👩👩👧👧 *WASU MATAN* 👩👩👧👧
@2021
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
*Story and Writting*
by
*Zainab Sardaunerh*
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
*⚜️©J.A.W📚🖌️*
Page 63~~64
"Mine ne ya sameki mai sunan Dadda.."
tafada a lokacin da muka zauna Saman kujerun dakinta.
"ba komi bane mama,mashin ne kawai ya dan bugeni da kafa amma ba wani ciwo naji ba"
"haba mamana buguwar machine zaki ce wa kawai,baki san hakan yana iya janyo wani matsala ba,kalli goshinki fa ya fashe wai ya ma haka ta kasance?saman titi ki ka haw ko kuma matukin mashine din ne bayada hankali...
"ko daya mama abunda Allah ya kaddara ne shiyasa ya afku amma kuskure ne kuma ma ya bani hakuri"
"wa?
"mai mashine din"
Labari na bata daga A har Z saidai ban fada mata cewa Salmat ta tsaya sa'insa da shi ba domin bazatayi mata da wasa ba.
"Assalamu Alaikum.....
taji ba'a amsa ba koma an amsa ita dai bataji ba,sake mai-maita sallamar tayi amma nan ma shiru ko oyoyo bataga an fito anyi mata ba.Cikin ranta take cewa,
" _dama Nasan a raina......_
_yanzu shikenan Adda Agla ta fadi abunda ya faru,yanzu mima zance wa mama ni salmat_
Cikin Parlon ta kusa kai tare da sabuwar sallama,zaune ta tadda su mama Kareema na yiwa Adda Agla dressing na jimuwarta,mazewa Salmat tayi tare da bata rai tana cewa,
" _sai yau na kara tabbatar da wani abu amma bakomi rayuwa ce, idan baku sona bazan rasa masu sona ba sai in koma gidanmu,yaseen kuma baza a kara gani na ba_ "
sai da ta bawa su mama dariya,da gudu Ramlat ta fada jikinta ta rungume ta cikin dariya tana fadin,
"yi hakuri kawas muna sonki, wa ya isa yace baya son Salamatun inna saude"
"ni dai kyaleni ba ruwana dake wlh,nasan yah Anwar baya nan shiyasa da tun farkon sallamata zai zo yanamin oyoyo"
Tafada cikin son ba Ramlat haushi aiko tayi nasara domin sakin baki Ramlat tayi tana kallonta kamin tayi murmushi tace,
"Ayya gashi kuma kinyi rashin sa'a saurayin naki baya ma garin sai ki koma gida in ya dawo kema sai kya dawo"
Pillon kujerar Salmat ta dauka ta makawa Ramlat da fuska tana cewa,
"ýar air kawai shi yaya Anwar din ne saurayina dan kin rainashi"
"Ah to naga Kamar wujinsa kika zo shiyasa"
itama ta fada tana makawa Salmat pillon tare da yi mata gwalo tare da cewa,
"na rama"
Da gudu Salmat tabi bayan Ramlat suna kama zagaye dakin sai da suka gaji suka zube saman Kujerun dakin suna haki.
"Sannunki Salmat ina yini kin yini lafiya"
"laaa mama wlh......
mama Kareema ta katse ta da cewa,
"baki ji mina ce ba"
"plss mamanmu ki hakuri"
"Wani abu kikaji nace miki"
"a'a"
"Ok,gaisheki kawai nayi kina lafiya"
"Allah na dauka mun gaisa mama"
"to ki sauke,dafatan ba kaya masu nauyi kika dauka ba "
"sorry gwaggo"
ko kala mama Kareema bata ce mata ba.
Tashi tayi ta dauki hijab din Ramlat dake kusa da ita ta saka sannan tafito sakar gidan ta sake komawa daki da sallama suka amsa ta duka kusa da mama Kareema tana cewa,
"Ina yini mama,ya gida,nasameku lafiya?
Da kallo kawai mutanen dakin suka bita Kafin mama Kareema ta amsa,
"Baffa yace yana gaisheki inna kuma ko cikanki bata ceba"
"ina amsawa"
miya sai dake saman hanya baki iso tare da ýar uwarki ba?
Gaban Salmat ya yanke ya fadi da tuna da bawan Allahn da ta bari waje.
"dama wanda ya kiďe Adda Agla ne yake sallama da mai gidannan"
"tun da na shigo da zu"
"kin kyauta Salmat"
"Wlh mama sam na manta shiyasa"
"ba wani kin manta renin hankali ne kawai mama,wai ace tundazu mutum yana garka tsaye fissabilillahi"
"rufe min baki duk bake bace ki ka batamun lokaci na biye miki ai da ban manta "
Cewar Salmat
"Mumhhh don Allah,wai ni na bata miki lokaci ko Kunyar fada baki ji ba, dani dake wa ya fara makawa wani pillo"
"Hmm ba wani nan in kina karbar laifinki ki karba yafi miki yarinya"
Ramlat ta bude baki tayi magana mama ta katse ta da cewa,
"Je kice masa ya shigo "
"to mama,Allah yasa yana nan idan bai yi zuciya ba ya tafiyatai"
Kallonta Salmat tayi kafin tace,
" hakan ma bazai faru ba ýar black stomach kawai"
"ko dai blue zaki ce bai dameni ba kuma sai nagaya masa"
tafada tana fita daga dakin
"kin ďade baki fada masa ba msstwws"
Kuryar ďaki mama Kareema ta Shiga domin Saka hijab dinta ni kuma na tashi na shiga ďakin Ramlat na kwanta domin bacci nake ji.....🖊🖊🖊
Zeesardaunerh ce
( ~Y'ar karamar su babbar su~👧🥰🤩)
# _comment_
# _like_
# _share_
comment and vote d'inku shike Karamin kafin guiwar typing💋
Hello my fan's I'm back🖤🤍❤️
YOU ARE READING
WASU MATAN✔
Short Storyبسم الله الرحمن الرحيم WASU MATAN Littafi ne da ya kunshi halayen matan mu na yanxu ko nace matan zamani,halaye masu kyau da ma akasin su. Wannan littafi ya kunshi Kishi,kiyayya,tausayi,dama sauran su. INA ROKON UB...
