👩👩👧👧WASU MATAN 👩👩👧👧
@2021
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
Story and Writting
by
Zainab Sardaunerh
🔔📚
JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
⚜️©J.A.W📚🖌️
DIYAH
{ Short story }
Labari ne mai cike da ban tautsayi tare da soyayya mai zafi
Wannan littafi na kuďi akan farashi Naira #300 kachal.zaku biya kudin ta wannan account number 2136300504 Sanusi A nura U B A,sai kiyi screen Short ki turo ta wannan WhatsApp number 09066484295 ko kuma 08104093636.Za ku iya turo katin MTN na dari uku ta wannan number 09066484295 domin karin bayani sai ku tuntubeni ta wannan number 09066484295
©️♤♡ Zeesardaunerh
Page 87~~88
2hours 50m+ jirginta yayi landing garin Kano,Bayan wani lokaci jirgi ya dauke su sai NEW DELHI.
Sun kwashe kimanin awa goma shadaya jirgin su na yawo A sararin samaniya kafin ya sauka a INDIRA GANDHI INTERNATIONAL AIRPORT.
Wata kawar ta yar kasar India mai suna Shyla yar addinin Hindu ce ta zo ta dauke ta, gaisawa suka yi da yaren Hindu,Direct Wani kawataccen hotel suka wuce mai suna RED FOX HOTEL;wani kawataccen room suka shiga bayan sun karbi card na bude d'akin Already Shyla tayi mata booking,komi da ke cikin room din tsaf_tsaf yake ba wani tarkace.
Bathroom tawuce kai tsaye domin ta watsa ruwa yayin da Shyla ta ke saka mata kayan ta a closate ,bayan wani lokaci ta fito daga bathroom lotion ta shafa tare da parfum dinta mai sanyayyen kamshi.
Shigar kananan kaya tayi wadanda suka kama jikinta yayin da tad'an tsakuri abincin da aka kawo daga hotel din,da yake ta saba da cin abincin kasar bai wani bata problem ba.
Cikin yaren India suke magana yayin Dr Ayshert ke cewa shyla su wuce University din da take karatu a chan ta matsu da taga Hasken Ruhinta,nan shyla ke sanar da ita cewa da wuya su riskeshi a chan yanzu badan ta so ba ta hakura.
************
Bada b'ata lokaci ba Allhaji Sa'id ya riske Abban Ramlat game da zancen da Muhammad Kabeer yazo dashi ya na neman ya yi masa rakiya a gun Mahaifin Aliya.
Abban Ramlat bai yi rejecting din bukatar Mahaifin Kabeer ba suka saka date din da zasuje.
Su ukku su ka je da Abban Kabeer da wani abokinsa sai Abban Ramlat sun tattauna sosai akan maganar auren Aleeya da Kabeer ke so amma sai dai Bappa bai amince ba ya gaya musu cewa shi bazai yiwa y'ar sa auren dole ba amma muddin tana son Kabeer d'in shi baya da matsala.
A takaice dai an bawa Kabeer damar zuwa zance gurin Aleeya idan har Allah ya kaddara ya yi mata falillahilhamdu idan kuma akasin hakan ne suyi hakuri.
Haka Mahaifin Kabeer da Amininsa suka koma gida suna yaba karamci da mutuntawar da akayi musu a gidan su Aleeya ya yin da suka bar Abban Ramlat a chan.
Bayan tafiyar su,su Bappa suka cigaba da tattaunawa shida Abban Ramlat inda yake nuna masa cewa bawai ba ya son yiwa Agla aure bane amma yana son ta samu illimi sosai yana son cika burin Ummynta akanta,shi kansa yasani cewa aure shine hutu ga Agla saboda aikin gida da take ya mata yawa yana son ta samu hutu itama ta huta a rayuwarta .
Sannan matsala ta biyun shine Kabeer yana da mata, da so samu nai ne ya kasance mijin Agla itace ta farko a gunsa kuma itace ta Karshe, duk da cewa yasan halin WASU MAZAN basa iya zama da mace daya a rayuwarsu ko da kuwa sun maka alkawarin hakan amma shi yasan cewa duk na mijin da ya aure mamana (Aleeya) bazai samu wurin korafi ba,ko kuwa yaji son sake auren wata mata ba .
Yasan yadda zama da kishiya yake,yasan yadda HALIMATUS_SADIYA ta rayu a gidansa, baya son wahalar da Ummynta tasha itama tasha irinta duk da cewa shi da Ummynta auren had'i ne.
Kwantar masa da hankali Abban Ramlat ya yi tare da bashi baki har hankalinsa ya d'an kwanta sannan ya nuna masa cewa iyayen Kabeer mutane ne masu dattako da illimin addini kuma Kabeer yaro ne mai hankali da natsuwa tabbas yana ji aransa muddin Aleeya ta auresa baza tayi dana sani ba zai riketa da amana,sannan a duniya ba abunda yafi dadi ga yaran zamanin irin ka aura masu wanda suke so in har ya kasance mutumin kirki.
Idan Allah ya kaddara cewa shi mijin tane sai kaga Allah ya dasa soyayya a tsakaninsu kuma karatu ba yada matsala ko da auren zata iya cigaba da karatunta har takai matsayin da kake bukata inshaallah.Ba abunda yafi Alkhairi a yanzu Mallam Yusuf (sorry nayi kuskure sunan mahaifin Aliya shine Malam Yusuf but a page 39 na Abba Mukhtar ya kira sa da suna muhammad )face mu rika saka su a cikin Addu'a Allah ya zab'ar mana abunda yafi zama Alkhairi A rayuwar su duka.
Sai Bayan karfe 5:30 sannan Abban Ramlat ya fito daga cikin dakin Bappa wanda Aliya ta share tayi ma tsaf ta shimfida masu tabarma ta saka masa turare sai kamshi ke tashi a gidan duka ko ina tsaf zaka ganshi.
Bayan Abban Ramlat ya yiwa Inna Saude sallama tare da aje mata dan wani hasafi sannan ya wuce domin yasan halinta tsaf ba wuya take yi mata taci masa mutunci ba domin ba yau farau ba gashi taga baki harda motoci,bakin garka Bappa ya raka Abban Ramlat ya shiga motarsa ya wuce gida.
A cikin gidan kuwa INNA SAUDE ta kasa ta tsare tana jiran dawowar Bappa taji yadda akayi kuma daga ina wadannan Bakin suke daga ganin su kasan mashaallah akwai abun hannu, ta na nan tana jiran Bappa su Salmat suka yi mata sai anjima suka fita, anan waje suka tara da Bappa ya saka musu Albarka suka kama hanyar Islamiyya .🖊️
Zeesardaunerh ce
( Y'ar karamar su babbar su👧🥰🤩)
# comment
# like
# share
comment and vote d'inku shike Karamin kafin guiwar typing💋
YOU ARE READING
WASU MATAN✔
Short Storyبسم الله الرحمن الرحيم WASU MATAN Littafi ne da ya kunshi halayen matan mu na yanxu ko nace matan zamani,halaye masu kyau da ma akasin su. Wannan littafi ya kunshi Kishi,kiyayya,tausayi,dama sauran su. INA ROKON UB...
