page 55&56

209 24 0
                                        

👩‍👩‍👧‍👧 *WASU MATAN*  👩‍👩‍👧‍👧
          @2021

~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤

*Story and Writting*
           by
*Zainab Sardaunerh*

🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
             
          *⚜️©J.A.W📚🖌️*

*Page* 55~~56

WACE CE MARYAMA...........

Maryama ta kasance y'a ta farko ga Alhji Umar Abba da hajiya Hawwa'u.Alhji Umar Abba ya yi tashen kud'i a shekarun da suka gabata amma ko yanzu Alhmdllh za'ace.
Hajiya Hawwa itace uwar gidansa kuma amaryarsa domin ta kasa ta tsare ba wacce ta isa ta shigo gidanta a matsayin matar Alhji Umar.

     Y'ay'an ta biyu kuma mata,Maryama da Nafeesat.
Tana matukar son Maryama domin itace y'arta ta farko kuma ta jima kafin ta samu cikin Maryama shiysa duk abunda Maryama ke so shi ake mata a gidan.

  Duk halin hajiya Hawwa Maryama ta kwashe har ta zarta domin ita hajiya Hawwa tana saka kissa a lamarinta saɓanin Maryama da komi nata direct ne,

Shiyasa Hajiya Hawwa ko a dangin mijinta bata samun matsala,tana sa Alhji Umar ya bada kuɗaɗe da sunan danginsa zata bawa amma sai ta raba su biyu ta rike rabi ta basu rabi su kuma suyi ta farin ciki suna samata albarka.

Aganinsu Alhaji Umar ya yi dacen mata ta gari wacce bata damu da da dukiyarsa ba mai sonsa don Allah ga kyauta.

Ko bukata wani keda ita a familyn Alhji Umar ita ke masa hanya,duk tabi ta saye zuciyar su.

Idan lalura ta tashi familynsa zata yi abubuwa dadama ya yinda a zahiri zata nuna da kuɗin ta tayi komi amma a baɗini shi ya bada kuɗin tabasu.

Cikin matacce Allah ke fitar da rayayye hakanne ya kasance ga Nafeesat domin sam bata yo halin uwarta da yayarta ba.Mafi yawan lokaci tafi zama inda kakarsu Balqeesu mahaifiyar Alhji Umar Abba,hakan ya saka dangin mahaifinta kaunarta sosai saboda kyawawan halayenta ba kamar Maryama ba.

Asma'u da Maryama ƙawaye a makaranta amma sukan samu saɓani saboda banbancin halayya, musamman Maryama da  tarbiyyar kwarai bata isheta ba ko a makaranta bata da aiki sai soyayya da malamai kala-kala.

Ko sun samu saɓani da exam ta matso Maryam zata fara neman shiri domin Asma'u na cikin hazikan dalibai na wannan lokacin.

Tun lokacin da Maryama ta ɗaura idanun ta akan Kabeer taji zuciyarta ta halba sai da ta dafe saitin zuciyarta,a lokacin suna tare da Ummanta sun biyo layin.

Taji a duniya ba wanda take so kamar sa.!domin son sa ya yi mata mugun kamu.

Ta rasa ya zatayi gashi sunyi kusan wata takwas basa magana da Asma'u ga exam ta yo kusa ga kuma soyayyar saurayin da batama san sunansa ba.

Shiyasa Maryama ta shirya taje gidansu Asma'u ta nemi sulhu dakyar ta sauko sai da momyn Asma'u ta tasa baki sannan, amma sam zuciyarta bata yarda da kalaman Maryama ba duk da cewa tasan lokacin exam ya yi kusa.

Ko a makaranta Maryama bata da aiki sai yiwa Asma'u firar Kabeer tana cewa tayi dacen saurayi amma Asma'u bata kawo komi a ranta ba.

 
    Duk yadda Maryama zatayi taga tasamu shiga wurin Kabeer tayi amma babu nasara.

Duk ta bi ta fige kan soyayyar saurayin kawarta.

Bata kara fita hayyacin ta ba sai da Asma'u ta fada mata cewa za'a yanka mata sadaqi, suma ne kawai bata yi ba a wannan lokacin.

Ai ko tana dawowa gida ta haukacewa hajiya Hawwa tana cewa,

"Wlh Ummah kin ji na rantse muddin kika bari na rasa Kabeer nima zaku rasani har abadan abada, domin zan kashe kaina"

Ba shirin Hajiya Hawwa ta kira kawarta Binta suka garzaya wurin boka,suka sa ya yi musu aikin da Kabeer yaji lokaci guda a duniya ba wacce yake so sai Maryama.

Itace ta saka shi yana yiwa Asma'u wulakanci yana jaddada mata cewa baya sonta baya ƙaunarta har hakan ya saka aka yi zama tsakanin mahaifan Kabeer dana Asma'u.

    Wannan zaman da akayi ya saka mahaifan Kabeer fushi dashi sosai har ya so ya tada hankalinsa kan fushinsu amma sai Maryama ta ɗinga kwantar masa da hankali ta cewa zasu sauko ne ai,ya yin da take banka masa magungunan asiri cikin abincin da take kawo masa in yazo fira.

A lokacin da Asma'u ke jinyar zuciyarta alokacin kuma Maryama ke shan soyayyar ta.


*************

Lokaci yaja yini ya tafi ya koma kwanaki,kwanaki sun koma satuttuka, satuttuka sun koma watanni, watanni na kokarin zama shekara amma iyayen Kabeer sunki yarda da aurensu shiyasa suma tasa Ummanta ta kai su wurin boka akayi aikin akansu kuma tasa akayi aikin da Kabeer ya manta da wata Asma'u a wannan duniyar.

Aure ya ɗauru da taimakon dije wacce Maryama ta bata kuɗi ta saka ma mahaifan Kabeer magani a abincin su suka ci.

Amma maganin bai jima ba ya warware aka barsu ta tunanin ya hakan ya faru.Ba haka Maryama ta so ba amma tun da ta samu muradin ranta sai ta share su.

Rayuwar auren Kabeer da Maryama ba acewa komi domin Maryama ta zamo miji shi kuma Kabeer mata,sai yadda tayi dashi, ga Maryama da shegen son jiki da ƙazamta.Aikin gida Kabeer keyi ta rabashi da danginsa har Allah ya azurtata da ɗansu Maleek.

Ko Maleek bata bari yasan dangin Mahaifinsa ba a cewar ta baya da bukatar hakan kuma idan su Batul da Fatima suka so gidan ta dinga yi musu abubuwa kala_kala idan suka rama tasa Kabeer ya korasu wani lokacin har da duka.

Ko Maleek kan sun jikinta wurin mahaifiyarta ta mai dashi.

************

A lokacin da Maryama ta sakankance cewa ta mallake Kabeer sai yadda tayi dashi,alokacin kuma addu'ar iyaye da y'an uwa Allah ya amsa domin Addu'ar iyaye bata faduwa kasa sai gashi Kabeer ya dawo hayyacin sa;asirin Maryama ya fara warware wa.

Hakan ya ba Maryama mamaki da tsoro har sai da ta sake sa mahaifiyarta ta koma wurin boka ta karbo mata magani.

Amma a yanzu ta kudurta a ranta cewa ba zaɓi daya da zata ɗauka cikin zaɓin da mahaifiyarta ta bata domin sai ta gasawa Kabeer aya a hannu.

Dole ta nunawa Kabeer ai nahin halinta dole ne yasan WACE CE MARYAMA ,ta shirya rashin mutunci kala_kala da zata yi masa domin rashin lafiyar da tayi akansa baza ta tafi a banza ba(🤔😱hajiyar Maryama mrs Kabeer Allah taimaka 🤣😂)

_CIGABAN LABARIN_

    Zeesardaunerh ce

          ( Y'ar karamar su babbarsu👧🥰🤩)

# _comment_
# _like_
# _share_

comment and vote d'inku shike Karamin kafin guiwar typing💋

WASU MATAN✔Stories to obsess over. Discover now