page 81&82

151 11 0
                                    

👩‍👩‍👧‍👧WASU MATAN 👩‍👩‍👧‍👧
          @2021

~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤

Story and Writting
           by
Zainab Sardaunerh

🔔📚
JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
             
          ⚜️©J.A.W📚🖌️

DIYAH
{ Short story }

Labari  ne mai cike da ban tautsayi tare da  soyayya mai zafi

Wannan littafi na kuďi akan farashi Naira #300 kachal.zaku biya kudin ta wannan account number 2136300504 Sanusi A nura U B A,sai kiyi screen Short ki turo ta wannan WhatsApp number 09066484295 ko kuma 08104093636.Za ku iya turo katin MTN na dari uku ta wannan number 09066484295 domin karin bayani sai ku tuntubeni ta wannan number 09066484295

©️♤♡ Zeesardaunerh

Page 81~~82

Dauke idanunsa daga kan Aleeya ya yi sannan yace "Amm Rahama je ki zauna" cike da mamaki Rahama da kowa da ke ajin ya kallesa  harda Aleeya(Agla) wadda ke jiran sakamakon hukuncin dariyarta.

   Kallon da tayi masa shine abunda ya idar da warware duk wani notin kansa da gangar jikinsa.Ba karamin illa dariyar ta tayi wa zuciyarsa da kwakwalwarsa ba wanda shine dalilin yanke hukuncin da yayi ba tare da yasan ta ya hakan ya faru ba.

Da sauri Rahama ta dawo wurin ta yayin ajin yayi tsit kamar ruwa yaci shi,duba agogon hannunsa yayi yaga saura time kalilan period dinsa ta kare batare da bata lokaci ba ya fita daga ajin.

      Domin kuwa muddin ya tsaya a ajin za'a samu power gaba daya ji yake kwakwalwarsa ta daina aiki ba abinda yake gani face fuskar Agla da dariyarta sai kuma kallon da tayi masa wanda ya riskesa a bazata.

Kamar jira ake ya fita ajin ya hautsine da surutu ko wane group anyi gungu ana tattaunawa kowa na cike da mamakin malam Nura .

******************
A bangaren Maryama kuwa

     Har yanzu babu wani sauyi ta lura yanzu kamar akwai abunda ya dauke hankalinsa kwana biyu yazama busy baya ma biye mata suna fada gashi ita kuma har yanzu bata dauki zabi ko daya ba cikin zabin da mahaifiyar ta tabata,amma zata kawo karshen abun.

*************
DR AYSHERT

Office din Dr Abdullah ta wuce kai tsaye...batare da tayi Sallama ko knocking ba ta murda handle din kofar ta shiga.

    Zaune yake saman kujera ya na duba wasu file yaji an bude gambu,dago kansa yayi ya kalle Dr Ayshert dake shigowa;matashiyar likita mai ji da kudi ga kwalisa amma duk ta rame ta dan fita hayyacinta wanda ba kowa ne zai fuskanci hakan ba sai wanda yama ta kyakkyawan sani.

    Kallon sa tayi yayin da ya dauke kai daga kallonta domin yasan halinta ba mutunci ne da ita ba,cikin isa da gadara take magana kamar ba ta so " Hydar yana ina"

wani kallon bangane ba ya watsamata da yake ko ba komi ya tashi tare da Aleeyu kuma ya koyi wasu daga cikin halayesa yace mata "ban fahimceki ba "

"Wane gari haidar yake"
Cikin kosawa kamar wacce aka yiwa dole take magana yayin da a zuciyar ta ta matsu da jiran amsar da zai bata

Cikin son gasa mata magana yace "oh na dauka kuna waya dashi ai"
Batace masa komi ba amma maganar ta dake zuciyar ta,yaci gaba da cewa...

"ko da yake no problem ba sai na miki dogon zance ba Aleeyu ya wuce India gurin wani course da zaiyi kuma I think zaiyi shekara daya ko biyu"

Cikin zare idanuwa da dukanta da maganar tayi tace .....🖊️🖊️🖊️

*Show me love patronize my book _Diyah❤️_*

*Zeesardaunerh ce*

          ( ~Y'ar karamar su babbar su~👧🥰🤩)

# _comment
# _like_
# _share_

*comment and vote d'inku shike Karamin kafin guiwar typing*💋

WASU MATAN✔Where stories live. Discover now