Page 97&98

178 22 13
                                        

👩‍👩‍👧‍👧 WASU MATAN 👩‍👩‍👧‍👧
@2022

~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤

Story and Writting
by
Zainab Sardaunerh

🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

⚜️©J.A.W📚🖌️

بسم الله الرحمن الرحيم
Da sunan Allah mai rahama mai jinkai

Ya ALLAH YADDA NAFARA WANNAN LITTAFIN LAFIYA KA YARDA NA KAMMALA SHI CIKIN KOSHIN LAFIYA.

SADAUKARWA

WANNAN LITTAFIN SADAUKARWA NE GA FADILA SANI BAKORI,HAFSAT ZUBAIRU SAMBO(Autar mama)AMINA MUHAMMAD BASO, MUMMYN SHUKURA,ASIYA MUHAMMAD,MAMAN AMATULLAH,MAMAN NUSAIBA,RAHMA KOISE,SISTER MIE AND HABIBTY NASMAH LOVE U ALL GUYS♥️♥️♥️

GODIYA

GODIYA MARA MISALI GA PHARTY BB,UMMU MAHIR,MOM ISLAM,UMMU ABDALLAH DA KUMA DAUKACIN MEMBERS NA JARUMAI WRITTER'S ASSOCIATION,MY DEAREST FAN'S SON SO FISSABILILLAH💓💓💓

BOOK 2
  Page 97&98

"Shikenan mun shiga ukun mu,komi yazo karshe...komi ya ƙare..kin haukatamun ƴa kin huta..kin haukata mun ita..shinekenan Maryama ta haukace"

Sabbatu kawai take yayin da kowa ya ƙasa fuskantar inda maganganunta suka dosa,duk ta bi ta rikice sai ɗumumuwa take marasa kan gaɗo,chakumo wuyan Asma'u tayi ta shaketa shaƙar kwarai tana cewa
"Meya kawo ki wannan gidan,uban me ya kawoki gidan ƴata,meyasa kika dawo rayuwarta"
Dakyar da wala haula aka ɓanbare Hajiya Hawwa daga shaƙar da tayi wa Asma'u,cikin faɗa ƙanwar mamar Asma'u ta fara magana "kasheta kikeso kiyi ko me? Ke wacece da har zaki shigo har gidanta ki nemi kassara mata rayuwa,me ta miki,a ina ma ta sanki"

"Gidanta" hajiya Hawwa ta furta cikin mamaki,cigaba da cewa tayi "Gidanta fa kika ce,to bara kiji wannan gidan ba mallakin kowa bane face ƴata ita kaɗai,wannan da kike gani" ta nuna Asma'u "Annoba ce,bakar macijiya ce,matsifa ce wacce ta ke shirin tarwatsa rayuwata"

"Mu ƴarmu ba annoba bace sai dai idan taki ƴar ce annoba kuma matsifa,wannan yarinyar da kike ga itama nan gidanta ne,amarya ce a jiyan ne ta tare a wannan gidan"

"Amarya? ina..karyane wallahi..wallahi karyane hakan bazai faru..bazata zauna a gidannan ba wallahi...tunda tayi sanadin haukacewar ƴata wallahi sai na kassara rayuwata,sai halakata,saina wujijjiga rayuwarta,sai mutuwa tafi mata rayuwa,ita da kanta sai ta dawo rokon Allah ya ɗauki ranta ta bar duniya,da farko rabaki kawai muka yi dashi amma yanzu rayuwarki zan rabaki da ita"

Cikin fushi gwaggon Asma'u tace "Kina maganar an haukata miki ƴa yaushe ƴar taki ta haukace ni zaki ɗinga gayawa mutane maganar banza,waya faɗa miki ƴarki ta haukace,wannan ai shashanci ne da hauka,me kika isa kiyi wa Asma'u idan Allah bai ƙaddara ba"

"Baki ganta ba wallahi ta haukace,dama an faɗamin cewa duk ranar da suka yi ido biyu da wannan yarinyar zata haukace" kallon Asma'u tayi tana cewa "wallahi tallahi ki fara kirgen kwanakin mutuwarki,sai kinyi dana sanin karya alƙadarina da haukatamun ƴa da kika yi,sai kinyi dana sanin kwana ɗayan da kika yi a matsayin kishiyar shalele,ki saka a ranki kin taro abunda zai zama karshen rayuwarki"

Ruwa Batul ta lemawa Maryama a fuska domin tabbatar da abunda uwarta ke faɗa,ruwan na sauka a fuskarta ta buɗe idanuwa ta binsu da kallo tana sauke su a kan Asma'u ta sake saka ƙara,shikenan fa daga wannan ƙarar abubuwa suka sauya domin hauka tuburan ta bayyana ga Maryama sai suruttai take tana cizgar gashin kanta yayin da kowa ya tsaya kallon ikon Allah,idan ta kalli Asma'u sai ta kece da dariya tana cewa "Nice ajalinki..tunda kika aurar min miji sai na kashe ki" sai kuma ta sake fashewa da dariya

WASU MATAN✔Stories to obsess over. Discover now