👩👩👧👧 WASU MATAN 👩👩👧👧
@2022
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
Story and Writting
by
Zainab Sardaunerh
🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
⚜️©J.A.W📚🖌️
بسم الله الرحمن الرحيم
Da sunan Allah mai rahama mai jinkai
Ya ALLAH YADDA NAFARA WANNAN LITTAFIN LAFIYA KA YARDA NA KAMMALA SHI CIKIN KOSHIN LAFIYA.
SADAUKARWA
WANNAN LITTAFIN SADAUKARWA NE GA FADILA SANI BAKORI,HAFSAT ZUBAIRU SAMBO(Autar mama)AMINA MUHAMMAD BASO, MUMMYN SHUKURA,ASIYA MUHAMMAD,MAMAN AMATULLAH,MAMAN NUSAIBA,RAHMA KOISE,SISTER MIE AND HABIBTY NASMAH LOVE U ALL GUYS♥️♥️♥️
GODIYA
GODIYA MARA MISALI GA PHARTY BB,UMMU MAHIR,MOM ISLAM,UMMU ABDALLAH DA KUMA DAUKACIN MEMBERS NA JARUMAI WRITTER'S ASSOCIATION,MY DEAREST FAN'S SON SO FISSABILILLAH💓💓💓
BOOK 2
Page 87&88
"Umma!!"
"Lafiya kike kwalamin ƙira haka shalele,me ya faru?"
"Komi ma ya faru Umma,komi ya faru wallahi"
"Ban fahimce maganarki ba Maryama kimin dalla-dalla yadda zan fahimta"
Mikawa Hajiya Hawwa wayar tata tayi domin taga abun da yake aciki,ita kanta Hawwar ba ƙaramin faɗuwa gabanta yayi ba alokacin da idanuwanta suka mata tozali da photon Kabeer a tsaye ras cikin koshin lafiya,itama kasa yadda da abunda tagani tayi sai da taga vedionsa yana tafiya harda magana ma sannan.
"Dagaske ne abunda idanuwana suka ganar mun shalele,ko dai tsoffin photonansa ne"
"Nakasa yadda Umma,taya hakan ta faru,yaushe ya samu lafiya bansani ba,wa ya ƙarya asirin jikinsa?"
" Shine abunda yake cikin raina Maryama,tsaya ma wa ya turo miki wannan photon"
"Wallahi wata maƙociyata ce ta kirani tana tayani murna wai ashe mijina ya samu lafiya shine ko na sanar musu"
"Me kikace mata "
"Me zance mata mana Umma,kawai dariya maganarta ta bani saboda nasan ba mai iya ƙarya asirin idan bamu ba,taje gidan iyayenta ne ta haɗu dashi a bakin titi,shine fa da taga ban yarda ba ta ɗauko min photonsa harma da vedion da kika gani,yanzu ni Umma kaina a kulle yake har ciwo yake mun miye mafita Umma? Kuma taya hakan ya kasance"
"Nima ban sani ba Maryama,bansan taya hakan ya kasance ba"
"Allah Umma Kabeer shine rayuwata idan har na rasashi mutuwa zanyi Umma ko na haukace,ina matuƙar kaunarsa Umma,tunda har suka iya ƙarya asirin jikinsa zasu iya rabamu Umma"
"Hakan ma bazai taɓa faruwa ba shalele,karki manta har yanzu Ummanki tana raye fa,bazan bari ki rasashi ba ki saka hakan a ranki"
"tou Umma,amma wallahi ina tsoro"
"Yawwa,kar kiji tsoron komi ina tare dake,maza ki tashi yanzun nan ki koma gidan mijinki, kiyi iya ƙokarinki ki ƙarkato da hankalinsa izuwa gareki,nafison ya kasance atare dake kina ganin duk wani motsinsa,kar ki samu damuwa kuma ƙar kiyi kuka yanzunnan illela na nufa bazan tsaya komi,dolene a yau ko gobe na haɗu da boka dajjal,zan samu cikkakken bayani gameda ƙarya asirin jikinsa da suka yi kuma zan saka ya miki sabon aiki a kansa bazan dawo miki ba sai da daddaɗan labari"
YOU ARE READING
WASU MATAN✔
Short Storyبسم الله الرحمن الرحيم WASU MATAN Littafi ne da ya kunshi halayen matan mu na yanxu ko nace matan zamani,halaye masu kyau da ma akasin su. Wannan littafi ya kunshi Kishi,kiyayya,tausayi,dama sauran su. INA ROKON UB...
