Page 10&11

272 38 0
                                    

👩‍👩‍👧‍👧 *WASU MATAN*  👩‍👩‍👧‍👧
          @2021

~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤

*Story and Writting*
           by
*Zainab sardaunerh*

   بسم الله الرحمن الرحيم
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai 📚

         _________________      
       ______
🅙︎𝗮𝗿𝘂𝗺𝗮𝗶 🅦︎𝗿𝗶𝘁𝗲𝗿𝘀 🅐︎𝘀𝘀𝗼𝗰𝗶𝗮𝘁𝗲𝗱📚🖊
https://www.facebook.com/101679598253281/posts/101680068253234/?app=fbl
_Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa illmantarwa, nishadantar tare da fadakarwa da jama'a bisa harshen hausa_

                 🏔🅙︎🅦︎🅐🏔

   *BARKAR MU DA DAWOWA* *HUTUN KARSHEN MAKO*

*Page* 11~~12

   Daga gidan Ubanki na ke!

"Ubana?"
"Ubana kace fa?"

"eh, ko Ubana ba Ubanki bane?"

"to waya sani" tapada tana jan tsaki, "tou wai tsayama mika je yi a chan din??"
"kamarya? banfahimci tambayarki ba"
"ai nasani bazaka fahimta ba, tunda kana  chan tare da wadan chan makirran..." bata karasa maganarta ba ya tari numfashinta cikin bacin rai yake cewa "su waye makirran??"
"kafini sani ai"cikin ranta kuwa mamaki take taya kabeer ya samu kwarin guiwar da zai tsaya yana ja'inja da ita anya...
maganarsa tadawo da ita duniyar tunanin da ta lula.
    "Na fiki sani? Uwar ta wace makirar ko k'annena?" ya fada cikin muryar da ta d'an tsorata ta amma sai ta waske bata nuna ba tayi k'asa da muryarta tana cewa" duka "tare da tabe baki.

    Da tsauri ta dafe kunchin ta saboda wani azababben zafi ne ya ratsa shi da zuciyarta tare da kai ziyara a k'wakwalwarta,batare da ta dawo hayyacinta ba taji wani zafin a dayan kunchin, bata ma san lokacin da ta lailayo ashar ba tana nuna kanta tare da cewa "ni!ni!!ni kabeer ka mara? marin ma har biyu?"

Cikin karfin hali tare da danne a bunda ya keji a zuciyarsa yace mata....

"Eh an mareki, nace na mareki, ke wace ce da baxan mareki ba?
   Ni kabeer sa'id mata ta zata zagi uwata?

"To tsaya kiji ba'ayi halittar da zata zagar min uwa a gabana in kyaleta ba wlh! kika kara gigin zagarmin uwa na rantse da Allah sai makiyin ki yaga tausayinki" yafada yana shigewarsa cikin dakin sa.

         Tsaye take mamaki,Al'ajabi,rudu tare da tashin hankali suka dirar mata bayan tadawo hayyacin ta daga marin bazata da kabeer yayi mata ko motsin kirki ta gaza yi ga maganganun da ya gaya mata!

safa da marwa ta dingayi a cikin palon nata.
  wai ni? ni  maryama ? ni dinnan kabeer ya mara harya ke gaya mun magana kan shashashar uwarsa da k'annensa? wlh baza ta sabu ba wai bindiga a ruwa.

      "Dole nagaya ma inna mu  koma gun boka dajjal in ba haka ba to wlh akwai matsala,  wanki hulla na neman kaimu dare.

  "Umma kin ga Khaleel Ya balla mun abun wasa na ko?"

      "Karya take Umma ita ce ta fara daukar nawa"

"Wlh Umma shine ya fara".

         "Wai khaleel miyasa baka jin magana? Khaleela yayar kace,
miyasa ka rena ta dayawa?

shiru Khaleel Yayi

"ba tambayar ka na ke ba"

"Umma kiyi hakuri bazan sake ba"

"ita zaka ba hakuri bani ba,kuma kar na sake jin ka ce mata karya take,kana jina ko?"

"eh Umma"

"ok oya bata hakuri"

"Anty khaleela kiyi hakuri kinji bazan sake ba" "kinyi hakurin?

"eh"

"Umma tace ta hakura"

"ok tafi palo ka ci gaba da wasarka"

da "tou" ya amsa ya fita a dakin.

"Khaleela zo nan"

"dan Allah Umma kiyi hakuri"

"wani abun nace miki ne?"

"a'a"

"ok zo nan nace"

hawaye ta fara tana cewa "Umma bazan sake ba wlh"

"miyasa kika d'aukar masa kaya?"

"um umm.. shine.."

"ba tambayarki nake ba?"

"Allah umma shine yamun jifa da kaya sai da ya balle"

"shine ke kuma kika balla masa nasa ko?miyasa baki da hakuri ne Khaleela?Khaleel ba kanin ki bane,idan baiji sanyi gunki ba gun wa zaiji ? banasan irin wannan abun kina jina ko?

"eh"

"dama nasan kece baki da gaskiya sai shegen bakin kawo kara" tafada tana hararar ta "kar na kuma ji, fice ki bani guri."

   Bayan fitar Khaleela Ta cigaba da linke kayan.

       Bayan ta gama ne ta gyara dakinta,palon ma tazo ta gyara,taje dakin Abban Khaleel Shima ta gyara masa,ta share harabar gidan bayan ta kammala ne ta ma su Khaleela wanka,ta shiryasu cikin kaya kala guda matsu kyau tace musu "oya kowa yadauko home-work dinsa yayi"

su amsa da "tou" a tare

   Ita kuwa wanka taje tayi tare da d'auro alwalla domin lokacin magrib ya gaba to.
  Palon ta shiga tana cewa "Khaleel it's time for prayer,ku tashi kuyo alwalla "tou umma" su   kace ita kuwa tanufi room dinta.

Abaya ta zura tare da d'auko hijab dinta da darduma domin an fara kiran sallah.
  koda ta fito har Khaleela tasa hijab dinta sun shinfida dardumarsu irin ta yara, ita ma shinfidawa tayi suka fara bin masallacin unguwarsu.

   Bayan Azeema ta i'da da sallar ne tasa su kayi azkar dinsu,wanda basu iyaba ta cigaba da koya musu cikin ma Allah yayiwa y'ayan nata basira ga wayo hadi da girman jiki dan ita suka dauko fannin zafin girma,idan kaga twins dinta zaka dauka sun kai six or saven year hardai Khaleela da take mace.

   Suna nan zaune tana koya musu karatu da azkar akayi kiran i'sha, suka sake bin masallacin.
   
    Da suka idarne ta tashi ta nufi room dinta domin ta gyara jikinta  because lokacin dawowar Abban Khaleel  ya kusa.
 
      Lotions ta murzawa fatar ta mai mugun kamshi ta saka riga da siket na atamfa, ta shafawa fuskarta powder tare da sakawa idanunta kwalli,ta murzawa lips din ta lips glow,ta na cikin daurin dan kwalin ne ta juyo muryar su Khaleel suna cewa................✍️✍️✍️

  *Zeesardauner ce*

       ( ~Y'ar karamarsu babbar~ ~su~👧🥰🤩)

# _comment_
# _like_
# _share_

*Comment and vote dinku shike* *karamin karfin guiwar* *typing*

WASU MATAN✔Where stories live. Discover now