👩👩👧👧 WASU MATAN 👩👩👧👧
@2022~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
Story and Writting
by
Zainab Sardaunerh🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo⚜️©J.A.W📚🖌️
بسم الله الرحمن الرحيم
Da sunan Allah mai rahama mai jinkaiYa ALLAH YADDA NAFARA WANNAN LITTAFIN LAFIYA KA YARDA NA KAMMALA SHI CIKIN KOSHIN LAFIYA.
SADAUKARWA
WANNAN LITTAFIN SADAUKARWA NE GA FADILA SANI BAKORI,HAFSAT ZUBAIRU SAMBO(Autar mama)AMINA MUHAMMAD BASO, MUMMYN SHUKURA,ASIYA MUHAMMAD,MAMAN AMATULLAH,MAMAN NUSAIBA,RAHMA KOISE,SISTER MIE AND HABIBTY NASMAH LOVE U ALL GUYS♥️♥️♥️
GODIYA
GODIYA MARA MISALI GA PHARTY BB,UMMU MAHIR,MOM ISLAM,UMMU ABDALLAH DA KUMA DAUKACIN MEMBERS NA JARUMAI WRITTER'S ASSOCIATION,MY DEAREST FAN'S SON SO FISSABILILLAH💓💓💓
BOOK 2
Page 95&96Sai guraren Isha'i sannan Ummu ta farfaɗo sai motsi bakinta yake tana ambatar sunan Hamma Yusuf.
Likita ne ya fito daga ɗakin da aka kwantar da ita ya nufo su Dad dake tsaye cirko cirko a ward ɗin,kallonsu yayi ɗaya bayan ɗaya sannan yace "Waye Hamma Yusuf a cikin ku?" da hanzari Baffa ya nufo likitan yana cewa "Ni ne""Mara lafiyar tana bukatar ganinka"
Cikin sauri Alh Muhammad ya tare numfashin likitan yana cewa "Ta farfaɗo ne?"
"Eh to,but she didn't open her eyes,sunan Yusuf kawai take kira"
Wane sanyi ne ya ratsa zuciyar su mama Kareema,kiran sunan Yusuf da Haleema tayi hakan ya tabbatar musu da cewa ta dawo hayyacinta kuma ta tuna matsayinsu a gurinta,ta tuna rayuwar da suka gudanar a tare da ita "Alhmdulillah" shine abunda ko wannensu yake furtawa
Ajiyar zuciya su Ammy da Amna suka sauke,duk da cewar Ummiey bata buɗa idanuwanta ba amma ai tayi magana,hakan ke tabbatar musu tana cikin koshin lafiya.
Wani irin kallo Abbiey wato Alh Abbas yabi bayan Baffa dashi,duk da cewar ba aure tsakanin Baffa da Ummiey hakan kawai yake jin kishin Baffa,ko a labarin da aka bayar a ɗazu alamu sun nuna ba ƙaramin so Haleema ke yiwa Yusuf ba,kuma yasan matukar ta dawo hayyacinta zata tuna komi na rayuwarsu,sannan kuma soyayyarsa ba gogewa zata yi a zuciyarta ba.
Cikin room ɗin Baffa ya shiga tare da ƙarasawa kusa da gadon da take ya zube duka guiwowinsa a kasa,cikin murya mai rauni ya kira yi sunanta "Haleema!"
"Hamma Yusuf" ta faɗa tana buɗe idanuwanta a hankali har ta saukesu a fuskarsa.
Kallonsa take shima yana kallonta yayin da hawaye suka fara zuba a fuskarsa yana cewa"Kiyi hakuri Haleematu ki gafarceni,nasan nayi miki laifi dayawa don Allah kiyi hakuri,nayi danasani marar adadi Haleema,nayi kuka nayi addu'a,nasan cewa tabbas na yi matuƙar zaluntarki a rayuwar auren da mukayi kimin afuwa ki yafemin,banfahimci kusakuran da na aikata ba sai da na rasa ki Haleema,tsawon waɗannan shekarun ba safiyar Allah da zata waye ban tuna kyautatawar ki da hakurinki a gareni ba,Don Allah ba domin ni ba kimin afuwa ki yafemin"
YOU ARE READING
WASU MATAN✔
Historia Cortaبسم الله الرحمن الرحيم WASU MATAN Littafi ne da ya kunshi halayen matan mu na yanxu ko nace matan zamani,halaye masu kyau da ma akasin su. Wannan littafi ya kunshi Kishi,kiyayya,tausayi,dama sauran su. INA ROKON UB...