Page 61&62

114 19 9
                                    

👩‍👩‍👧‍👧 WASU MATAN 👩‍👩‍👧‍👧
@2022

~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤

Story and Writting
by
Zainab Sardaunerh

🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

⚜️©J.A.W📚🖌️

بسم الله الرحمن الرحيم
Da sunan Allah mai rahama mai jinkai

Ya ALLAH YADDA NAFARA WANNAN LITTAFIN LAFIYA KA YARDA NA KAMMALA SHI CIKIN KOSHIN LAFIYA.

SADAUKARWA

WANNAN LITTAFIN SADAUKARWA NE GA FADILA SANI BAKORI,HAFSAT ZUBAIRU SAMBO(Autar mama)AMINA MUHAMMAD BASO, MUMMYN SHUKURA,ASIYA MUHAMMAD,MAMAN AMATULLAH,MAMAN NUSAIBA,RAHMA KOISE,SISTER MIE AND HABIBTY NASMAH LOVE U ALL GUYS♥️♥️♥️

GODIYA

GODIYA MARA MISALI GA PHARTY BB,UMMU MAHIR,MOM ISLAM,UMMU ABDALLAH DA KUMA DAUKACIN MEMBERS NA JARUMAI WRITTER'S ASSOCIATION,MY DEAREST FAN'S SON SO FISSABILILLAH💓💓💓

BOOK 2
  Page 61&62

GIDAN SU ABBAN KHALIL

Rayuwar su suke cikin lumana da soyayya duk da  kasan cewar ko wannen su da damuwa a zuciyarsa.

Azeema na iya kokarinta na ganin cewa bata canja daga kyautatawar da takewa mijinta ba, a duk lokacin da shedan ya ziyarceta tare da nuna mata cewar yanzu Abban  Khaleel zai zama ba nata ita kaɗai ba dole za'a kira shi da mijin mata biyu takan shige ɗaki taci kukanta sannan ta kore shi da ayoyin ubangiji tsarkaka, tana kuma addu'ar Allah ya kareta da sharrin kishiya,ko wacece ya yi mata tsari ita da ƴaƴanta daga ita,duk kishiya kishiya ce amma ɓata fatan samun muguwar kishiya.

An yi ɗauki ba daɗi tsakanin Umma da Malam kan auren da take son Abubakar ya ƙara,malam yace sam ba wannan zancen ita kuma tace aure ba fashi,tunda har ya yi mata kishiya don haka bai isa ya hana a yiwa Azeema ba, "hausawa suka ce kyan ɗa ya gaji ubansa, yadda kayi mata biyu haka Abubakar zai yi su,dama ai babban burinka ne ɗanka ya gaɗe ka,wannan burin naka zan cika"

Abun ya koma rikici a giɗan Umma Hadiza ta hana kowa zaman lafiya karshe sai da abun ya kai gurin mahaifin Azeema,ɗakyar ya shawo kan yayansa ya yarje ayi auren amma ba hannunsa aciki,Umma Hadiza tace

"chan ta matse maka,dama ni bana son ka sanya hannunka a ciki, daɗa ga ka mai ƴa baza'a yi mata kishiya ba,nasan ni bana da iyayen ne da ka tashi kayi min ita,kaji yadda nawa iyayen suka ji,itama ƴar taji yadda naji a lokacin da uwarta ta kulla aurenka da wannan makirar matar ta cikin gidannan"

Har sakin Umma Hadiza Malam Usman yayi niyar yi domin bakaramin ɓata masa rai tayi ba gaban kanensa take masa waɗannan maganganun amma mahaifin Azeema ya ɗakatar dashi domin ba'a yanke hukunci cikin fushi.

"ba wai abun da Allah ya halatta nake son haramtawa ba Umar,yarinyar da takeson Abubakar ya aura ba mutuniyar kirki bace,na gani da idona kuma an gayamin samari kala-kala take tarawa,wani lokacin ma bata kwana a gida,ba mutum daya ba ansha an faɗamin an ganta a Abuja da mazaje daban_daban,a haka kake son na bari Abubakar ya aureta? idan tana da wata cutar ba iya Abubakar zata tsaya ba har Azeema sai ta shafa,idan shi Abubakar mahaifiyarsa ta ja masa ita Azeema fa,sai a cutar da rayuwarta?"

"maganganunka abun dubawa ne yaya amma ina mai rokon ka da ka tayasu da Addu'a kawai,ba abunda ya isa ya samu bawa face yana rubuce a zanen kaddararsa,idan har Allah ya kaddara faruwar wannan auren bamu isa mu dakatar da shi ba,kai da kanka kasha faɗamin kuma na karanta na gani Allah ba azzalumin kowa bane sannan baya son masu zalunci,ka fawwala Allah komi shine zai ba su kariya,matukar sun sarkake zuciyoyinsu Allah bazai bari su wulakanta ba,karka saka zancen mutane a ranka game da waccan yarinyar,kasan halin mutane ba kasafai suke faɗin khairin mutum ba,sanin cikakken halin mutum sai Allah,idan ma har tana da wata cutar zamu iya yin test a asibiti kafin auren domin kawar da shakku akan hakan duk da cewar hakan bazai kawar da abunda Allah ya kaddara ba,matukar ya kaddara kamuwar su da wata cuta ko ba yarinyar dole zasu kamu da ita,kasani yaya wani abun yana faru ne saboda yazama izna ko ishara ga wasu,watakil sanadiyar wannan auren Hadiza ta gyara halayenta,wannan auren yana yiwa yazama isharar da zata sauya rayuwarta"

WASU MATAN✔Where stories live. Discover now