👩👩👧👧 WASU MATAN 👩👩👧👧
@2022
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
Story and Writting
by
Zainab Sardaunerh
🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
⚜️©J.A.W📚🖌️
بسم الله الرحمن الرحيم
Da sunan Allah mai rahama mai jinkai
Ya ALLAH YADDA NAFARA WANNAN LITTAFIN LAFIYA KA YARDA NA KAMMALA SHI CIKIN KOSHIN LAFIYA.
SADAUKARWA
WANNAN LITTAFIN SADAUKARWA NE GA FADILA SANI BAKORI,HAFSAT ZUBAIRU SAMBO(Autar mama)AMINA MUHAMMAD BASO, MUMMYN SHUKURA,ASIYA MUHAMMAD,MAMAN AMATULLAH,MAMAN NUSAIBA,RAHMA KOISE,SISTER MIE AND HABIBTY NASMAH LOVE U ALL GUYS♥️♥️♥️
GODIYA
GODIYA MARA MISALI GA PHARTY BB,UMMU MAHIR,MOM ISLAM,UMMU ABDALLAH DA KUMA DAUKACIN MEMBERS NA JARUMAI WRITTER'S ASSOCIATION,MY DEAREST FAN'S SON SO FISSABILILLAH💓💓💓
BOOK 2
Page 39&40
Kallon sa take a zuciyarta tace"kaine"
waiwayawa tayi domin ta ga wa yake kira haka,ta ga bakowa a kusa da su..
Kenan da ita yake?
Jin sunan da ya kirata da shi da kuma kallon da yake mata fuskarsa dauke da mamaki da kuma alamar tambayoyi,duk da cewar tsayuwar na yi mata wani iri bata saba tsayuwa da maza hakan ba ballantana shi da takejin wani abu idan yana kusa da ita gashi kusancin nasu ya yi over,a hankali cikin sanyayyiyar muryarta tace "ba sunana Amrah ba..kayi hakuri da marin da nayi maka a bisa kuskure,bansan dalili ko hujjarka na son ganin fuskata ba amma kasani wannan abun da kayi kuskure ne, a zamanance ko a addinance bai dace ba ka..."
Bata karisa ba tayi ido hudu da mama Kareema da yake ita ke facing hanyar dakin,chan ta tsinkayi muryarta "mai tsada"
A hankali ta amsa "na'am" tana dauke idanuwanta daga kan mama Kareema ta daurasu akan yelwatacciyar fuskarsa mai cike da kwarjini dake gabanta,idanuwanta ne suka shiga cikin nasa wadanda suke kan kyakkyawar fuskar ta .
Kallon da bai wuce na second biyar ba tayi masa tare da rab'awa ta gefenshi ta wuce cikin takunta na nutsuwa ta nufi gurin mama Kareema.
"gani mama"
Wani kallo mama Kareema ta yi mata kafin tace "Waye wanchan"
waiwayawa nayi idanuwana suka sauka akan bayansa yana nan bai motsa ba sai dai ba'a ganin fuskarsa domin ya bada baya "Bansanshi ba"
"baki sanshi ba kika tsaya magana dashi?"
Shiru nayi
"Ba mara kunyar yaron nan bane?"
Kallon ta nayi domin ban fuskanci wane yaron take nufi ba,kamar ta karanceni naji tace
"KABEER"
Kamar saukar aradu haka naji sunan nasa ya sauka a kaina "Kabeer"
na maimaita sunan a zuciyata,mi zai kawo yayan su Batul gurina?miye alakarmu da har zan tsaya magana dashi wata zuciyar tace mun "to shi wanchan kuna da alaka ne da kika tsaya magana dashi?" nayi saurin kawar da wannan tunanin araina batare da na bawa zuciyata amsa ba.
Kallo na take, mai yuwa ta fuskanci yanayin da na shiga ko kuma a'a,idan ma ta fuskanta bansan ya zata fassara shirun nawa ba
"Ko shine"
YOU ARE READING
WASU MATAN✔
Short Storyبسم الله الرحمن الرحيم WASU MATAN Littafi ne da ya kunshi halayen matan mu na yanxu ko nace matan zamani,halaye masu kyau da ma akasin su. Wannan littafi ya kunshi Kishi,kiyayya,tausayi,dama sauran su. INA ROKON UB...
