Page 69&70

121 17 5
                                        

👩‍👩‍👧‍👧 WASU MATAN 👩‍👩‍👧‍👧
@2022

~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤

Story and Writting
by
Zainab Sardaunerh

🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

⚜️©J.A.W📚🖌️

بسم الله الرحمن الرحيم
Da sunan Allah mai rahama mai jinkai

Ya ALLAH YADDA NAFARA WANNAN LITTAFIN LAFIYA KA YARDA NA KAMMALA SHI CIKIN KOSHIN LAFIYA.

SADAUKARWA

WANNAN LITTAFIN SADAUKARWA NE GA FADILA SANI BAKORI,HAFSAT ZUBAIRU SAMBO(Autar mama)AMINA MUHAMMAD BASO, MUMMYN SHUKURA,ASIYA MUHAMMAD,MAMAN AMATULLAH,MAMAN NUSAIBA,RAHMA KOISE,SISTER MIE AND HABIBTY NASMAH LOVE U ALL GUYS♥️♥️♥️

GODIYA

GODIYA MARA MISALI GA PHARTY BB,UMMU MAHIR,MOM ISLAM,UMMU ABDALLAH DA KUMA DAUKACIN MEMBERS NA JARUMAI WRITTER'S ASSOCIATION,MY DEAREST FAN'S SON SO FISSABILILLAH💓💓💓

BOOK 2
  Page 69&70

Yau kimanin sati biyu da zuwan yah Anwar Abuja,yana iya kokarinsa na ganin cewa Aleeya ta saki jiki dashi a matsayinsa na tilon ɗan uwa na jini da take dashi a Abuja, kuma Alhmdllh ya fara ganin alamun nasara,yanzu haka an kammala duk wani abu da za'ayi game da school ɗinta kuma shi ke droping ɗinsu wani lokaci.

KABEER

Sai da ya yi kwana uku a kwance a gadon asibiti kafin a sallameshi batare da raunin sa sun gama warkewa ba,ba abunda yake buri yake fata face ganin fuskar Aleeya,gabadaya kwana ukun yayi su ne ba cikin kwanciyar hankali ba wannan shine dalilin da yasa likitoci suka sallameshi saboda ya takura akan hakan.

Gabaɗaya an kasa controll ɗinsa a gida,ya koma tamkar zararre,tun ranar da aka sallameshi daga asibiti duk safiyar Allah sai yaje unguwarsu Aleeya ya tsaya a kofar gida yana kiran sunanta sai kace mai tabin kwakwalwa kuma ya kasa samun damar magana da Baffa domin Baffa ko fuskar baya bukatar gani,ba wai yana rike dashi game da abun da ya faru bane amma zamansa silar tarwatsewar farinciki da kwanciyar hankalin gidansa da ƴarsa bazai goge ba a zuciyarsa,ko ta ina aka je aka dawo shine za'a samu a matsayin sila na komi da ya faru a watannin baya har a yanzun ma domin shine silar rabuwarsa da Aleeya wanda hakan yake cutar dashi a kowace rana,ya nisan ta Aleeya da garin ne domin ceton rayuwarta amma shi yasan cewa hakan na matukar cutar dashi,Aleeya itace farincikinsa,walwalarsa,ganinta shine kwanciyar hankalinsa ya na samun nutsuwa ne a duk lokacin da yaji muryarta,amma yanzun duk waɗannan abubuwan sunyi masa ƙaura sai dai kawai yaji muryarta a waya duk a sanadin KABEER ! yasan cewa hakan shine Kaddarar Aleeya kuma bazai iya sauya hakan ba.

Inna Saude kuwa babu halin tayi magana da Kabeer domin tana cikin gida shi kuma yana waje,tana matukar bukatar ganawarta dashi domin tasan aikin da ta taro babba ne ba ƙarami ba,cire Aleeya a zuciyarsa wannan abu ne mai matukar wahalar gaske,taya ma zai ƙarbi Asma'u a matsayin matarsa ? gabadaya tama kasa yin tunani,kullin nan da Baffa ya sakata harda kwakwalwarta ya kulle ji take tamkar a kurkutu take,so take ta fita a gidan ta shaki iskar Allah ko kwakwalwarta zata dawo daga yajin aiki da taje.

Haka zai je ya yi ta ihunsa,ya koma abun kallo ga yara har ma da manya,wasu suji tausayinsa wasu kuma suce hakkinta na ke bibiyarshi na ɓata mata suna a sanadin fasa aurenta da yayi,idan ya kira sunanta ya gaji sai ya zauna yayi ta bawa yara labarin irin son da yake mata abun gwanin tautsayi,ba ci ba sha har yini ya ƙare sai tsakar dare sannan ya dawo gida kamar ɗan maye,su Ummu sun saka masa ido ba yadda zasu yi duk yadda aka tsare shi a gida sai ya fita abu sai kace jaraba ko an kulle gida sai ya haura ta gatan ga ya fita, ba abunda take idan tayi sallah face yi masa addu'a Allah ya yaye masa soyayyar Aleeya acikin zuciyarsa,kullum sai hawaye ya zuba a idanuwan su batul ganin irin halin da yayansu yake ciki ya yin da inna dije abun yayi mata sugar ba kaɗan ba, kallon taɓabbe mara hankali take yiwa KABEER domin kuwa a kallo daya idan ka kallesa zaka ɗauka mahaukacin ne.

WASU MATAN✔Stories to obsess over. Discover now