Page 39&40

197 28 2
                                        

👩‍👩‍👧‍👧 *WASU MATAN*  👩‍👩‍👧‍👧
          @2021

~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤

*Story and Writting*
           by
*Zainab sardaunerh*

   بسم الله الرحمن الرحيم
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai 📚

         _________________      
       ______
🅙︎𝗮𝗿𝘂𝗺𝗮𝗶 🅦︎𝗿𝗶𝘁𝗲𝗿𝘀 🅐︎𝘀𝘀𝗼𝗰𝗶𝗮𝘁𝗲𝗱📚🖊
https://www.facebook.com/101679598253281/posts/101680068253234/?app=fbl
_Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa illmantarwa, nishadantar tare da fadakarwa da jama'a bisa harshen hausa_

                 🏔🅙︎🅦︎🅐🏔
*Follow this link to join my* *whatsApp group*
https://chat.whatsapp.com/LXIF4UAUqeGCWONjQCrG4Y

*Follow this link to join my* *WhatsApp group* : https://chat.whatsapp.com/J7fqJ9AqzNTGfSryVEm4dZ

*Join me on Telegram*
https://t.me/joinchat/yZ0tHN29JA4wMzZk

*Join me on Whattpad*
https://www.wattpad.com/

*_Don Allah ina mai neman_* *_Alfarma ga duk wanda ya_* *_karanta wannan page din da_ ya taimaka ya ma Abbana Addu'a Allah ya bashi lafiya*🙏🙏 🙏

*Page* 39~~40

    "Mafitar ko nace hanyoyin sune......... *na daya* dole ki sauya ki rika yi masa girki a ko da yaushe sannan duk abunda ki kasan mace na yi wa mijinta ta bangaren ladabi da biyayya ki dinga yi masa,ki kwantar da hankalinki ki rika bin umurninsa,ki kuma daure duk fada ko wani abu da zai miki ta hakan ne zai tabbatar cewa kin sauya.Ta nan ne zaki yi amfani da damarki wurin ganin cewa yaci maganin sannan na wankan ma kin sa masa yayi amfani dashi, kinga kuwa bukata ta biya domin shi zai d'auka kin sauya ne saboda shariyar da yake miki amma ke a gunki ba hakan bane,ki sauya ne na wani lokaci saboda cimma burinki".

"umma......"

Da hanzari tace ,
"dakata shalele!ki bari na ida bayanin mana".

Numfashi ta fesar sannan ta ci gaba da cewa,
"hanya ta *biyu* kuwa!Dole ki yarda na nemo miki y'ar aiki wacce za ta rika yin girki da gyara gida.Da ta gama aikinta zata koma gida ba'anan zata ciga ba da zama ba, kawai zata zo na wani lokaci da ta gama ta koma,in yarinya kikeso ko dattijuwa za'a nemo miki.kinga idan yasan da mai girka abinci wani lokaci zaya tsaya yaci. Shikenan, dama sau ukku a keso yaci,kiyi tunani ki gani.

Tana gama fadar haka ta katse kiran ya yinda ta bar Maryama cikin kogin tunani domin ta rasa madafa(kishi zata aje ta bari akawo mata y'ar aiki ko kiwa zata cire ta ma mijin ta girki).

Haka MARYAMA Ta yini ciki tunani da neman zab'i acikin biyun,lokacin da taga kanta zai yi ciwo sanadiyyar zafin da ya d'auk a sai ta watsar da komi da d'auko wayar ta ta cigaba da karatun littafin ta,bayan ta turawa ummanta text na alala take so tayi ta bada akawo mata.

Yinin yau jin kanta take cikin feeling mara iyaka tun tana d'aurewa saboda alwashin da tayi na baza taje gun kabeer ba sai mallakesa .Tofa abun na yau na neman fin karfin ta,ta rasa ya zatayi,karatun novels d'in ma ya isheta ta ajiye wayar.

Bayan tayi sallar magrib ta shirya kanta cikin doguwar rigar bacci mai kyau ta zauna falo tana jiran dawowarsa domin yau kam baza tayi jurewa ba.ta na nan zaune akayi isha'i taje tayi tana Allah Allah Kabeer Ya dawo amma Kabeer Shiru kamar an aiki bawa garin su gashi abun nata sai tsamari yake.

   Takwass ta wuce Tara ma haka amma ba'alamar Kabeer,iya shaka ta shaka domin tasan baza ya wuce yana gun mahaifansa ba,tsanin kanta ne Kabeer a ko ina yake da anyi sallar isha'i ya dawo gida,idan ko hakanne dole tayi zab'i acikin biyun da ummanta tace.

WASU MATAN✔Stories to obsess over. Discover now