💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*
https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl
_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_
*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
*Join me on Telegram*
https://t.me/joinchat/yZ0tHN29JA4wMzZk
*Join me on Whattpad*
https://www.wattpad.com/
*Page* 49~~50
"Wai mike damun ki ne Aysha?haba dan Allah kina son jawo mana raini a Asibitin nan wannan wallahi,kinga yadda sauran likitoci da nurses maza da mata ke kallonki?&
kaf cikin Asibitin nan waye baisan soyayyar da kike yiwa Dr Aliyu Muhammad Ahmad ba"
"ya ki keson nayi ne Rabi'at?zuciya ta ce!zuciyata ce!!zuciyata ce!!!
"itace silar duk abun da kika ga A.M ya yimin,kar ki manta wacece Aysha! samari nawa na wulakanta, ko a yanxu Allah kad'ai yasan adadin masoyana wad'anda dama kawai suke jira na basu,amma miyasa na share su duk wannan abun fa saboda soyayyarshi ce! shin ban chanchancii ya SO ni ba ne Rabi'at ?
"abun da nake son ki fuskanta Aishert shine wannan abun da ki keyi fa shine news din dake yawo a cikin Asibitinnan, samari da dama suna farin cikin hakan saboda wulakancin da kike musu gashi kuma wanda kike yi kansa ya nuna baisan kina yi ba"
"ni fa wannan ba ya damu na Rabi'at in har A.M Zai karbi soyayyata, ki duba fa saboda shine na dawo wannan kasar,saboda shine na dawo sokoto saboda shine na nemi aiki a wannan Asibitin amma duk da hakan ban chanci ya soni ba ?
Tautsayin ta duk ya cika Dr.Rab'iat ta ma rasa abinda zata ce mata domin ta sanyaya mata zuciya,ta lura cikin bacin rai take a yanxu.
Sautin ne ya fara tashi a jakar Aisha,hannu Dr.Rabi'at Tasa ta dauko wayar ta mi kawa Aysha.
Ba tare da ta duba no din ba tasa hannu ta kashe kiran(rejecting),sake kira akayi ta share wayar har ta sinke amma duk da hakan mai kiran bai hakura ba ya sake kira.
Daukar wayar tayi a hasale domin wannan mai kiran ya takura mata budar bakin ta bayan ta aza wayar a kunnenta sai cewa tayi,
"wai wani irin rashin hankali ne ake damun mutum da kira ko na gayama ina bukatar hakan ne nonsense msstwwwssss"
ta yanke kiran ba tare da ta saurari ko wanene ba.
"kin gani ko wannan yana cikin abinda yasa ki ka kasa samun Hydar"
dago idanuwanta Ayshert tayi tana duban Rabi'at cikin mamaki,
"eh hakanne,Aisha wulakanta mutum ba komi bane a gare ki,musamman wanda yace yana sonki,ke bakya tunanin cewa suma suna jin abinda kike ji ne a zuciyarki?ko suma ba zuciyar ce ke da su ba?
"dakata Rabi'at kar ki kara batamin rai"
"ba maganar bacin rai bane kawai gaskiyace, ki gyara ko da Allah zai taimakeki.
" sannan ki cigaba da addu'a ki rage damuwa da tunaninsa a ranki idan ba haka ba hawan jini zai samiki wallahi"
"naji
"amma baki dauka ba ko?"
"Ni nace miki hakan?"
"a'a alamunki ne suka nuna hakan!kinga ni na tafi na duba maras lafiya sai anjima "
Dr Rabi'atu Ta fada tana ficewa daga office din ya yin da Ayshert ta zurfafa a tunanin rabin rayuwarta.
Da kyar ta dan yi wani aiki yau a office din domin rayuwarta bata yi mata d'adi,agogon hannunta ta kalla lokacin tashin Dr.A.M ya kusa kuma tana bukatar sanyashi a idonta kafin ya tafi domin hakan zai saukaka mata radadin da take ji.Saura minti biyar ya wuce ta fito daga office d'inta domin ta jira isowarshi amma kash tana bisa hanya Dr.Jameela ta tsaida ita da magana ko da ta isa har ya wuce(amma djameela kin iya bakin ciki🤣)
Itama motarta ta shiga ta figeta da gudu domin bataga amfanin zamanta a Asibitin ba.
*********
Bayan mun taso daga islamiyya muka ci abinci Salmat Ta masa sai munje mun kwantaba yadda banyi da ita ba amma taki,domin naso ne mujira baffa da ya fita,wani makocinmu ne ba ya da lafiya shine suka tafi kaishi Asibiti yanzu.
Alwala nasa ta yi nima na yi tare da yiwa Inna saida safe muka shiga dakin mu itama Inna ta shiga nata.
Bayan kamar minti ar'ba'in da kwanciyar mu Salmat Ta fasa kara wacce tasa na farka dama bana da nauyin bacci.
Ihu kawai Salmat ke yi da gudu Inna Saude ta fito daga d'akinta ta yo namu ko da shigo ina tambayar Salmat Lafiya amma ta ki magana sai ihu take zabgawa.
Gunta Inna ma tayi itama tana tambayarta,
"Ke Salamatu Lafiya miya faru"
ina Salmat Baki yaki yin shiru.jijjigata Inna Saude Ta rinka yi tana cewa,
"wai ba tambayarki na ke ba miya faru ne ??"
cikin rarrabewar murya Salmat tace,
"In.. Inna ba.. barawo.... barawo Inna"
zaro idanuwa nida Inna mu ka yi har muna hada baki wurin cewa,
"b'a..mi?"
"b'arawo"
Salmat Ta idar mana.
"inna tace barawo fa kika ce Salamatu"
"eh Inna na ganshi da idanuna ya dauki kudinmu wandanda kikace Adda Agla ta ajiye,muna hada ido ya ari na kare"
"kud'i fa ki ka ce Salamatu?"
"eh wallashi Inna na ganshi idanuwana muna hada ido ya sheka,Inna yi sauri mu duba shi kar ya tsere"
Salmat ta fadi haka tana arcewa ganin kallon da Aleeya ke jifanta dashi ya yin da Inna Saude Iya gaskiyarta ta yarda da batun autar ta.
Bin bayanta Inna tayi amma sai tace,
"inna ki cewa Adda ta fito itama mu duba tare tun bai fita ba"
tafada cikin tsauri da muryar tsoro,aiko inna ta koma cikin dakin da hanzarinta harda bugewa ta yi da kanta.
Salmat kuwa ganin Inna Ta shiga dakin su sai taci taya sai dakin Inna ya yin ta kwaso kud'i ta watsa wasu a kasa, irin barawo ya shigo dauka abu yaga za'a kama shi ya yarda ya yi ta kansa.
A saba'in ta fito dakin Inna Sauden ya yin da ta shiga ya da duk kyallen da taci karo dashi ga yagiyar shanya.
*******
Sannu nake wa inna amma fada ta ke min wai,
"na taho na zauna ko ajikina kamar ba barawo naji ance ba kenan ko bindiga gareshi in ya harbesu ba ruwana ina d'aka zaune ban ma san anyi ba"
ko kala bance mata ba face hakurin da na ke bata, domin nasan duk wannan shirin na Salmat ne,tunda ta fara maganar kud'i nasan karyace kuma na lua da rantsuwar karyar da tayi dazu wai wallashi "hmm" sai naci kaniyar yarinyar nan take hankali.
Kaf gidan mu zagayeshi ba mu ga kowa ba ya yin da duk inda muka bi sai Salmat ta yarda duk abunda ta gani.
Hankalin inna fa duk ya tashi da kyar muke lallashinta har ta hakura da bid'ar barawon ya yin sai debewa barawo albarka take Salmat na kama mata.
_Manage please inshallah ranar monday zanyi mai yawa sai kun gaji da karatu_ 😊
Zeesardaunerh ce
( ~Y'ar karamar su babbar~ ~su~👧🥰🤩)
# _comment_
# _like_
# _share_
comment and vote d'inku shike karamin kafin guiwar typing💋
YOU ARE READING
WASU MATAN✔
Storie breviبسم الله الرحمن الرحيم WASU MATAN Littafi ne da ya kunshi halayen matan mu na yanxu ko nace matan zamani,halaye masu kyau da ma akasin su. Wannan littafi ya kunshi Kishi,kiyayya,tausayi,dama sauran su. INA ROKON UB...
