👩👩👧👧 WASU MATAN 👩👩👧👧
@2022~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
Story and Writting
by
Zainab Sardaunerh🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
⚜️©J.A.W📚🖌️بسم الله الرحمن الرحيم
Da sunan Allah mai rahama mai jinkaiYa ALLAH YADDA NAFARA WANNAN LITTAFIN LAFIYA KA YARDA NA KAMMALA SHI CIKIN KOSHIN LAFIYA.
SADAUKARWA
WANNAN LITTAFIN SADAUKARWA NE GA FADILA SANI BAKORI,HAFSAT ZUBAIRU SAMBO(Autar mama)AMINA MUHAMMAD BASO, MUMMYN SHUKURA,ASIYA MUHAMMAD,MAMAN AMATULLAH,MAMAN NUSAIBA,RAHMA KOISE,SISTER MIE AND HABIBTY NASMAH LOVE U ALL GUYS♥️♥️♥️
GODIYA
GODIYA MARA MISALI GA PHARTY BB,UMMU MAHIR,MOM ISLAM,UMMU ABDALLAH DA KUMA DAUKACIN MEMBERS NA JARUMAI WRITTER'S ASSOCIATION,MY DEAREST FAN'S SON SO FISSABILILLAH💓💓💓
BOOK 2
Page 3&4Bakinciki ko Farinciki ya rasa wanne yake ciki a lokacin da ya tabbatar da cewa an fasa auren,tabbas yaudarar zuciyarsa ne zaiyi idan har yace yayi farinciki da wannan al'amarin, ko mai son da yake wa Beauty(Agla)bazai so yar kankanuwar zuciyarta ta karye a kan soyayya ba,bazai so irin hakan ya faru Ramlat ba matsayinsa na yayanta to hakan ne ko bada Soyayya ba Aleeya kanwarsa ce ta jini,bai kasance cikin matune masu mugun son kan su da yawa ba da zai manta duk wannan saboda muradin zuciyarsa.
Farin cikin Aleeya ya fiye masa nasa farin cikin,bai kara tabbatar da yana matukar son ta ba sai a yau amma yanzu da yake da dama kuma yake da sa rai zuciyarsa tafi kuntata da kuma zafi fiye da yadda yake ji alokacin da ya tabbatar wa kansa ya rasata har abada.MARYAMA (UWAR GIDA RAN GIDA)
Wayyo Allah Ina zata saka ranta a wannan duniyar,farincikin da take a ciki yafi karfin kwatance,duk da cewa kuwa tasan hakan zata kasance bare kuma mai gayya mai aiki Hajiya Hawwa ikon Allah jinkansu suke a wannan duniyar ba ranar da ta kai musu wannan ranar,komai da komai da ya faru a wajen daurin auren tass har faduwar ANGO NA AMARYA KABEER sun ganewa idanunsu ta hanyar wani mutummen da suka tura wajen daurin auren domin ya dauko musu vedion abun da zai faru kar asha dasu,har da masu DJ Umman Maryama ta dauko wacce ta tare a gidan tun ana jibi buki itada kawayenta sai kadan daga cikin kawayen Maryamar wai zasuyi dannar kirjin Maryama kafin akawo amaryar(Sabon Salo liman da gadin gidan chacha😯).
Gidan sai kida ke tashi ba kama hannun yaro yayin da sauran kawayen maryama har da wadanda ta hadu da su a WhatsApp da sauran yan kungiyar Hajiya Hawwa sai isowa suke Maryama sai barin kudi take tana yiwa masu rawa liki itama tana tattakawa cikin ado mai daukar hankali dama chan ita ba mummuna bace kuma kyakkyawa ba amma tana da hanci da manyan idanuwa kowa yana mamaki Anya Maryama kanta qalau yake kuwa Anya tana cikin hayyacinta?kishiyafa za a yi mata!Aure ake daurawa mijin ta da wata a yau a kuma wannan lokacin!!amma kuma sai rawa take tana liki kamar itace uwar Amaryar, mai DJ sai wake ta yake duk kuwa shima abun ganinsa yake kamar almara.
Wannan abun bakon Abu ne ga mutane domin basu saba ganin hakan ba,Mutanen Unguwar sai mamaki suke da tu'ajjubi wai akace b'arawo da sallama basu kadai ba har kawayen Maryamar da Mutanen Hajiya Hawwa hakanne a gunsu amma sun kama baki duk cewa hakan ya mugun daure musu kai gashi mutanenta sai zuwa suke kamar gayyatar su akayi.

YOU ARE READING
WASU MATAN✔
Cerita Pendekبسم الله الرحمن الرحيم WASU MATAN Littafi ne da ya kunshi halayen matan mu na yanxu ko nace matan zamani,halaye masu kyau da ma akasin su. Wannan littafi ya kunshi Kishi,kiyayya,tausayi,dama sauran su. INA ROKON UB...