Page 57&58

142 17 4
                                        

👩‍👩‍👧‍👧 WASU MATAN 👩‍👩‍👧‍👧
          @2021

~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤

Story and Writting
           by
Zainab Sardaunerh

🔔📚
JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
             
          ⚜️©J.A.W📚

بسم الله الرحمن الرحيم
Da sunan Allah mai rahama mai jinkai

Ya ALLAH YADDA NAFARA WANNAN LITTAFIN LAFIYA KA YARDA NA KAMMALA SHI CIKIN KOSHIN LAFIYA.

SADAUKARWA

WANNAN LITTAFIN SADAUKARWA NE GA FADILA SANI BAKORI,HAFSAT ZUBAIRU SAMBO(Autar mama)AMINA MUHAMMAD BASO, MUMMYN SHUKURA,ASIYA MUHAMMAD,MAMAN AMATULLAH,MAMAN NUSAIBA,RAHMA KOISE,SISTER MIE AND HABIBTY NASMAH LOVE U ALL GUYS♥️♥️♥️

GODIYA

GODIYA MARA MISALI GA PHARTY BB,UMMU MAHIR,MOM ISLAM,UMMU ABDALLAH DA KUMA DAUKACIN MEMBERS NA JARUMAI WRITTER'S ASSOCIATION,MY DEAREST FAN'S SON SO FISSABILILLAH💓💓💓

BOOK 2
  Page 57&58

Wani sanyi ne ya ratsa zuciyarta ganin cewa ba wanda ya fahimci cewa itace a jikin photon,kwanciya ta sake yi tana sauke a jiyar zuciya a hankali,tunani take idan baffanta ya ga waɗannan hotunan ya zai ji kuma wane tunani zai yi a kanta gaskiya ko wanene ya ɗauki wannan hoton bai mata adalci ba,tana cikin wannan tunanin har bacci ɓarawo ya saceta.

****************

kallon wayar take yi yayin da take ganin kamar mafarki ba gaskiya ba,dariya ta yi tana kara kallon wayar, kira ta dannawa Jauhar da yah Amar.

"anya lafiyar qalau kuwa baby?wannan kiran haka cikin talatainin ɗare"

"abunda zance kenan ya Amar ka rigani,go to the point nasan ba zakiyi kiran banza ba"

"kwarai kuwa ƴar ƙanwata ashe kina ganewa"

"kinsan kwakwalwarmu iri ɗaya ce taya ba zan gane ba, sannan kuma ni yayarki ce ba ƙanwar ki ba"

"sai shegen son girma kamar dawo"

"naɗaiji, idan bazaki faɗi dalilin kiran ba Allah zan kashe wayata nayi kwanciyata"

"ku shiga group na tura wani abu ku duba ku gani"

"minene ?"

"ku shiga kawai yah Amar zaku ganewa idanuwanku"

"pics ɗin yaya lion kawai na gani fa"

"eh sune na tura,ku duba da kyau shi da wacece a jikin hoton"

"ke mana "

"Allah jauhar na ci gidanku,gabaɗaya ke bakya ganewa,can't you see yadda ake kallon love sannan kice ni ce"

" idan bake bace to wacece? "

"sabuwar budurwarsa mana"

"budurwa kuma?"

"kwarai kuwa yah Amar"

"yaushe yayana yayi budurwa kuma?"

"ohon masa,ki tambayesa mana, ba yana nan part ɗinsa ba"

" eh yana nan, da hankalina bazan yi abunda zai zamemin matsala ba amma ke a ina kika samu waɗannan pics"

WASU MATAN✔Stories to obsess over. Discover now