Page 63&64

144 23 5
                                        

👩‍👩‍👧‍👧 WASU MATAN 👩‍👩‍👧‍👧
@2022

~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤

Story and Writting
by
Zainab Sardaunerh

🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

⚜️©J.A.W📚🖌️

بسم الله الرحمن الرحيم
Da sunan Allah mai rahama mai jinkai

Ya ALLAH YADDA NAFARA WANNAN LITTAFIN LAFIYA KA YARDA NA KAMMALA SHI CIKIN KOSHIN LAFIYA.

SADAUKARWA

WANNAN LITTAFIN SADAUKARWA NE GA FADILA SANI BAKORI,HAFSAT ZUBAIRU SAMBO(Autar mama)AMINA MUHAMMAD BASO, MUMMYN SHUKURA,ASIYA MUHAMMAD,MAMAN AMATULLAH,MAMAN NUSAIBA,RAHMA KOISE,SISTER MIE AND HABIBTY NASMAH LOVE U ALL GUYS♥️♥️♥️

GODIYA

GODIYA MARA MISALI GA PHARTY BB,UMMU MAHIR,MOM ISLAM,UMMU ABDALLAH DA KUMA DAUKACIN MEMBERS NA JARUMAI WRITTER'S ASSOCIATION,MY DEAREST FAN'S SON SO FISSABILILLAH💓💓💓

BOOK 2
  Page 63&64

BAYAN WATA DAYA

Rayuwa Aleeya ke yi cikin walwala da farinciki,tana iya kokarinta na ganin cewa ta boye damuwarta bata bayyanar da ita,burin kowa a gidan ya ganta cikin farinciki,Abba,mum,hanna da kuma Hisham,ta sake da ahalin fiye da tunanin mai karatu,matsalarta ɗaya zaman banzan da take wanda bata saba dashi a gidansu ba,ba wani aiki da take bayan taya mum girki,daga karatun al-qur'ani sai bacci, ta kasa sabawa da wannan sabuwar rayuwar .

A fannin sutura ba abunda ta nema ta rasa,kuɗi masu yawa Abba Muktar ya bawa Hanna suka je da ita suka yi siyayya.

Babbar yarinyar gidan Hanan ko kaɗan Allah bai haɗa jinin su da Aleeya ba,a fili take bayyanar da ƙiyayyar da take mata wadda batasan dalilinta ba.

A kowace rana sai tayi waya da Baffanta da Salamatu,hakama mama Kareema da mama Yelwa basu ɗaukar kwana biyu basu yi waya ba.

  Yanzun ma zaune take a cikin ɗakin nasu tana game da waya,gidan so silent Hanna da Hisham suna makaranta,Abba da Hanan suna office,mum kuwa ta je gidan kawarta, ita kaɗaice a gidan sai masu aiki.

Zaman ɗakin ne ya isheta ta fito garden ɗin gidan ta zauna,duk yadda take son hana kanta yawan tunani amma hakan ya faskara domin babban abunda ke saka mutum a damuwa shine kaɗaici,ta yi nisa a tunani batasan lokacin da Abba ya zo gurin ba,ko kaɗan bata ji horn ɗin motarsa ba sai muryarsa da taji a kusa da ita yana kiran sunanta "daughter !"

Firgigit ta dawo daga duniyar tinanin da afka "Abba sannu da dawowa"

"yawwa,me ke damunki ne daughter?tun ɗazu nake a gurin nan baki san  ma nazo ba "

"bakomi Abba"

"kin tabbata ?"

"eh"

"okay,dama wasu files ne dana manta da su na dawo ɗauka,da zan fita na hangoki a nan,ina mum ɗinku?"

"ta fita"

"ok, kema idan nadawo zamu tattauna ya kamata ace kin fara zuwa school ki daina wannan zaman"

"tou Abba"

Ta ji daɗin maganar Abba sosai,Allah shine shaida tana matukar son ta cigaba da karatu zancen aurenta ne ya tarwatsa komi.

WASU MATAN✔Stories to obsess over. Discover now