Page 19&20

222 30 0
                                        

👩‍👩‍👧‍👧 *WASU MATAN*  👩‍👩‍👧‍👧
          @2021

~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤

*Story and Writting*
           by
*Zainab sardaunerh*

   بسم الله الرحمن الرحيم
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai 📚

         _________________      
       ______
🅙︎𝗮𝗿𝘂𝗺𝗮𝗶 🅦︎𝗿𝗶𝘁𝗲𝗿𝘀 🅐︎𝘀𝘀𝗼𝗰𝗶𝗮𝘁𝗲𝗱📚🖊
https://www.facebook.com/101679598253281/posts/101680068253234/?app=fbl
_Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa illmantarwa, nishadantar tare da fadakarwa da jama'a bisa harshen hausa_

                 🏔🅙︎🅦︎🅐🏔
*Follow this link to join my* *whatsApp group*
https://chat.whatsapp.com/LXIF4UAUqeGCWONjQCrG4Y

*Follow this link to join my* *WhatsApp group* : https://chat.whatsapp.com/J7fqJ9AqzNTGfSryVEm4dZ

*Join me on Telegram*
https://t.me/joinchat/yZ0tHN29JA4wMzZk

*Join me on Whattpad*
https://www.wattpad.com/

*Page* 19~~20
 
   Murmushi tayi irin nasu na manya tana cewa "ka duba dining baza'a rasa ba"
"godiya nake umma Allah kara nisan kwana,"dining d'in ya nufa,soyayyen arish da kwai ya zuba cikin plate ya na ci sannan ya hada tea mai kauri ya kora dashi,sai anjima ya yima Umma ta amsa tare da masa Addu'a ya fita daga dakin nata ya nufi chemist dinsa da yake tsayar da magunguna.

    Inna Dije da ke labe cikin dakinnata tun shigowar kabeer, ta kasa ta tsare sai da ta ga yafita daga gidan sannan ta lalibo wayarta ta dannawa Maryama Kira.

Abangaren Maryama Kuwa, itama ba wani isashen baccin kirki ta samu ba sakamakon kiran innarta da tayi domin ta sanar da ita abunda ke faruwa amma bata samu ba,hankalinta ya tashi sosai da yadda kabeer din yayi mata,hakan ke nuna cewa abun da sukayi a kansa yana neman ya warware musu.
     Karar wayar tane ya tashe ta daga baccin hasarar da takeyi, domin ko salla bata samu yi ba gashi har wuraren 9:00 (A'uzubillah) dagawa tayi tare da kara wayar a kunnenta duk atunanin ta  Babar tace;murya inna dije da ta jine yaganar da ita ba innarta bace,zuwan da kabeer yayi gidan da tsawon lokacin da ya d'auka a dakin Umman sa ta sanar mata tare da kara tinzirata hadi da zugata kan ta tashi tsaye, in ba hakanan ba akwai matsala, domin alamu sun nuna aikin dake kansa ya fara warwarewa in ba haka ba "saidai kiji ana guda,kuma in baki yi saurin daukar mata ki ba sirrin boye zai fito fili"
"ok naji da yardar Allah ma hakan bazai faru ba"sannan ta kashe kiran.
     Abu goma da ashirin, kan Maryama ya kara d'aukar zafi sosai fiye da da,domin inna Dije ta kara hautsina tinaninta sosai,tabbas ta san cewa muddin aikin farko da akayi a kan kabeer ya karye to tabbas a ranar aurenta ya kare.Ita kuma bata shiryama hakan ba.
    
      Sake gwada kiran innarta tayi amma number bata shiga,jifa tayi da wyar kan gadon ta dake harmutse,bama shiba har dakin a hargitse yake tana cewa "Dam it"mike damun wayar inna ne wai,Ni maryama ya zanyi yanzun
tafada tana dafe kanta...!

Bayan sun tashi ne daga barci ta  tada yaran sukayi sallar subhi ita kuma tashiga cikin kitchen lokaci na tafiya sosai gashi yaran sun kusa makara zuwa makaranta.
Breakfast ta d'aura bayan ta kammala ne tazo ta musu wanka ta shiryasu cikin tufafinsu na makarantar boko,palon ta fito rike da hannuwansu tace"kuzauna bari na kira Abbanku"
"tou Umma"suka ce then suka zauna bisa carfet din.Dakin Abban khaleel ta nufa,sallama tayi ya amsa ta shiga ciki.
    Sakin baki tayi tana kallansa,ya kamla shirinsa cikin yadi bowl milk colour yasaka hullarsa,sak ya fito hausa fulani,ba karamin kyau ya mata ba kamar tace yau kar yaje kasuwa, bata fuskarta tayi tana cewa "shine ka kwashe ladar ka ko dan kar ka jirani nazo na shiryama"
"no ba hakan bane Ummu Khaleel ai lada ko da yaushe cikin ta kike,naga aikin yamiki yawa ne ga breakfast ga shirya yara, ga nawa shirrin ma shine fa na rage miki tunda yau mun makara bamu tashi da wuri ba"
"ka taba ganin inda lada tama mutum yawa Abban Khaleel"
"a'a Umman Khaleel,domin da tanayi y'ar kyawwar matata zata farama bcox yar aljanna ce da yardar Allah "
       Fadawa tayi bisa faffadan kijinsa tana murmushi take cewa Allah ka barmu tare har a aljanna firdausi mijina"
"Ameen matata"jan hannunta yayi suka fito palon inda yaran suke.
Gaida Abbannasu sukayi ya amsa yana tambayar sun tashi lafiya"lfy lau Abba"
"mashaallah"ya fada yana zaunawa kusa da Umman Khaleel.
   Sarving d'in kowa tayi sannan suka fara karyawa,abin karin take ci amma hankalinta na kanshi sai kallon shi take yi,kusa da kunnenta ya matso yana cewa "yadai an mata"yafada tare da dage mata gira,murmushin da bata shirya yi ba ya subuce mata,yadda ya dage giran yasata sakin murmushi itama cikin rad'a take cemasa"uwar y'an mata dai tana kashe masa ido daya"murmushi shima yayi yace"eh hakane kuma,to ya akayi naga sai kallona kike kona chanza miki ne?"
"sosaima kuwa jina ke kamar ace yau kar ka tafi kasuwa katsaya nayi ta kallanka har sai nagaji banason ka fita wasu su ganka"
"hhh kice kishin ya motsa"
"dolene ai in dai akan ka ne"
murmushi yayi ya cigaba breakfast dinsa domin yasan muddin ya biye mata tabbas zata hanasa zuwa kasuwa yau.
       Bayan sun kare karyawar ne ya mike yana cema su Khaleel............................................✍️✍️✍️

    *Zeesardaunerh ce*

          ( ~Y'ar karamar su babbar~ ~su~👧🥰🤩)

# _comment_
# _like_
# _share_

*comment and vote dinku* *shike* *karamin karfin guiwar* *typing* 💋

WASU MATAN✔Where stories live. Discover now