👩👩👧👧 WASU MATAN 👩👩👧👧
@2022
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
Story and Writting
by
Zainab Sardaunerh
🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
⚜️©J.A.W📚🖌️
بسم الله الرحمن الرحيم
Da sunan Allah mai rahama mai jinkai
Ya ALLAH YADDA NAFARA WANNAN LITTAFIN LAFIYA KA YARDA NA KAMMALA SHI CIKIN KOSHIN LAFIYA.
SADAUKARWA
WANNAN LITTAFIN SADAUKARWA NE GA FADILA SANI BAKORI,HAFSAT ZUBAIRU SAMBO(Autar mama)AMINA MUHAMMAD BASO, MUMMYN SHUKURA,ASIYA MUHAMMAD,MAMAN AMATULLAH,MAMAN NUSAIBA,RAHMA KOISE,SISTER MIE AND HABIBTY NASMAH LOVE U ALL GUYS♥️♥️♥️
GODIYA
GODIYA MARA MISALI GA PHARTY BB,UMMU MAHIR,MOM ISLAM,UMMU ABDALLAH DA KUMA DAUKACIN MEMBERS NA JARUMAI WRITTER'S ASSOCIATION,MY DEAREST FAN'S SON SO FISSABILILLAH💓💓💓
BOOK 2
Page 75&76
GIDAN BOKA
"Kinga wannan turarashi zata yi a cikin ɗakinta ta tabbatar da cewa ya shakesa;wannan kuma zata saka masa shine a abinsha ta tabbatar da cewa ya shanye abinshan baki ɗaya ƙar ya rage komi,idan aka yi yadda nace to ba shakka Abubakar ya dawo a tafin hannunku sai yadda kuka yi dashi
"Allah boka"
"Ina miki wasa ne Hanne"
"A'a babban malamina"
"Ki gaya mata kar ta samu damuwa idan taga ya yi dogon bacci,dama hakan zai faru,ta hakan ne kaɗai zan aiwatar da aikin ku akansa"
"Godiya nake boka"
Bayan Hanne ta fito daga gidan boka,bata tsaya ɓata lokaci ba,ta nufi gidan Umma Hadiza tare da zayyane mata komi kamar yadda boka ya faɗamata.
"Wallahi Hadiza abun nan yana matukar bani mamaki,bansan wane kasurgumin boka waɗannan mutanen suke zuwa gurinsa yana musu aiki ba,shiyasa ko kaɗan basu wani damu da auren da Abubakar ya ƙara ba domin sun san abunda suka shirya;yanzu dai yace na faɗamiki aiki akanta ko kaɗan bazai yu ba,suma a tsaye suke ba a zaune ba,don haka dole akalar aikin zai koma akan Abubakar ne saboda shine mai yin sakin;yace kuma na ƙara tabbatar miki matukar aka aiwatar kamar yadda yace,wallahi gidan Abubakar sai ya yiwa Azeema wuyar zama,da kafafunta zata bar gidan ko da ace bai furta sakin ba,zaman gidan yari sai yafi mata daɗi sau dubu bisa zamanta a gidan "
"Alhamdulillah, idan har hakan ta tabbata ni kuma zan masa kyauta ta ban mamaki,wacce bazai manta da ita ba har abada;dole zan aiwatar da aikin kamar yadda yace a yau ɗinnan batare da ɓata lokaci ba;wayyo Allah daga yau ranakun farincikina sun fara,damuwata ta shekara da shekaru a yau zata yaye,hakika ina cikin farinciki mara misiltuwa"
Kallonta Hanne tayi tare da yin wani murmushin mugunta a baɗini tana cewa "Hausawa sukance idan zaka gina ramin mugunta ka gina shi gajere domin watarana kai ne zaka afka cikinsa;daga yau wannan murmushin naki zai rikiɗe ya koma kuka,farincikin ki zai koma bakincikinki;daga yau ranakun damuwa,bakinciki,danasani da zubar hawaye zasu fara a rayuwarki "
"Ya akayi ne Hanne naga kin tsure guri guda da kallo ko da matsala ne"
Cikin hanzari Hanne tace "A'a ba wata matsala,ba komi kar ki damu,ki cigaba da farincikinki, ki more wannan ranar yadda zata zama cikin ranakun da baza ki taɓa mantawa da su ba "
YOU ARE READING
WASU MATAN✔
Short Storyبسم الله الرحمن الرحيم WASU MATAN Littafi ne da ya kunshi halayen matan mu na yanxu ko nace matan zamani,halaye masu kyau da ma akasin su. Wannan littafi ya kunshi Kishi,kiyayya,tausayi,dama sauran su. INA ROKON UB...
