page 5&6

108 14 4
                                        

👩‍👩‍👧‍👧 WASU MATAN  👩‍👩‍👧‍👧
          @2022

~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤

Story and Writting
           by
Zainab Sardaunerh

🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
             
          ⚜️©J.A.W📚🖌️

بسم الله الرحمن الرحيم
Da sunan Allah mai rahama mai jinkai

Ya ALLAH YADDA NAFARA WANNAN LITTAFIN LAFIYA KA YARDA NA KAMMALA SHI CIKIN KOSHIN LAFIYA.

SADAUKARWA

       WANNAN LITTAFIN SADAUKARWA NE GA FADILA SANI BAKORI,HAFSAT ZUBAIRU SAMBO(Autar mama)AMINA MUHAMMAD BASO, MUMMYN SHUKURA,ASIYA MUHAMMAD,MAMAN AMATULLAH,MAMAN NUSAIBA,RAHMA KOISE,SISTER MIE AND HABIBTY NASMAH LOVE U ALL GUYS♥️♥️♥️

GODIYA

    GODIYA MARA MISALI GA PHARTY BB,UMMU MAHIR,MOM ISLAM,UMMU ABDALLAH DA KUMA DAUKACIN MEMBERS NA JARUMAI WRITTER'S ASSOCIATION,MY DEAREST FAN'S SON SO FISSABILILLAH💓💓💓

BOOK 2
   Page 5&6

Hajiya Hawwa ce tafara magana bayan ta karbi Mic hannun Dj tana yiwa duk wandanda suka halarta godiya sannan ta d'aura da cewa..

"Nasan cewa kan mutane da yawa a wannan gurin a kulle yake yayin da kwanyarsu ke yi musu tunanuka barkatai game da wannan shagalin,to ina son kowa ya bude kunnuwansa ya saurara cikin basira domin wannan shagalin na shiryashi ne ba domin komi ba face yau ne Yar lele ta (Maryama) ke murnar zagayowar ranar haihuwarta sannan kuma a irin wannan ranar ce  tafara haduwa da sahibin ranta "

   Tafi aka saka wasu suka saka kuwa ana taya Maryama murnar zagayowar ranar haihuwa,hajiya hawwa ta cigaba da fadin..

"akalla kowa da ke wannan gurin yasan ni, ko nace yasan wacece Hajiya Hawwa sannan kuma yasan minene matsayin Maryama a guna" taja nimfashi sannan ta cigaba da magana a dan zafafe "Maryama fa y'ata ce ba y'ar riko ba, nice na tsuguna na haifeta sannan kuyi tunanin zan bari a yo mata KISHIYA ?
Wallahi wannan karyane,ba Namijin da ya isa ya yiwa ya'ta Kishiya ba'a samu cikinsa ba balle a haifosa MUDDIN INA RAYE A DORON DUNIYA TO WALLAHI YA'TA MARYAMA TAFI KARFIN KISHIYA"
kururuwa wurin ya kara kaurewa da shi tare da tafi harda sowa.

  Wata cikin kawayen Hajiya Hawwa da takasance tana kishinta tace "Batun auren fa da aka daura yau?"

Wata arniyar dariya Umman Maryarma ta kwashe da ita har saida gurin yayi tsit ana kallonta sannan tace "Wane Auren kike magana Balki?wa aka daurawa aure yau? Oh namanta baki da ko nace dukkanku baku da labarin cewa angon ya fasa auren,ke banda abinki waya isa ya ja da hajiya hawwa.. ko yayan wasu ban bari aka yiwa kishiya ba ballantana tawa y'ar, ni na tsani Kishiya kuma na tsani namijin da ke yiwa matar sa kishiya"
yan zuma dai tafin aka sa yayin wasu ke cewa sai dake hajiyarmu suna sowa.

Zuciyar Hajiya Balkisu tayi bakikirrin,Allah shine shaida har niyar azumi ukku tayi na alwashi idan har wannan auren ya dauru amma kash ko a yanzu Hawwa ce tayi nasara ta hanyar dakile wannan auren,a duniya ba abunda take bukata face ganin Hajiya Hawwa ta girbi ayukan da ta shuka tana son ganin ranar da jiji da kan Hajiya Hawwa zai kare ta wulakanta sannan kuma a yi wa ita ko yarta kishiya taga karshen takama.

Order hajiya Hawwa ta bada sai gashi an fito da katoton cake wanda dama sun tanadesa domin wannan Shagalin.

Chasu aka cigaba da yi mussamman yanzun da kawayenta suka tabbatar da cewa ba'a yi mata kishiya ba.
    Y'an gulma kuwa da guda guda suka ware abunsu, wasun dama shine abunda ya kawo ji, suna nan har isha'i Dj na tashi ba batun aje ayi sallah .

WASU MATAN✔Where stories live. Discover now