page 53&54

244 29 3
                                        

👩‍👩‍👧‍👧 *WASU MATAN*  👩‍👩‍👧‍👧
          @2021

~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤

*Story and Writting*
           by
*Zainab Sardaunerh*

🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
             
          *⚜️©J.A.W📚🖌️*

Page 53~~54

WANE NE KABEER.............

      Alhaji Sa'id Ibrahim Shine mahaifinsa sai Hajiya Aisha Mahaifiyarsa hausa fulani ne su, wurno local goverment channe kauyensu;achan Alhaji Said ya yi primary da secondry d'insa bayan result dinsa ya fito kuma ya yi kyau sosai sai kanen mahaifinsa Abba Lurwanu dake aiki anan birni yasa ma masa Admission a *Sokoto State University* inda ya karanci pharmacy. Ya nada abukkai da dama wad'anda suke karatu a tare wata rana suka tafi gidan abokinsa Bashar shida sauran abokanan su achan ne yaga kanwarsa Aisha.
     Tun ranar da ya dora idanunsa kan Aisha yaji yana sonta so mai zafi gashi ya rasa hanyar da zai sake zuwa gidan,ana cikin haka bashar ya yi rashin lafiya har ta kai saida aka kwantar dashi Asibiti.Ciwo ba d'adi domin Said baiji d'adin rashin lafiyar abokinsa ba amma kuma sai wannan rashin lafiyar tazama alkhairi ta wannan hanyar yasamu ya kulla soyayya da Aisha,kullum yana Asibiti da sunan jinya yana soye wa da sahibarsa.

   maganar soyayyar su tayi nisa har manya suka shigo ciki ya yin da Abba Lurwanu ya wakilci mahaifin Said wato Alhaji Ibrahim inda aka tsaida magana kan cewa in ta kammala jarabawar SSCE sai ayi auren.
       Cikin ikon Allah takammala jarabawa lafiya akasha buki inda aka kai amaryar anan shiyar da kanen mahaifinsa ya tsaya masa gida a Runjin sambo.

   Kabeer shine d'ansu na farko sai Fatima da Batul twins tun daga haka Allah bai kara basu haihuwa ba yanzu haka Batul da Fatima suna rubuta WAEC da NECO ne ya yinda kabeer ya yi karatun Pharmacy kamar mahaifinsa inda ya cigaba da kula masa da chemist dinsa kuma yana karatun computer.

     Kabeer yana soyayya da wata yarinya a nan shiyarsu mai suna Asma'u suna matukar son junansu sosai har iyayen Kabeer sun san da maganar itama Asma'u gidansu sun san da maganar  ana batun kai sadaki gidan su Asma'u rana tsaka kabeer ya haukace musu cikin gida shi baya sonta akwai wacce yake so tun iyayen sa na daukar abun wasa har suka sawa sarautar Allah ido domin har gida kabeer yaje ya yiwa Asma'u cin mutunci kuma yace mata baya sonta ya tsaneta a take a wurin Asma'u ta sume amma ko ajikinsa.An kai ruwa rana kan wannan batun domin mahaifansa sun dau zafi kan abunda ya yiwa yarinyar mutane kafin aka zauna tsakanin iyayensa da na Asma'u da shi da kuma Asma'u ya kara tabbatar musu baya sonta kuma ko andaura sai ya saketa domin iyayensa cewa sukayi aure ba fashi.

      cikin kuka Asma'u ke tambayarsa mi tayi masa ya yi mata haka mi yasa ya yaudari zuciyarta sai da ta ba kowa tausayi amma shi ko ajikinshi,taci gaba da tambayarshi wacce yake so mi ta fita dashi ?yace bata fiki da komi ba kinma santa bakowa bace face kawarki *Maryama* cikin razana da kaduwa tace,

"maryam.."

bata ida ba a wurin ta suma saida aka yayyafa mata ruwa ta farfado maganganu take tayi tanal cewa mahaifin Kabeer Abba na hakura da shi in nice baya so amma don Allah ku ceci rayuwarsa kar ku aura masa maryama Wallahi ba yarinyar kwarai bace zata raba ku da danku ko a yanzu na san ba cikin hankalinsa yake ba da bazai min haka ba Abba duk tabi ta rikice dakyar mamanta taja ta yi daki da ita domin itama da ganinta kasan ba a hayyacinta take ba tana cewa,

"haba dama biri ya yi kama da mutum ni tunda naga Maryama ta like min mama nace miki ba alkharine tazo dashi ba ki kace na       kyaleta kila ta chanza kinga abun tayi min ko mama"

ta fada tana rushewa da kuka ta ci gaba da cewa,

"kingani ko mama Kabeer ba'a hayyacinsa yake ba akwai abunda tayi masa nasan kabeer bazaimin haka ba yana sona sosai don Allah mama ku karya Asirin da ta masa kinji mamana"

sai da aka bata maganin kwana sannan bacci ya dauketa tana yi tana kiran kabeer acikin mafarkinta.

Bayan su Asma'u sun fita Abban Asma'u ya ba baban Kabeer hakuri amma tunda kabeer yace ba yason Asma'u don haka bazai bada diyarsa ga wanda baya sonta ba don Allah su yi hakuri su barshi ya aure wacce ya ke so.

Haka iyayen Kabeer suka koma batare da jindain hana su auren Asma'u da akayi ba musamman Ummu Aisha mahaifiyar Kabeer domin ko wace mace tana burin samun suruka kamar Asma'u.

Kalaman Asma'u na nan cikin kan Ummu ya yin da Abba ya dauke su shirme kuma ya yi bincike kan Maryama mahaifinta ba ya da matsala sai dai mahaifiyarta ce mai matsala sannan ko yarinyar ance bata da mutunci shiyasa ya watsar da zancen Kabeer na son aurenta ya yin da Umma ke yiwa d'anta addu'a amma kamar ta azzara abun ake domin ko wace safiya son Maryama kara hauhawa yake a zuciyarsa ya yin da ko da yaushe yana gidansu Maryama.

     Abunda Allah ya kaddara ba fashi domin dakyar akai auren Kabeer da Maryama ba tare da danginsa na so ba sai don babu yadda zasu yi Alokacin.

   Bayan aure suka dawo tunanin ya akayi suka yarda da wannan auren bayan sun san halin yarinyar dana mahaifiyarta amma ba amsa domin sun kasa tunawa.

    Abu ya zame musu goma da ashirin domin maryama ta mallake musu d'a ya yin da ya manta da Ahalinsa ba ya zuwa inda suke kuma ko sy Batul suka je chan sai Maryama tayi musu wulakanci yana gani bazai tanka ba in suka maida martani idan ta zagesu yakmasu ya jibga son ranshi shiyasa suka daina zuwa gidansa.Haihuwar maryama daya inda ta samu d'a namiji  suka samai suna Maleek yana chan gun mahaifiyar Maryama ita ke kula da shi baisan kakarsa ta uba ba domin bata bari akaishi chan.

  Abu guda ke gama Kabeer da maryama shine kazamta kwata-kwata ba tada tsafta bata iya gyara  dakinta bare ta gyara masa nasa gashi bata sallah sai ta ga dama ga shegen karatun littafan hausa ya yin da in ta rika waya dakyar take dagawa ko da yaushe abu dayane karatun littafi bata gajiya.Alokacin da taga ta mallaki Kabeer ko gardama ba ya iya yi mata duk abunda tace shikenan sai ta sakankance da banka masa Asirin da take.

    Addu'a bata faduwa kasa banza ko sau daya Ummu bata taba gajiya da yiwa d'anta Addu'a ba haka ma Abba domin y yardashima cewa Kabeer ba'a hayyacinsa yake ba,Batul,fatima da kuma Asma'u wacce har yanzu bata yi aure ba karaunta ta cigaba da yi suma ko da yaushe suna yi masa Addu'a domin duk da Kabeer bai auri Asma'u ba hakan bai hanata yin zumunci da su Umma ba hakama Mahaifiyarta da Ummu sun zama ka'waye.
    Wata rana Asma'u tazo ziyara nan inda Ummu sai ga Kabeer ya shigo lokacin dai anfara samun sauki yakan zo wani lokacin batare da sanin Maryama ba domin ba ya son bacin ranta suka gamu da Asma'u a dakin Ummu ta gaidashi ya amsa har yana tambayar wacece ita.Abun ya basu mamaki sosai sun dauka raina musu hankali yake sai daga baya suka fahimci cewa gabadaya ya manta da Asma'u,ya manta ya taba yin soyayya da ita bazai iya tuna ta ba.

   Haka rayuwa ta cigaba da tafiya har izuwa yanzun da yadawo cikin hayyacinsa kaso sittin  cikin dari.

    Inna Dije takasance kanwa ga Alhji Sa'id.
      Abba Lurwanu shine mahaifinta itace yarsa ta farko mijinta ya rasu bata da d'a ko guda, gabadaya mahaifiyarsu bata koya musu son dangin mahaifinsu ba bata kaunar Sa'id tun yana gidansu mahaifiyarsu tace musu gani take cinye musu dukiyar mahaifi zai yi, amma yanzu da taga Allah ya masa bud'i tazo gidan ta tare tunda bata da aure shikuma Alhji Said bazai iya korarta ba domin mahaifinta ya gama masa komai a rayuwa.
     Da taimakonta Maryama ke aikata wasu abubuwa na asirce Kabeer.

  WACE CE MARYAMA........🖊️🖊️🖊️

     Zeesardaunerh ce

          ( ~Y'ar karamar su babbar~ ~su~👧🥰🤩)

# _comment_
# _like_
# _share_

comment and vote d'inku shike Karamin kafin guiwar typing💋

WASU MATAN✔Stories to obsess over. Discover now