page 65&66

261 34 5
                                        

👩‍👩‍👧‍👧 WASU MATAN  👩‍👩‍👧‍👧
          @2021

Mallakar Zeesardaunerh💜🖤

Story and Writting
           by
Zainab Sardaunerh

🔔📚
JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
             
          ⚜️©J.A.W📚🖌️

Page 65~~66

Ko da Ramlat ta fita Kabeer yana zaune saman mashine dinsa duk alamun gajiya sun bayyana gareshi kai da gani kasan ya Jima anan ga rana ta fito duk sai yabawa Ramlat tausayi gaishesa tayi ya amsa sannan tace ance ya shigo ciki.
   tare suka shiga gidan da Ramlat tana bashi labarin cewa Salmat bata fadi cewa yana waje ba ta tsaya iya yi da kaudi.
   Abun dariya ya bashi domin saida ya murmursa acikin ransa yake cewa,

"duk wanda aka bawa Salmat da Ramlat ko da na kwana biyu ne sai sun sakashi cikin nishadi da dariya "

Ko da suka shiga Palon mama Kareema bata fito ba Salmat kawai ce a Palon cikin jan magana Ramlat ta takalo Salmat aikuwa suka kama gardama da rikici ana cikin haka mama Kareema ta shigo tsit sukayi kamar basu ne ke rashin ji ba domin sun san halinta duk iskacin su basu yi mata gaban baki.

    

   Gaisawa mama Kareema da kabeer su kayi sannan ya bada hakuri Kan abunda ya faru bada gannan bane kaddarace mama tace,

" bakomi Allah ya tsare gaba ya kara kiyayewa"

"Ameen"

Duk yadda ya so ya ga Agla babu hali domin bata fito ba haka ya tafi cikin farin cikin haduwa da ita,yanaji aransa ya samu wani abu da ya rasa duk da ya manta ko minene amma zuciyarsa na sanar dashi cewa ya rasa muhimmin abu a rayuwarsa.

Ko a gida ma da yaje ba labarin da yake musu sai na Aliya da su batul suka tambaisa minene sunanta sai yayi shiru suka dinga masa dariya
a ransu kuwa suna fatan Allah yasa yarinyar nan da tatafi da zuciyar yayan nasu ya kasance ta kwaraice ba Kamar maryama ba.

  Duk da ba haka su ka so ba,son so ace yazamana yayan nasu su kulla Alaka da Adda Asmeey  (Asma'u tsohuwar budurwar kabeer)ganin yadda suke mutunci da junansu duk da kabeer har yanzu bai tuna komi game da ita ba  kawai yana mutunci da ita ganin yadda mutanen gidan nasu keji da ita amma sun san cewa har yanzu akwai soyayyar yayansu a cikin zuciyar Adda Asmeey.

      Suna masa fatan samun wannan yarinya duk da basu yi tozali da ita ba kuma basu san wacece ita ba amma yadda yake ta basu labarinta ko gajiya baya yi yasa sukaji suma ta kwanta musu arai kuma suna son mummy'n Maleek(maryama)ta gane kurenta domin yaseen yah kabeer yana yin aure sai ta raina kanta sai ta gane ba dangin miji ba abun wulakantawa bane kuma addu'a makamin Mumuni ce bata bar komi ba(🙄).

************

Har na manta da batun ciwon da naji a kafana domin ban dauke shi serious ba duk da cewa kafan na dan yi mun ciwo,mun yini cikin farinciki da walwala a gidan,sosai na godewa Allah da yah Anwar ba ya nan ya yi tafiya.

Bangaren Salmat da Ramlat kuwa shirme kala_kala suka yi Kamar su yallallaba,ďan waken fulawa,dan ta malili da dai sauransu(d.d.s)kuma mama Kareema bata hana su ba,idan suka gama wannan shirmen sai suyi wani,sosai suka ji haushin rashin yah Anwar abokin shiritarsu da yana nan da abun sai yafi dad'i da armashi.

Duk da da girkin dare su sukayi jellop din macaroni da nikaken Kofi Salmat uwayen kwadai ta bude ciki ta kwashi girkin tana santi Kamar basu ne suka yisa ba,Ramlat ba biye mata tayi suka narki abinci iya son ransu.

WASU MATAN✔Stories to obsess over. Discover now