👩👩👧👧WASU MATAN 👩👩👧👧
@2021
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
Story and Writting
by
Zainab Sardaunerh
🔔📚
JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
⚜️©J.A.W📚🖌️
DIYAH
{ Short story }
Labari ne mai cike da ban tautsayi tare da soyayya mai zafi
Wannan littafi na kuďi akan farashi Naira #300 kachal.zaku biya kudin ta wannan account number 2136300504 Sanusi A nura U B A,sai kiyi screen Short ki turo ta wannan WhatsApp number 09066484295 ko kuma 08104093636.Za ku iya turo katin MTN na dari uku ta wannan number 09066484295 domin karin bayani sai ku tuntubeni ta wannan number 09066484295
©️♤♡ Zeesardaunerh
Thanks for the prayers Fan's Allah ya saka muku da mafificin Alkhairinsa Thanks alot
Page77~~78
"hmmm Salamatu Allah ya shirye ki maimakon kiyi hankali naga birkicewa kawai kike"
"Allah bawasa ba inna na samo wa Adda miji wanda ke sonta kamar ransa"
"wai dagaske kike?"
"Allah kuwa innata"
"wanene shi"
" kar ki samu damuwa yace zai zo ya gaisheki ai,sunansa Muhammad Kabeer kyakkyawane kamar Adda,
amma Addana tafishi kyau"
"Allah ya kawo shi lafiya,hhhh dama nasan ba fadar gaskiya zaki yi ba domin a duniya bantaba jin kince ga wanda yafi addar ki kyau ba"
"Allah ba hakan bane inna,ko ke kanki kinsan Adda Agla kyakkyawa ce ajin karshe,ko ya mamien Adda ta kasance?nasan tanada kyau sosai amma da wuya tafi Adda ko inna?"
Shiru inna tayi tana tuna fuskar Halimatu,yanayinta da kuma sanyinta,tabbas Halimatu kyakkyawa ce itama domin a hasashenta kamar tafi Aleeya kyau sai dai Agla ta nuna mata farin fata sosai,wani kishine ya taso mata da tuna irin son da Baffa ke yiwa Sadiya yanzu nan take fuskarta ta chanza.
"Lafiya inna? naji kinyi shiru baki bani amsata ba"
"Lafiya lau,tashi ki chire wadannan tufafin na makaranta ga abincinku chan madafi"
Da "to" Salmat ta amsa tana tunanin ko miye ya batawa inna rai kuma?amma ba mai bata amsa,mikewa tayi ta shiga dakinsu ta chanza tufafi tare da yin alwala tayi sallar azhar,taso su ci abinci amma ganin Aleeya bacci ya seceta a wurin da tayi sallah yasata itama kwantawa domin batason ta tasheta.
Sai karfe hudu suka farka,bayan sunyi sallar la'asar Agla tayi mitar miyasa Salmat bata tasheta ba,gashi hudu tayi tasan kuma karfe shida islamiyya zasu na gashi ko girkin dare bata aza ba"
"lokaci fa ya riga ya wuce Adda,kwana ne mun riga mun sha shi kinga sanadin baccin da kikayi nima na samu na runtsa,kuma dama rayuwa saida hutu "
YOU ARE READING
WASU MATAN✔
Short Storyبسم الله الرحمن الرحيم WASU MATAN Littafi ne da ya kunshi halayen matan mu na yanxu ko nace matan zamani,halaye masu kyau da ma akasin su. Wannan littafi ya kunshi Kishi,kiyayya,tausayi,dama sauran su. INA ROKON UB...
