👩👩👧👧 WASU MATAN 👩👩👧👧
@2022
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
Story and Writting
by
Zainab Sardaunerh
🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
⚜️©J.A.W📚🖌️
بسم الله الرحمن الرحيم
Da sunan Allah mai rahama mai jinkai
Ya ALLAH YADDA NAFARA WANNAN LITTAFIN LAFIYA KA YARDA NA KAMMALA SHI CIKIN KOSHIN LAFIYA.
SADAUKARWA
WANNAN LITTAFIN SADAUKARWA NE GA FADILA SANI BAKORI,HAFSAT ZUBAIRU SAMBO(Autar mama)AMINA MUHAMMAD BASO, MUMMYN SHUKURA,ASIYA MUHAMMAD,MAMAN AMATULLAH,MAMAN NUSAIBA,RAHMA KOISE,SISTER MIE AND HABIBTY NASMAH LOVE U ALL GUYS♥️♥️♥️
GODIYA
GODIYA MARA MISALI GA PHARTY BB,UMMU MAHIR,MOM ISLAM,UMMU ABDALLAH DA KUMA DAUKACIN MEMBERS NA JARUMAI WRITTER'S ASSOCIATION,MY DEAREST FAN'S SON SO FISSABILILLAH💓💓💓
BOOK 2
Page 47&48
“ohon mata,wannan bai shafe ni ba ko ma ina zata je”
“kuma fa,tabar garin ta tsira da rayuwarta da’alama tana da sauran kwana a gaba, amma kuma ke ya akai ki ka sani”
“Umma ke nan, kar ki manta fa ni yárki ce kuma renon ki ce”
“hakane shalele,congratulations to us”
“Allah Umma ji nake tamkar an mun kyautar Aljanna,yanzu Kabeer ya zama nawa ni kadái, ya zama mallakina kamar yadda yake a baya, dama itace ta shiga gonar da bata kama ce ta ba don kawai ta na takáma da tsarin Ubangiji amma yanzu ba wata y’ar iskar da zata kára samun irin wannan damar domin Kabeer nawa ne ni kadái duk wacce ta yi wannan gangancin kuwa…hmm bazan tsaya jiran aikin boka ko malam ba zan nakàsar da rayuwar ta”
“kafin wata mai tsautsayin tayi gangancin yin hakan zan saka a yi mummunan aiki a kansa wanda ba macen da za ta burge shi har ya ji yana son ta a doron duniya”
“sai Ummana, ina matukar sonki sosai”
“nima hakan shalele,kije ki yi shirin celebrating domin yau ranar farin ciki ce a garemu”
“hakane Umma, after celebrating sai mutattauna a warware asiran da aka yi masa domin ina matukar bukace da mijina kuma kin san ina son sa fiye da tsammaninki”
“naji za’a warware dama kuma lokacin warwararsa ya yi amma idan naji kina furta cewa kina son wancan mayaudarin zafi nake ji a zuciyata da fa yanzu bamu dage ba shikenan ya yi miki kishiya ya gama da duk wani tinkaho nawa,ina mai shawartar ki da ki rage son sa a zuciyar ki domin hakan zai iya zama barazana ga rayuwarki wani lokacin, duk yadda ki ke ganin namiji ki barshi a yadda yake, matukar son da ki ke masa ya rinjaya a zuciyar ki baza ki iya tabùka komi ba face kunsar bakin ciki da takaici"
"amma ai Umma soyayyar da nakewa Kabeer bata saka na kasa yi masa abunda naga dama ba ko na mallake shi ba, matan da son mazansu ke saka su kunsar bakinciki su ne wadánda baza su iya tabùka komi ba domin kwatar wa kansu ýanci wai su tsoron Allah! Allah ne zai yaye musu kaddarar su ce hakan,ni kuma nayi hannun riga da su don haka ba wani connection tsakanin mu,ki saka a ranki har abada bazan kunshi bakinciki akan soyayyar Kabeer ba kamar yar da har abada bazan rabu dashi ba domin shi ďin mallakina ne ni kadài"
YOU ARE READING
WASU MATAN✔
Short Storyبسم الله الرحمن الرحيم WASU MATAN Littafi ne da ya kunshi halayen matan mu na yanxu ko nace matan zamani,halaye masu kyau da ma akasin su. Wannan littafi ya kunshi Kishi,kiyayya,tausayi,dama sauran su. INA ROKON UB...
