MUHAMMAD BASO, MUMMYN SHUKURA,ASIYA MUHAMMAD,MAMAN AMATULLAH,MAMAN NUSAIBA,RAHMA KOISE,SISTER MIE AND HABIBTY NASMAH LOVE U ALL GUYS♥️♥️♥️
GODIYA
GODIYA MARA MISALI GA PHARTY BB,UMMU MAHIR,MOM ISLAM,UMMU ABDALLAH DA KUMA DAUKACIN MEMBERS NA JARUMAI WRITTER'S ASSOCIATION,MY DEAREST FAN'S SON SO FISSABILILLAH💓💓💓
BOOK 2
Page 71&72
"eh..um..shi naje siya,ba gashi kina gani a hannuna ba" ta faɗa tana nuna mata ledar hannunta
"naga kin jima ne dayawa shiyasa nayi tunanin ko ba gurin mai yalon kika je ba"
"wallahi canji ne bayada shiyasa na jima sai da ma na barmasa naira ɗari saboda rashin canjin"
"tou muje mai agwagwa yana ta jira an tsayar dashi"
Nauyayyiyar ajiyar zuciya Hanne ta sauke lokacin da taga Umma Hadiza ta bata baya, a zuciyarta tana cewa "Allah na gode maka da baka bari ta ritsani ba a lokacin da nake wayar"
Bada ɓata lokaci ba suka isa Durbawa,mai napep yace sai an ƙara masa kuɗi saboda jiran da ya yi,kuɗin Umma Hadiza ta ƙara masa sannan suka fara tafiya.
Sun ɗau dogon lokaci suna tafiya har sai da Umma Hadiza ta fara korafi kafin suka.
Kamar yadda suka shirya da Hanne haka bokan ya aiwatar,dama can Umma Hadiza bata ƙaunar Azeema gashi ɗuk ya ƙara mata tsanarta,ba abunda take so face a cire soyayyar Azeema acikin zuciyar Abubakar ko ta halin ƙaƙa,a yanda take ji zata iya aikata ko minene domin fitar da Azeema daga rayuwar Abubakar,ta wannan hanyar suka yi amfani suka tatseta kuɗaɗe masu yawa sauran kuɗin ma sai ta siyar da wasu ƙadarorinta zata kawosu.
Haka ta tafi gida da yaƙinin cewa wahalarta tazo karshe, ɗanta zai dawo hayyacinsa ya zama mutum kamar kowa,ya rabu da waccan laƙaƙƙar, ya yi rayuwar aminci da farinciki tare da matar da ta aura masa(rashin sani yafi dare duhu)
Yayin da Hanne da ƴarta Binta suka koma gida cike da farinciki mara iyaka,komi na tafiyar musu ne a yanda suka tsara,ada suna tunanin ina zasu samu kuɗin yiwa Abubakar Asiri tunda Binta ta daina yawon gantali ta yi aure,yanzu gashi Umma Hadiza ta ɗauke musu nauyin aikin kallo ne kawai nasu sai jiran sakamako,ba wahalar biyan kuɗi ba wahalar saka masa magani a abinci ko abinsha.
Lokacin da Binta ta koma gida Abubakar da Azeema suna tsakiyar gidan ko mi suke oho,cikin mamaki Abubakar ya kalleta ganin ta fito daga waje kuma bai san fitar ta ba,kamar wanda aka matsi bakinsa ya furta cewa "Ke daga gidan Ubanwa kike?da izinin wa kika fita?"
YOU ARE READING
WASU MATAN✔
Historia Cortaبسم الله الرحمن الرحيم WASU MATAN Littafi ne da ya kunshi halayen matan mu na yanxu ko nace matan zamani,halaye masu kyau da ma akasin su. Wannan littafi ya kunshi Kishi,kiyayya,tausayi,dama sauran su. INA ROKON UB...
