👩👩👧👧WASU MATAN 👩👩👧👧
@2021~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
Story and Writting
by
Zainab Sardaunerh🔔📚
JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
⚜️©J.A.W📚🖌️DIYAH
{ Short story }Labari ne mai cike da ban tautsayi tare da soyayya mai zafi
Wannan littafi na kuďi akan farashi Naira #300 kachal.zaku biya kudin ta wannan account number 2136300504 Sanusi A nura U B A,sai kiyi screen Short ki turo ta wannan WhatsApp number 09066484295 ko kuma 08104093636.Za ku iya turo katin MTN na dari uku ta wannan number 09066484295 domin karin bayani sai ku tuntubeni ta wannan number 09066484295
©️♤♡ Zeesardaunerh
Page 85~~86
Kwana daya kwana biyu amma Aliya bata cewa Salmat komi ba ko maganar bata tadda ba tun Salmat na jiran sammani na fadan da zata sha har ta fidda rai ta sake jikinta ko a islamiyya tun lokacin da su Maryam suka tada maganar suka ga iya gaskiyar tace batasan wani abu game da Kabeer ba suka bar tada maganar,idan har wani abu suke son ji gurin Salmat suke zuwa ta fada musu duk yadda akayi tun farkon haduwar Aliya da K.B.
A gurin Malam Nura kuwa a koda yaushe idan ya shigo class idonsa na kanta har tsarguwa take duk da cewa yana dan basarwa amma saida yan class din suka saka masa ido cikin ma suna shakkarsa fiye da sauran malaman islamiyyar.
Idan taji bata jin dadi a rayuwarta sai ta dauko Al-qur'ani ta ringa karantawa sai taji sanyi a ranta,wani lokaci sai taji kewar Ummynta ta kamata (wato mahaifiyar ta) duk da cewa tun tashin ta bata taba ganin ta ba sai dai a labari ko shi wani lokaci a gun mama Kareema.
Alokacin da take yarinya a tunanin ta tadauka cewa Inna Saude ce mahaifiyar ta sai daga baya ta fuskanci bahakan bane, wata rana bata mantawa alokacin bakinta shekara tara Inna Laure kawar Inna Saude ta aiketa da kud'i wani dan iska ya kwace shine fa tahau fada tana mata cin mutunci har da zagin Ummynta.A wannan rana ne tasan sunan mahaifiyarta,tasha kuka tana tambayar Bappa ina Ummynta take tanason ta ganta Alokacin yake bata hakuri tare da sanar da ita cewa Ummynta bata raye ta rasu kuma danginsa sune dangin Ummynta.
Bakaramin sab'ani Inna Saude suka samu da Bappa ba a lokacin wanda shine karin tsanar da Inna Saude tayi mata ita da Ummynta.
Tabbas tana ciki kewar mahaifiyar ta sosai kuma har yanzu zancen Ummynta bai kara hadata da Bappa ba.
INNA SAUDE
Ta gaji da cin magani ta sake fuskarta ya yin da suka cigaba da gudanar da rayuwarsu kamar yadda suka saba,wani lokaci Agla taji sanyi a gunta wani lokaci tasha fada da hantara musamman ma yanzu da kishin ya dan motsa mata ga aikin gida da take jibga ba abun da ya ragu.
Bayan sati daya da dawowar su sai ga Kabeer yazo gidan gaida inna harma ya yi mata Alkhairi wanda yasakata a cikin farin ciki (kunsan halin Inna Saude da son banza😅)
A lokacin Kabeer bai samu haduwa da Baffa ba da Agla sun dai sha fira da Salmat wacce duk rabin fira akan Agla ne har ya koma tana daki bata fito ba.
Sai a sannan tama tuna shima sunansa Kabeer ko shine Salmat ke nufi oho bata da mai b'ata amsa sai kawai ta share ta cigaba da linke tufafinsu da ta wanke.
BAPPA
Mashaallah cigaba yana ta samuwa Allah ya sakawa shago Albarka kasuwanci yana dan bunkasa dai_dai gwargwado yana iya kokarin sa domin tara kudin da zai biyawa Agla kudin WAEC gashi ta zo kusa ana bukatar kudin registration.
Duk da cewa Makarantar gwamnati ce amma wai governor kudin NECO kawai ya biya duk wanda ya zana WAEC to bazai yi NECO ba idan kuma kanason zana biyu sai dai mahaifanka su biya ma dayan.
Yana waya da Dadda da kuma Abba Muktar ana gaisawa.
KABEER
Duk zuwan da Kabeer yake yi baya haduwa da Agla; sau daya ne ya taba haduwa da ita lokacin da ya kai su Batul gidan su suka wuni, Inna tasakata yi musu rakiya.
Tabbas shi yasan Son Agla bashi yasakawa kansa ba Allah ne ya jarabcesa dashi kuma yana fatan ta zama mallakinsa.
Bayan wani lokaci KABEER yaje ya samu mahaifinsa kan cewa yana son yaje gidansu Aleeya ya nema masa Izinin Mahaifin Agla yana son fara zuwa zance gurin ta.
(Maryama kina ina 😅😂)DR AYSHERT
Duk wani bincike wanda zatayi game da wurin da Haidar ya sauka ta kammala shi har ma tayi booking flight jirgin ta zai daga gobe da safe inshaallah,duk wani shirinata ta kammala har takardar neman izzini ta tura a hospital, yanzu haka waya take mom d'inta tana gayamata cewa gobe jirginta zai tashi zata wuce India, cikin d'an nuna damuwa mom d'in tata take tambayar ta "Dafatan kina lafiya Baby ko likata zaki je gani?"
"No mom kinsan yanayin aiki stresses yamun yawa kawai zance na huta ne na d'an wasu watanni"
Daga chan cikin wayar mom d'inta tace "eh hakan nada kyau baby but wata nawa zakiyi a chan"
"Nima I don't know just kawai ki sanar wa dad domin bazan samu damar kiran nasa ba kuma idan na shigo Kano bazan shigo gida ba"
"Ok no problem nima cikin satin nan zan wuce Germany, safe journey"
"Ok bye mom luv u much"
Karfe goma na safe jirginta ya d'aga a SULTAN ABUBAKAR III INTERNATIONAL AIRPORT
{ SAI KANO TA DABO TUMBIN GIWA}Show me love patronize my book _Diyah❤️
Zeesardaunerh ce
( Y'ar karamar su babbar su👧🥰🤩)
# comment
# like
# sharecomment and vote d'inku shike Karamin kafin guiwar typing💋
![](https://img.wattpad.com/cover/260818017-288-k618322.jpg)
YOU ARE READING
WASU MATAN✔
Short Storyبسم الله الرحمن الرحيم WASU MATAN Littafi ne da ya kunshi halayen matan mu na yanxu ko nace matan zamani,halaye masu kyau da ma akasin su. Wannan littafi ya kunshi Kishi,kiyayya,tausayi,dama sauran su. INA ROKON UB...