👩👩👧👧 WASU MATAN 👩👩👧👧
@2022~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
Story and Writting
by
Zainab Sardaunerh🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo⚜️©J.A.W📚🖌️
بسم الله الرحمن الرحيم
Da sunan Allah mai rahama mai jinkaiYa ALLAH YADDA NAFARA WANNAN LITTAFIN LAFIYA KA YARDA NA KAMMALA SHI CIKIN KOSHIN LAFIYA.
SADAUKARWA
WANNAN LITTAFIN SADAUKARWA NE GA FADILA SANI BAKORI,HAFSAT ZUBAIRU SAMBO(Autar mama)AMINA MUHAMMAD BASO, MUMMYN SHUKURA,ASIYA MUHAMMAD,MAMAN AMATULLAH,MAMAN NUSAIBA,RAHMA KOISE,SISTER MIE AND HABIBTY NASMAH LOVE U ALL GUYS♥️♥️♥️
GODIYA
GODIYA MARA MISALI GA PHARTY BB,UMMU MAHIR,MOM ISLAM,UMMU ABDALLAH DA KUMA DAUKACIN MEMBERS NA JARUMAI WRITTER'S ASSOCIATION,MY DEAREST FAN'S SON SO FISSABILILLAH💓💓💓
BOOK 2
Page 9&10Kayan da aka kwaso wurin da aka siye su aka mayar da su, da yake akwai sanayya sosai tsakanin mai wurin da mama Kareema kuma sunyi magana dashi game da kayan,gidan mama Kareema suka wuce tare da motar da ta kwaso sauran tarkacen daki da kuma kayan kitchen bayan sun bawa Batul mukullin gida ta koma dashi.
A spare room suka ajiye kayan kitchen din Agla da sauran kayayyakin nata domin barinsu wurin Inna Saude bazai haifar d'a mai ido ba duk da cewa tayi sanyi amma hakan ba shi ke nuna zata chanza ba domin mai hali baya fasa halinsa.
Wasu daga cikin turarukanta suka dibar mata tare da Khumra tayi amfani da su domin duk wanda yasan Aleeya yasanta ma'abociya son kamshi ce ba kadan ba,sun dibarwa Inna saude da Baffa kulolin da zasu saka abincin su aciki duk wani abun amfani sun dibarwa Agla wanda zata iya amfani da su.
Sai 4:40 suka dawo gidan, ko da suka iso an kawo spare katifar Agla ya Anwar ne da kansa ya shigar da ita dakin nasu tare da sauran kayayyakin da suka zo dasu domin koda suka shiga gidan yana ciki Mama Kareema ta taso keyarsa gaba domin tana lura da take_takensa wa yake kunya Baffa ko Dadda bata sanar masa ba.
Sun dauka Inna Saude tace wani abun game da ajiye kayan da akayi gidan mama Kareema amma bata ce komi ba kayan ma da aka bata batace ta gode ba kuma basu ga alamun ta rena ba.
Abunda su kansu basu sani ba shine duk wadannan abubuwan a yanzu basa gaban Hajiya Saude,ba abunda ke a zuciyarta face BASHIN GABA wutar fansa ce ke ruruwa a zuciyarta game da Maryama kudi ko wani abu ko kadan basa burgeta abu guda ne ya tsaya mata a zuciyarta cin kashi da cin mutuncin da Maryama tayi mata,tabbas sai tarama domin ita ba ta barin bashi ko kadan sai ta nunawa Maryama cewar ta debo wutar dafa kanta,ko ba jima ko ba dade Kabeer zai tashi kuma soyayyar Aleeya bazata goge ba a zuciyarsa.
Da yake mama Kareema tadan sauko ko nace ta sauko gabadaya; kayan lehen Agla ma da ita aka fitar da dinkaku wadanda Aleeya zata saka tun da an riga an dunka,sanin kansu ne kayan sun mata yawa ba kadan ba amma hakan suka bar mata abunta,kayan Bacci ma wadanda a normal suka fitar mata sauran kuwa za'a ajiye sai tayi aure.
Sun dibarwa Inna Saude atamfofi da laces harma da shadda wadanda ba a dinka ba haka ma Salmat da Ramlat, Murja da Anty Amrah sai kuma tsohuwa mai ran karfe Dadda.
Kawayen Agla ko wanensu an fitar mishi da Atamfa da lace guda_guda, hakama Inna Laure basu manta da ita ba ita da yaranta.kayan rar_rabesu ake amma kamar ba a diba,babu karya duk wani abu da aka saka a cikin lehen babu karami, ba karamin kokari sukayi ba wujen hada lefen kuma ko wanne akwati makil ya ke da kaya cikinsa.
Sauran suturar mama Yelwa ta ce wa mama Kareema idan zata koma sai ta wuce dasu chan wujinta ta ajiyewa Agla har Allah ya nuna mata ta sanye duka wadan chan da suka fitar mata,akalla ba a kasara ba ace ko da yaushe Agla ta saka kala biyu a yini to tabbas sai tafi wata biyu ba ta sake mai_maita wadanda ta saka ba.
Fridge din da yaya Umar ya siyawa Agla aka barwa Inna Saude tayi sana'a dashi,gas cooker da mijin mama Yelwa ya bawa Aleeya an ajiye mata abunta,duk abunda ya dace sai da su mama Yelwa suka zartar tare da shawara da Dadda da kuma d'an kanen nata.
Mama Yelwa ta buga ko ina akan Baffa ya bar mata Aleeya ta koma da ita amma yaki yarda, har da Abban su Murja ya saka baki amma Bappa ya basu hakuri bazai iya bari AGLA tayi nesa dashi,idan har bata tare dashi taya za yasan cewa bata cikin damuwa,Anty Amrah ma ta saka yaya Umar ya yi magana amma ba nasara haka suka hakura suka koma Yola cike da kewa da kuma rashin jin dadin kin amuncewar Baffa.
Abu guda Mama yelwa ke gudu takurar da Agla zata Shiga acikin Unguwar duk da cewa ba yawan fita take ba amma kuma ai dole zata koma Islamiyya kafin ta jona higher,jita_jitar da ke yawo game da fasa auren a Unguwar ta kazanta bakaramin sakawa auren ido akayi ba.
Yanzu duniya ta lalace Yan Adam basa kunyar yiwa wani Kazafi dan gane da abunda basu da tabbaci akansa,Abunda mutum baya ganewa shine kaddara tana kan kowa kuma idan muguwar Kaddara tazo acikin rayuwar ka ba yadda zaka yi sai Addu'a domin ba wanda ya isa ya hana faruwar hakan,Rayuwar Musulmi a ko da yaushe acikin jarabawa take,sun dauki munana ma mutum zato ba abakin komi ba.Gida ya watse ya koma Shiru Mama Kareema ma takoma gidanta itada Ramlat gidan ya koma daga su sai Dadda kuma har yanzu ta kasa komawa dai_dai kamar yadda Inna Saude bata sauya ta koma yadda take da ba.
Kulawa sosai Baffa da Dadda ke bawa Aleeya; suna iya kokarin su ganin cewa basu barta a cikin damuwa ba,ko kad'an basa sun suga tana tunani.
Su Rahama na yawan kawo mata ziyara da duba halin da take ciki mussamman ma Amina da suke a kusa.
Matan da ke Unguwar suna zuwa jajantawa Inna Saude game da abunda ya faru,WASU MATAN ma gulma ce ke kawo su gidan domin ganin halin da Ahalin gidan ke ciki,dama Inna Saude ba ragowa take yiwa mutanen Unguwar ba idan har aka tab'ata, idan suka zo suyi ta fadin abubuwa kala_kala wai wance ce tace hakan,ko lokacin su bata da duk da cewar ta saka su a BAKIN LITTAFI kuma duk kansu sai ta rama su jira lokaci.
SALMAT
Salmat uwar jidali duk wanda taji yana zagin Addanta ko yana fadin munanan kalami akanta sai inda karfinta ya kare,mace ko namiji,Babba da yaro ba wanda take ragawa komi girman mutum.
BAYAN SATI BIYU
Sati Ukku kenan da faruwar wannan Al'amarin, so daya Aleeya ta fita wajen da sunan zuwa ISLAMIYYA domin zaman gidan yana saka zuciyarta a cikin wani yanayi dakyar Dadda ta yarda ta barta ta fita da sunan zata biya gidan su Amina Idan Salmat ta dawo daga aiken da Inna tayi mata ta risketa chan su wuce, tayi gudun gara ta farma damo ashe damuwar ce zata karawa kanta bata sani ba domin kuwa tana fita idanuwa suka koma kanta tanajin yadda ake zancenta mussamman wasu gungun MATASA da tazo wucewa tun kafin takaice wurinsu ta ji yadda suke jifanta da kalma mafi muni wato Zina har ana nunata da yatsa wani daga cikin samarin yace..
"dubeta fa har wani jan aji ake mana da wani katon hijab da likabi idan ka ganta kamar ta Allah amma Allah kadai yasan mugun abunda ake shukawa a boye"
Wani daga cikin su yace "nifa yarda naji ma ana fada amma ban shaida ba
wai wani vedion ta ne ya gani no kuma kamata yayi ana lesbian da ita,kasan ance manyan hajiyoyi sunfi son irinsu kyawawa...🖊️🖊️Show me love patronize my book Diyah❤️
Zeesardaunerh ce
(~ Y'ar karamar su babbar su~👧🥰🤩)
# comment
# like
# sharecomment and vote d'inku shike Karamin kafin guiwar typing💋

YOU ARE READING
WASU MATAN✔
Short Storyبسم الله الرحمن الرحيم WASU MATAN Littafi ne da ya kunshi halayen matan mu na yanxu ko nace matan zamani,halaye masu kyau da ma akasin su. Wannan littafi ya kunshi Kishi,kiyayya,tausayi,dama sauran su. INA ROKON UB...