👩👩👧👧 WASU MATAN 👩👩👧👧
@2022
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
Story and Writting
by
Zainab Sardaunerh
🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
⚜️©J.A.W📚🖌️
بسم الله الرحمن الرحيم
Da sunan Allah mai rahama mai jinkai
Ya ALLAH YADDA NAFARA WANNAN LITTAFIN LAFIYA KA YARDA NA KAMMALA SHI CIKIN KOSHIN LAFIYA.
SADAUKARWA
WANNAN LITTAFIN SADAUKARWA NE GA FADILA SANI BAKORI,HAFSAT ZUBAIRU SAMBO(Autar mama)AMINA MUHAMMAD BASO, MUMMYN SHUKURA,ASIYA MUHAMMAD,MAMAN AMATULLAH,MAMAN NUSAIBA,RAHMA KOISE,SISTER MIE AND HABIBTY NASMAH LOVE U ALL GUYS♥️♥️♥️
GODIYA
GODIYA MARA MISALI GA PHARTY BB,UMMU MAHIR,MOM ISLAM,UMMU ABDALLAH DA KUMA DAUKACIN MEMBERS NA JARUMAI WRITTER'S ASSOCIATION,MY DEAREST FAN'S SON SO FISSABILILLAH💓💓💓
BOOK 2
Page 27&28
She can't remember what happened bayan faduwar ta;kawai dai ta buda idanuwanta ta ganta a kwance saman bed dinta,yunkurin tashi tayi amma kanta ya mata nauyi hanunta ta dago da niyar rike kan nata shima sai taji radadin azaba na ratsata da sauri ta kalli hanun nata ta gansa anyi dressing dinsa da bandage sannu_sannu abunda ya faru ya fara dawo cikin kwakwalwarta,tana bukatar tashi amma kan nata ya mata mugun nauyi,she has no option da ya wuce ta koma kwance.
A hankali ta buda eyes dinta guda takai duba izuwa tangamemen agogon dake manne a bangon dakin 2:30am ta kwashe almost four to five hours tana bacci,waye ya kawota nan sannan kuma waye ya yi mata dressing din ciwonta?
Tambayoyi ne birjik acikin Kwakwalwarta amma ba wanda zata tambaya,sannu a hankali bacci barawo ya sake awon gaba da ita amma ko kadan batajin dadinsa.
Gidan so silent ba wanda ya fito,masu zuwa makaranta suki fitowa,Haidar ma haka daya daga cikin securities ne ya kai marwan makaranta because part d'in Amna a garkame yake yayi nooking har ya gaji Ummiey ma tayi ta kiranta da waya amma bata picking Amar ma haka,Suhailat kawai tayi breakfast a gidan sai Ummiey.
HAIDAR
Hayaniyar da Ayshert tayi masa a ka jiya ya haddasa masa matsanancin ciwon kai ko sallar subhi da kyar yaje masallaci yayi ta.
Amna da ya Amar kuwa tsoron yah lion ne ya hanasu fitowa,ko wannensu na tsoron haduwarsu dashi da kuma hukuncin da zai yanke musu.
Makure take a karshen bed d'inta abun duniya ya sha mata kai tana tunanin yadda hukuncin ta zai kasance a gurin yayan Jauhar,gabadaya a tsorace take batasan kalar matakin da zai dauka akan wannan lamarin ba,duk abunda ya faru laifintane da tasan Ayshert nada iskokai bazata nemi yin rigima da ita ba;a duniya ba abunda take tsoro irin mutum mai aljanu,bata manta abunda ya faru jiya ba bayan Ayshert ta zube jini na zuba daga hannunta.
FLASH BACK
Ga tsoro ga ban tausayi,mutum mai aljanu yana matukar bata tausayi da tsoro haka ta daure tayi ta maza ta fito daga bayan kofar da take lab'e da niyar ta fita waje ta kira mutane akawowa Ayshert taimakon gaggawa gabadaya ta manta sai da takawo tsakiyar palourn sannan hankalinta ya dawo kanta cikin kan kanin lokaci ta tuna waye a cikin dakin a hankali ta tsaya kamar wacce aka dasa ta kasa gaba bare baya.
YOU ARE READING
WASU MATAN✔
Storie breviبسم الله الرحمن الرحيم WASU MATAN Littafi ne da ya kunshi halayen matan mu na yanxu ko nace matan zamani,halaye masu kyau da ma akasin su. Wannan littafi ya kunshi Kishi,kiyayya,tausayi,dama sauran su. INA ROKON UB...
