👩👩👧👧 WASU MATAN 👩👩👧👧
@2022~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
Story and Writting
by
Zainab Sardaunerh🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
⚜️©J.A.W📚🖌️بسم الله الرحمن الرحيم
Da sunan Allah mai rahama mai jinkaiYa ALLAH YADDA NAFARA WANNAN LITTAFIN LAFIYA KA YARDA NA KAMMALA SHI CIKIN KOSHIN LAFIYA.
SADAUKARWA
WANNAN LITTAFIN SADAUKARWA NE GA FADILA SANI BAKORI,HAFSAT ZUBAIRU SAMBO(Autar mama)AMINA MUHAMMAD BASO, MUMMYN SHUKURA,ASIYA MUHAMMAD,MAMAN AMATULLAH,MAMAN NUSAIBA,RAHMA KOISE,SISTER MIE AND HABIBTY NASMAH LOVE U ALL GUYS♥️♥️♥️
GODIYA
GODIYA MARA MISALI GA PHARTY BB,UMMU MAHIR,MOM ISLAM,UMMU ABDALLAH DA KUMA DAUKACIN MEMBERS NA JARUMAI WRITTER'S ASSOCIATION,MY DEAREST FAN'S SON SO FISSABILILLAH💓💓💓
BOOK 2
Page 1&2Iya kokari Dr Mu'azu yayi amma ba alamar farfadowar Kabeer,hakuri ya ba su Umma da Abokan ango yana sanar musu cewa dole sai ankai Kabeer Asibiti fa domin lamarin yafi karfinsa.
Kwalla ne suka cika idunuwan Umma amma bata basu damar kwaranyowa ba tace wa su Mahmud su sakasa cikin mota a wuce Asibiti dashi .
Yayar Ummu ce ta shiga gaban mota yayin da Mahmud dake rungume da kabir suke a baya sai dayan abokinsu mai suna Mubarak da ke tuka motar, sauran kuma suka shiga cikin motocinsu aka dunguma izuwa SARAKI HOSPITAL domin channe kadai baza su sha wahalar bin layi ba.
Cikin gaggawa aka karbesu aka cigaba da bawa kabeer taimakon gaggawa.
Achan gidan su Kabeer kuwa hankalin kowa ya tashi yan uwa Abban Kabeer da na Ummun Duka,ya yin da suke cike da alhini ana maida yadda akayi, kowa yaji ciwon wannan abun baka dan ba yayin da wasu daga cikin yan uwa suke hasashen anya Maryama tabar Kabeer hakanan kuwa domin tabbas wannan abun da d'aure kai yake,sanin kansu ne yarinyar da mahaifiyarta muggan shu'umammu ne duba da yadda auren ma nasu ya kasance ita da Kabeer.
Wata daga cikin kannen Abban Kabeer ke cewa aiko wannan auren babu fashi domin sunga yarinya kuma ta musu aure sai an daurashi ko da kuwa duka ahalin Maryama bokaye ne to wallahi Kabeer sai yayi aure bari ya farfado, don taga an zuba mata ido shine take son wuce gona da iri wannan abun da Kabeeru ya aikata da me yayi kama yanzu wane hali yarinyar da ahalinta ke ciki?
Ummu gaba daya bata cikin nutsuwarta gashi ta kira Abban Kabeer yaki daukar waya tarasa wani tunani zatayi ga halin da d'anta tilo ya ke ciki gashi batasan wanne hali Mijinta ke ciki ba da wanne zataji da fasa auren da Kabber yayi ko ko da halin yarinyar mutane zata shiga ko kuma da halin da Kabeer yake ciki gabaya kanta ya kulle.
Su Batul suna gidan wata Amarya makwafciyar su suna shiryawa because gidan nasu ya cika Allah Allah kawai suke su kammala shirinsu kafin ango yazo su poster hotuna amma murnarsu ta koma ciki,bakin ciki ya mamaye farincikinsu a yayin da suka shigo gidansu suka riske labarin abun da ke faruwa,ina zasu nufa?Asibiti ko wurin Agla?wanne hali take ciki? babu mai basu amsa
Inna Dije kan farinciki ko lekowa waje batayi ba ita da mahaifiyarta kamar su zuba ruwa a kasa su sha,ita gaba daya bata bukatar farincikin alhalin wannan gidan idan zata gansu a damuwa to shine farincikinta(Allah ya rabamu da hassada ameen)
INNA SAUDE
Asibitin Specialist aka wuce da Inna Saude da sauri nurses suka karbesu duba da irin shigar da ke a jikinsu ga sauran ma jinyata nan a zaune wasu ma sunfi awa daya kasancewar asibitin Specialist ta gwanati ce shiyasa Nurse suke yin rashin mutuncinsu yadda suke so muggan yan wulakanci ne na bugawa a jarida .
Mama Kareema ce da Inna Laure wacce tayi dagwas cikin Atamfar da Inna Saude ta b'ata tayi fitar buki sai kuma Anty Amrah tare da mijinta wanda shine ya tuko motar.
Bayan an bawa Inna Saude gado aka kara mata ruwa domin bata da isassun ruwan jiki,sai da aka saka mata gorar ruwa biyu .
Likita ya yiwa Mama Kareema baya ni cewa Inshaallah nan da awa guda ko biyu zata farfado jininta ne ya hau sosai Allah ya taimaketa irin wannan faduwar ita ke haifar da cutar barin jiki wato paralyse,Magani ya rubuta ya mika mata takarda.
A kage Mama Kareema ta fito da Asibitin aka bar Inna laure kafin Inna Saude ta farfado domin Anty Amrah ta dage sai tabi Mama Kareema gida,gaba daya hankalin Mama kareema ba'a kwance yake ba tana tunanin wani yanayi Agla zata shiga idan ta samu wannan mummunan labarin ga kuma yay'an ta wane hali yake a ciki.Darajar daraja Inna Saude taci har ta kawo ta asibiti da badon hakan ba da ba dalilin da zayasa tazo asibiti cikin wannan halin da ake ciki gashi gidan buki duk ya harmutse,tunanin Aleeya shine ke dagawa Anty Amrah hankali itama shiyasa taki tsayawa tace zata koma gida Allah yasan tanason Aleeya har cikin ziciyarta, Yaya Umar ne ya tuka motar ya maida su gida.
INNA LAURE
Tarasa wane kalar farinciki zatayi ji take kamar tayi ihu don murna cikin ma an tauye farincikinta kasan cewar ta tare da su Mama Kareema amma tabbas ji take a yau tafi kowa farinciki a duniya tabass aiki boka na kan tudu yayi domin taga alama,bayan fitar su mama Kareema itama fita tayi daga Asibitin taje chan nesa kadan da Asibitin ta rinka kyalkyalar dariya kamar wata zautatta.
ANWAR
Tun cikin daren yake kukan rasa sahibarsa domin karma yaje wurin daurin Auren ya kashe wayarsa ya kama daki a IBRO HOTEL sakamakon gidansu ya cika da baki,Abokanansa ko daya bai gayyata ba domim sun san Aleeya a photo sun san yadda yake matukar sonta.
Yana ji a ransa tabbas a wannan duniyar da wuya yayi aure domin bazai iya bawa wata yarinya gurbin Beauty(Agla) a zuciyarsa ba tabbas yasan yayi rashi wanda har abada zuciyar sa bazata dena jin ciwon hakan ba she loves her more than yadda mai hasashe zai hasaso.Misalin 12:00am ya yi wanka ya shirya amma idanunsa sunyi ja kamar garwashi,tabbas yasan i zuwa wannan lokacin ya rasata har abada,yasan kuma hukunci tsayawa tinaninta da zai amma zai yi iya kokarinsa ya hana zuciyarshi tuna fuskarta da kyakkyawar fuskarta,zai kasance cikin yima ta addua'r zaman lafiya a gidan mijinta duk da kasancewar hakan zai matukar illatar da zuciyarsa,ruhinsa da kuma gangar jikinsa.
Wayarsa ya kunna tare da fitowa daga room dinsa ya mikawa ma'aikatan key din dakin ya fito harabar hotel din yana tunanin yadda zai samu abun hawa a yanzu,wani cousin dinsa ya kira Allah ya taimakesa yana kusa domin ba nisa tsakanin IBRO HOTEL da kuma RUNJIN SANBO.
Sakonnin da aka turo masa ya fara dubawa kafin isowar Ibrahim,sakon mama Kareema ne asama kafin na Ramlat wacce tayi amfani da wata waya ta tura masa.
Sakon Ramlat ya fara karatawa domin ya san mama Kareema fadan ne zata mass game da rashin zuwa gurin daurin auren da yayi.
yadda yayi tunani ba hakan ya kasance ba aduk tunaninsa Ramlat zata gaya masa kalma mafi daci a rayuwarsa cewar andaura auren Aleeya wanda ya dade da sanarwa zuciyarsa hakan but sai idanunsa suka ganar masa abunda kwakwalwarsa ta kasa yarda..Wayyo Yah Anwar kana ina AN FASA AUREN ADDA AGLA
ya maimaita sau ba adadi amma kuma ya kasa yarda, sakon Mama Kareema ya duba in da take cewa ...
Ako ina kake ka gaggautawa dawowa gida ina nemanka
Tabbas akwai matsala,akwai abunda ke faruwa a gida ga kuma sakon Salmat wanda ya kasa yarda dashi ammakuma ya tsaya a kahon zuciyarsa.
Maimakon nan Runjin Sambo da yayi niyar wucewa sai ya fasa direct ya nufi MABERA domin yasan achanne zai iske Mama Kareema sannan yasan gaskiyar wannan lamarin.
Show me love patronize my book Diyah❤️
Zeesardaunerh ce
(~ Y'ar karamar su babbar su~👧🥰🤩)
# comment
# like
# sharecomment and vote d'inku shike Karamin kafin guiwar typing💋
![](https://img.wattpad.com/cover/260818017-288-k618322.jpg)
YOU ARE READING
WASU MATAN✔
Historia Cortaبسم الله الرحمن الرحيم WASU MATAN Littafi ne da ya kunshi halayen matan mu na yanxu ko nace matan zamani,halaye masu kyau da ma akasin su. Wannan littafi ya kunshi Kishi,kiyayya,tausayi,dama sauran su. INA ROKON UB...