Page 17&18

242 33 0
                                        

👩‍👩‍👧‍👧 *WASU MATAN*  👩‍👩‍👧‍👧
          @2021

~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤

*Story and Writting*
           by
*Zainab sardaunerh*

   بسم الله الرحمن الرحيم
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai 📚

         _________________      
       ______
🅙︎𝗮𝗿𝘂𝗺𝗮𝗶 🅦︎𝗿𝗶𝘁𝗲𝗿𝘀 🅐︎𝘀𝘀𝗼𝗰𝗶𝗮𝘁𝗲𝗱📚🖊
https://www.facebook.com/101679598253281/posts/101680068253234/?app=fbl
_Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa illmantarwa, nishadantar tare da fadakarwa da jama'a bisa harshen hausa_

                 🏔🅙︎🅦︎🅐🏔
*Follow this link to join my* *whatsApp group*
https://chat.whatsapp.com/LXIF4UAUqeGCWONjQCrG4Y

*Follow this link to join my* *WhatsApp group* : https://chat.whatsapp.com/J7fqJ9AqzNTGfSryVEm4dZ

*Join me on Telegram*
https://t.me/joinchat/yZ0tHN29JA4wMzZk

*Join me on Whattpad*
https://www.wattpad.com/

*Page* 17~~18

Dariya Amina Da Bilkisu keyi don sallon yadda Salmat Ke basu labarin ma abin dariya ne sannan kuma suna jinjina  masifar inna Saude Ga shi Allah ya bata d'iya mai tsokana.

Abangaren Aliyu kuwa;
   Kiran sallar farko ya tadashi daga baccin da yake bakinsa d'auke da addu'ar tashi daga bacci ,bathroom ya nufa ya watsa ruwa tare yin alwala ya fito,jallabiya maroon colour yasaka tare da fesa turare ya nufi masallaci.

       Da sunka idar da sallah ne ya tsaya ya gaisa da masu aikin gidan kamar yadda ya saba sannan ya nufi cikin gidan.Shirin zuwa hospital ya fara yi becouse ya na da patient din da zai duba sannan akwai abubuwan da yake sonyi a chan kafin ya tafi company.
         Bayan ya kammala shirinsa ya sauko kasa part din Suhailat ya nufa amma har yanxu bata dawo ba,cikin ransa yake cewa "it means ko ina taje a chan ta kwana" tabe baki yayi tare da daga shoulder dinsa alamun i don't care ya fice daga part din baki daya.

Kichen ya shiga ya hada tea ya dawo palon ya zauna yana sha tare da amsa calling da ya shigo wayarsa,ya jima yana waya kafin yatashi ya fita.

       Motarsa ya shiga yadan na  order,da gudu Ila Mai gadi yazo ya bude masa gate din yana cewa "Alhaji Allah yatsare ya kai ka lafiya"
"Ameen"yace yana fita daga gidan.
      U.D.U.TH ya nufa,da isar sa direct offices d'in sa ya nufa yana amsa gaisuwar da nurses and doctors ke masa.
        Bai jima da zama ba yana duba wasu files na maras lafiya akayi noking "yes,come in"yace yana cigabah da abunda yake .
  Turo kofar Dr.Abdallah yayi yana cewa "Dr.haidar harka isone?" "eh wlh,nama jima amman ba sosai ba, dama koda mukayi waya dakai zan fito ne daga gida" "ok" Dr.Abdallah yace yana mika masa hannu sukayi musabaha,ya zauna bisa kujerar dake cikin office din yana cewa  "saura 30mint mushiga theater " tsadadden agogon dake hannunsa ya duba yana cewa "ashe ma lokaci yayi kusa sosai","eh wlh yanzu kasan lokaci ba yada wuyar tafiya","hakanne kuma"nan suka cigaba da tattaunawa kafin lokacin ya cika.
   Suna cikin tattaunawar ne akayi noking,"yes"wata nurse ce ta shigo,d'an rusunawa ta gaidasu kafin tace "sir dama lokacin theater yayi ne shine Dr.Aysha tace nazo na fada muku"
"okey, we are coming" Dr.Abdallah yace da ita , juyawa tayi ta fita.
       shirin shiga theater room sukayi sannan suka fita.

A bangaren Kabir Kuwa,da bakin cikin abunda maryama ta masa ya kwana shiyasa daya tashi da safe bai nemeta ba kamar yadda ya sabayi ko wanne lokaci,shirinsa ya hauyi ya fita.
       Gidansu ya fara biyawa domin ya gaida iyayen nasa,a kofar gida ya hadu da Allhj sa'id mahaifinsa suka gaisa sannan ya shiga cikin gidan, sashen umma ya wuce,koda ya shiga cikin palon nata ba kowa a ciki ,kuryar dakinta ya wuce domin yasan da wuya ta wuce chan,zaune ya tadda ita bisa darduma tana lazimi ta gama sallar walha;durkusawa yayi yana cewa "Umma ina kwana antashiya lfy"
"lfy lau Muhammad Ya iyalin naka"
  cikin boye abunda ke damunsa sanadin maganar maryama da tayi yace "tana lfy "
"mashaallah haka ake so.Allah yakara tsareka"
"Ameen Umma"
"Kana cigaba da addu'a ko?"
"eh,sosaima","yayi kyau ka kara dagewa ba'ason mutum ya kasance mai sakaci da ibada da kuma addu'a,koda mutum baya cikin damuwa,bakinciki,tashin hankali tou ana son yakasan ce mai yawan ibada da neman kariyar Allah;basai ana cikin wad'annan abubuwa sannan zakace kayi addu'a ba,a'a ita addu'a makamin muminice.Duk wanda ke jifar ka da sharri ko sihiri muddun ka tsare addu'a sannan ka tsalkake zuciyarka ya kasance ba ka bibiyarsa da sharri tou  ba'abun da zai sameka sai abunda Allah ya kaddara."

"insha'allah zan cigaba da kiyayewa Umma"
     "yawwa hakan nake san ji,Allah ya dafa ma"
    "Ameen"
shiru yayi nadan wani lokaci kafin yace "wai ina su batul ne yau,naji gidan shiru?"

"kamanta cewa yau ana zuwa makaranta ne"

"Ohh na tina"ummm..
"da wani abun ne?"
"cewa nayi za'a dan samu wani abu",
   Murmushi tayi irin nasu na manya tana cewa...........................✍️✍️✍️

      *Zeesardauner ce*

          ( ~Y'ar karamar su babbar~ ~su~👧🥰🤩)

# _comment_
# _like_
# _share_

*comment and vote dinku shike* *karamin karfin guiwar typing* 💋

WASU MATAN✔Stories to obsess over. Discover now