👩👩👧👧WASU MATAN 👩👩👧👧
@2021
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
Story and Writting
by
Zainab Sardaunerh
🔔📚
JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
⚜️©J.A.W📚🖌️
Assalamu Alaikum sunana Ummu Maleek
Muna siyarda kayayyaki masu kyau da inganci
munada maganin Ni’ima macce duk rashin ni’imarta Insha allahu rabbi zataji ni’ima tamkar korama ±💃💃💃💃
Muna da maganin infection ko wanne iri duk nacin infection Insha allahu rabbi kikayi amfani dashi zai rabu dake
munadasu Tsumin kala kala Munada gumbar nonon rakumin munadata dabino
Akwai mallakar miji masu zamu🔥🔥wanda inki kayi amfani dashi mijinki ko dutsene shi saiya tanka
Munada Emergency thghting duk yadda kika kai da budewa zaki hade tsaf Insha allah’ akwai hips Elargenment akwai breast Elargenment
Munada kayayyakin mata kala da iri masu zafi🔥🔥tamkar boom😻😻sha yanzu magani yanzu
Duk abinda kake da bukata zaka iya nemana ta👉07037112549
©️♤♡ Zeesardaunerh
Page 95~~96
Ba kowa bace face Dadda mahaifiyar Malam Yusuf wato Bappa tsohuwa mai ran karfe,da gudu Salmat taje ta rungumota tana mata oyoyo ya yin da Agla ta rike hannunta suna gaisawa da ita cikin farinciki da kaunar juna.
Murmushin yake wanda yafi kuka ciwo Inna Saude ta aro ta yab'awa fuskarta itama ta shiga jerin masu yiwa Dadda barka da zuwa tare da murnar ganinta.
Idanuwa kai Dadda ta zuba mata domin sarai ba halin Saude wanda bata sani ba.
Sosai Bappa ya yi farincikin ganin mahaifiyar sa ba kad'an ba duk da cewa daman yasan da zuwan na ta,raba dare suka yi suna hirar yaushe gamo dukansu banda Inna Saude ta sharbi baccin ta son ranta Bayan ta boye dubu biyar da kuma turare guda daga cikin kayan da Kabeer ya kawo na jin kira domin baza a kasa dai_dai da kowa a bata ba,dame zata tashi kenan?gara walla tayi wa kanta kaso kafun a kaiwa waccan tsohuwar cewa ga Dadda.
Tun da safe sai ga mama Kareema tazo ita da Ramlat,yah Anwar baya nan shiyasa basu zo tare da shi ba gidan ya kara cika kowa cikin farin ciki sabanin Inna Saude da ke jibgar aiki, ta saba duk wata wahala Agla keyi ita kuma tasha bacci son ranta amma yau komi ita keyi Dadda ta rike mai sunanta ko ina suna tare ba batun wani aiki, da Aleeya ta tashi zata kirata tace ta dawo ta zauna ba ta gaji da ganin ta ba tayi kewarta sosai.
Har vedio call sukayi da Mama yelwa babbar yayarsu(wato diyar Dadda ta fari ) dake yola a wayan mama Kareema,taji kamar tayi tsuntsuwa tazo,Anwar ma haka sunyi vedio call da Dadda har tsokanar ta ya dingayi haka ake yi, ayi doguwar tafiya baza a sanarwa miji ba gaskiya da sake kar fa tasa yace ya fasa,ya dage sai janta fira yake alhalin zuciyarsa da ruhinsa suna kan Agla wacce ke zaune a gefen Dadda batare da ta sanya hijab ba.
A ko da yaushe ako wane lokaci ko kuma yanayi muddin yayi tozali da fuskarta sai yaga tamkar ana zuba mata madarar kyau ne wanda ke karuwa ko wani second,ba karamin farinciki yayi ba na tozali da kyakkyawar fuskarta,tabbas hakurin sa ya kai intiha da yadawo zai sanar da Bappa cewa yana mahaukacin sonta mara iyaka a taimaka a yi masu aure(🤣😂 an maka kutse yah Anwar,Agla ta mai rabo ce Allura a ruwa)
YOU ARE READING
WASU MATAN✔
Short Storyبسم الله الرحمن الرحيم WASU MATAN Littafi ne da ya kunshi halayen matan mu na yanxu ko nace matan zamani,halaye masu kyau da ma akasin su. Wannan littafi ya kunshi Kishi,kiyayya,tausayi,dama sauran su. INA ROKON UB...
