Page 49&50

183 16 4
                                        

👩‍👩‍👧‍👧 WASU MATAN 👩‍👩‍👧‍👧
@2022

~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤

Story and Writting
by
Zainab Sardaunerh

🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

⚜️©J.A.W📚🖌️

بسم الله الرحمن الرحيم
Da sunan Allah mai rahama mai jinkai

Ya ALLAH YADDA NAFARA WANNAN LITTAFIN LAFIYA KA YARDA NA KAMMALA SHI CIKIN KOSHIN LAFIYA.

SADAUKARWA

WANNAN LITTAFIN SADAUKARWA NE GA FADILA SANI BAKORI,HAFSAT ZUBAIRU SAMBO(Autar mama)AMINA MUHAMMAD BASO, MUMMYN SHUKURA,ASIYA MUHAMMAD,MAMAN AMATULLAH,MAMAN NUSAIBA,RAHMA KOISE,SISTER MIE AND HABIBTY NASMAH LOVE U ALL GUYS♥️♥️♥️

GODIYA

GODIYA MARA MISALI GA PHARTY BB,UMMU MAHIR,MOM ISLAM,UMMU ABDALLAH DA KUMA DAUKACIN MEMBERS NA JARUMAI WRITTER'S ASSOCIATION,MY DEAREST FAN'S SON SO FISSABILILLAH💓💓💓

BOOK 2
  Page 49&50

BAFFA

"ina mai matukar baku hakuri a bisa hukuncin da na yanke ba tare da na yi shawara ko na tuntubè ra'ayinku ba,ban dáuka tafiyar ta su ta kasance a yau ba,nasan na yi magana da Muktar a lokacin da ya samu labarin abubuwan da suka faru tun ranar dàurin auren har izuwa kwanciyar mai mamana Asibiti,ya nuna bácin ransa sosai sannan ya roki alfarma a kàro na biyu da na bashi ita yaje da ita Abuja ta zauna a gurinsa na wani lokaci ko zata manta da abubuwan da suka faru,duk mun san abunda likitoci suka ce dangane da damuwa da tayi mata yawa har hakan ya janyo mata ciwon zuciya wanda idan ba'a dâuki mataki ba za'a iya rasa rayuwar ta baki daya ni kaina da farko ban amince masa ba amma da ya matsa kuma na yi tunani tare da nazari sai na amince masa,har ga Allah yau ko gobe na yi niyar yin wannan maganar da ku domin na fitar muku da hakkin ku amma kuma sai gashi ya kirani jiya tsakiyar dare yana fadamin cewa da safe zai biyo ya dàuki mamana a ranar zai wuce,ko kadàn ban yi tunanin kin samun goyon baya daga gare ku ba shiyasa nace masa ba damuwa sai ya zo,ko kad'an ban kawo a raina cewa zaku yi tunanin tafiya da ita wajenku ba"

Mama Yelwa tace
"bakomi Yusuf Allah ya sa hakan shine Alkhairi"
suka amsa da"Ameen"

Dadda tace "Allah ya sa tafiyar itace mafi alkhairi a rayuwar jikata"

"Ameen ya Allah Dadda"

Duban Kareema Baffa ya yi yace " kinyi shiru Kareema baki ce komi ba"

"mai afkuwa ta afku ba abunda zance yaya fa ce Allah ya bata hakurin zama a gurin da bata sani ba,ya sa hakan shine mafi alkhairi a rayuwar ta"

"Ameen ya hayyu ya qayyum"

Inna Saude da ke lab'e ta dubi Baffa da sauran mutanen dake cikin d'akin a zuciyar ta ce wato ni ce báre ni ce ba'a bukatar na ce wani abu shiyasa ba za'a gayyace ni ba ya yi kyau ta yi kwafa sai na ga wanda ya isa ya hanani magana ni da bakina,kamar wacca aka hankado ta fadá cikin dákin tana cewa "na ce ba"
Muryarta ta ratsa kunnuwan kowa dake gurin suka ji yo suna kallonta ba wanda ya ga shigowarta a cikin su.

"duk da cewa nasan ba'a bukatar maganata a wannan wurin sannan kuma ba'a gayyace ni ba amma zan maganta, ban sani ba maganar ta wa ta yi muku dad'i ko a'a ! wannan bai damu Saude ba,na ji kuna cewa likata yace damuwa ta yi wa mai tsada yawa nima kuma nasan da wannan bayanin na likita amma kuma mai yasa bakwa nazari kafin yanke hukunci? burin ku kawai ku aikata zai bàta raina,yanzu ku a naku tunanin nisanta Aleeya daga gareku shine zai warkar da damuwar ta? ko kuma kuna tunanin d'auketa daga wujina shine zai yaye damuwa da ciyon da zuciyarta ke d'auke da shi?ko kuma kuna tunanin zamanta da ni ne ya janyo mata hakan? don kawai kuna son rabani da ita shine zaku dàuke ta ku kai ta uwa duniya har Abuja! gurin da babu uwa ko ubanta a chan,ba ķanne ko ýan uwa sannan kuce lafiya ku ke mata fatan samu? wallahi ku sani sam wannan shawarar ko na ce hukuncin na ku bai yi ba, ba abunda ya shafi saude idan lamarinku ya kwabe amma ina ji muku tsoron gurin samun lafiyar ta ku aikata kuskuren da za ku dawo da na sani daga baya domin kàdaici kàdai idan ya yi mata yawa zai iya sa zuciyarta bugawa..."

WASU MATAN✔Stories to obsess over. Discover now