👩👩👧👧 WASU MATAN 👩👩👧👧
@2022~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
Story and Writting
by
Zainab Sardaunerh🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo⚜️©J.A.W📚🖌️
بسم الله الرحمن الرحيم
Da sunan Allah mai rahama mai jinkaiYa ALLAH YADDA NAFARA WANNAN LITTAFIN LAFIYA KA YARDA NA KAMMALA SHI CIKIN KOSHIN LAFIYA.
SADAUKARWA
WANNAN LITTAFIN SADAUKARWA NE GA FADILA SANI BAKORI,HAFSAT ZUBAIRU SAMBO(Autar mama)AMINA MUHAMMAD BASO, MUMMYN SHUKURA,ASIYA MUHAMMAD,MAMAN AMATULLAH,MAMAN NUSAIBA,RAHMA KOISE,SISTER MIE AND HABIBTY NASMAH LOVE U ALL GUYS♥️♥️♥️
GODIYA
GODIYA MARA MISALI GA PHARTY BB,UMMU MAHIR,MOM ISLAM,UMMU ABDALLAH DA KUMA DAUKACIN MEMBERS NA JARUMAI WRITTER'S ASSOCIATION,MY DEAREST FAN'S SON SO FISSABILILLAH💓💓💓
BOOK 2
Page 11&12Kasan ance manyan hajiyoyin sun fi son irinsu kyawawa, amma fa ban shaida kar a tasheni kiyama shaidu"
"Kai jama'a jita jita tayi yawa yaseen,wannan abun duka karyane"
"Idan har karyane Auwalu to miye gaskiyar?"
"yaudararta da kudi yayi kasan dai SAUDE Kishiyar gyatumarta yadda take akan kudi shine ya bude musu bakin Aljihu sai daya karbe Budurcinta shine fa yace ya fasa auren "
"aiko idan hakane sai munnuna masa ba'a taba yammatan Unguwar mu a kwashe lafiya sai mun bi mata hakkinta"
sauran suka ce "awo Walla"."Wani dan air daga cinkinsu ya kwaso ashar sannan yace..
" shine dai dai da makwadaita wallahi, shi miye laifinsa wa yace ta bashi yaci? na ma so ganin yadda abun ya wakana wallahi nasan zai bada show"
ya karisa yana zukar wiwi dinsa." Gaskiya hakan baikamata ba,ka dinga sanin me kake fada fa Baba aha,da kanwarka ce zakace hakkan"
"Idan banda abunka baba wake raba mata da son kudi?kamar yadda mu maza mu ke baza mu iya rayuwa ba idan ba Mace, hakama mafi yawa daga cikin WASU MATAN baza su iya rayuwa ba kudi ba;ku mata ne abokan more rayuwarku, su kuma kud'ade ne, miye na kwadayi a ciki? ni banga laifinta ba sai dai shi da yayi asara na rabuwa da wannan santaleliyar kayan alatun bayan ya lashi Zumarta,kai wallahi irinsu matan manya ne,ni wallahi idan ta yarda ta aureni a hakan da take zan riritata kamar kwai zan gwada mata Love sai ta mance da first night dinta da wanchan gayen"sowa aka saka agun.
"Saurayin dazu yace ku atunanin ku SAUDE zata kyaleshi hakan ne bayan yaci yarta ya tafi hakan ?lalllaima to bara kaji tun ranar da yace ya fasa auren ta bankawa dan shegiya Asiri yanzun hakan batun da nake ma yana Chan kwanche a Asibiti likitoci sun rasa gane kansa""Wai dagaske kake Awwalu?"
" wallahi kuwa kasan LAURE da SAUDE kwan fara guda suka rabo to kasan Yarta Hindatu cika tace ina dan rage zafi da ita wani lokacin itace ta bani wannan labarin"
"a kace daga majiya mai karfi kasamu wannan labarin"
"Kana wasa"
Nan suka cigaba da firarsu.ALEEYA
YOU ARE READING
WASU MATAN✔
Cerita Pendekبسم الله الرحمن الرحيم WASU MATAN Littafi ne da ya kunshi halayen matan mu na yanxu ko nace matan zamani,halaye masu kyau da ma akasin su. Wannan littafi ya kunshi Kishi,kiyayya,tausayi,dama sauran su. INA ROKON UB...