Page 23&24

220 30 2
                                        

👩‍👩‍👧‍👧 *WASU MATAN*  👩‍👩‍👧‍👧
          @2021

~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤

*Story and Writting*
           by
*Zainab sardaunerh*
🎂🎂🎂🎉🎉🎊🎊🎂🎂🎂🎊🎊🎉🎉🎂🎂🎂🎊🎉🎉🎉🎊🎂🎂
*HAPPY 1 YEAR ANNIVERSIRY AL'UMMA WRITERS ASSOCIATION*
🎂🎂🎂🎉🎉🎉🎊🎊🎂🎂🎉🎉🎂🎂🎂🎉🎉🎉🎉🎂🎂🎂🎂🎉

بسم الله الرحمن الرحيم
         _________________      
       ______
🅙︎𝗮𝗿𝘂𝗺𝗮𝗶 🅦︎𝗿𝗶𝘁𝗲𝗿𝘀 🅐︎𝘀𝘀𝗼𝗰𝗶𝗮𝘁𝗲𝗱📚🖊
https://www.facebook.com/101679598253281/posts/101680068253234/?app=fbl
_Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa illmantarwa, nishadantar tare da fadakarwa da jama'a bisa harshen hausa _

                 🏔🅙︎🅦︎🅐🏔

*AL'UMMA WRITER'S ASSOCIATION*
🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎇🎇🎇🎇🎇🎇🎉🎉🎉🎉🎉🎉🎉🥳🥳🥳🥳🥳🎉🎉🎉🎉🎉

Muna taya ku murnar cika shekara ɗaya da kafuwa *(AL'UMMA WRITERS ASSOCIATION)* Ƙungiya ɗaya tamkar da dubu, ina miƙo gaisauwa tare da jinjina agareku marubuta *Al'umma*.🥳🥳🥳🥳

Allah ya ƙara muku basira ɗaukaka tare da dunbin mabiya marubutan Al'umma, haƙiƙa wani kayan sai amale, muna matuƙar alfahari daku, Allah ya kare daga dukkan sharri, Allah ya ci gaba da dafa muku cikin al'amuranku, Allah ya ɗaukaka ku, Allah yasa ku kasancen cikin jerin da al'umma zasuyi alfarhari da ku, bisa faɗakar dasu da kuke yi, Allah ya biyaku afsa faɗakarwa da kuke yiwa al'umma, Allah ya tsare gabanku da bayanku ya shiga cikin lamauranku duk duniya tasan daku.

Haƙiƙa mu ƙungiyar *Jarumai writer's association* mana matuƙar tayaku murna tare da tarin jinjina a gareku bisa ga namijin ƙoƙarin ku, Allah ya ƙara basira haɗe da hasken makaranta.

*HAPPY ONE YEAR ANNIVERSERY AL'UMMA WRITER'S ASSOCIATION ONCE AGAIN*🎉🎉🎉🎉🎉🎉🥳🥳🥳🥳🥳🥳🥳.

*Follow this link to join my* *whatsApp group*
https://chat.whatsapp.com/LXIF4UAUqeGCWONjQCrG4Y

*Follow this link to join my* *WhatsApp group* : https://chat.whatsapp.com/J7fqJ9AqzNTGfSryVEm4dZ

*Join me on Telegram*
https://t.me/joinchat/yZ0tHN29JA4wMzZk

*Join me on Whattpad*
https://www.wattpad.com/

*Page* 23~~24

    Murmushi ne ya subuce mata a lokacin da taga number innarta ta shiga,ringing ukku ta d'auka, handsfree Maryama Ta sa sannan takara a kunnenta dadai lokacin innarta ke cewa" ya akayi ne shalele dafatan kina lpy,"
"mssstwwwssssss"cikin kwabe fuska ta cigaba da cewa "ina ko lfy inna,tin jiya fa nake ta kiranki amma wayar ki ta ki shiga"
"miya faru ne shalele"
"akwai matsala fa inna dan ina tinanin aikin da mukayi kan kabeer ya warware"Cikin kidima da tashin hankali inna tace"whattt...!
kamarya ya warware?duk aikin da nasa akayi kansa!
Cikin yanayi na mutummen dake son yin kuka take cewa "Allah inna ya warware,kinga harda dukana yayi"
"duka kuma,yi hakuri kinji zai dawo hannu ne,duk sai kin rama abunda ya miki"
"tou inna,amma yau ne zamuje wurin dujjal ko?
dan gaskiya bana san na rasa kabeer"
"ki kwantar da hankalinki shalele ,indai ni hjy hawwa ina da rai da numfashi bazaki rasa kabeer ba har abada ko da kuwa zanyi yawo tsirara ne"
"yawwa mamata ta kaina shiyasa nake matukar sanki wallahi"
"nima ina matukar sanki 'ya ta"
"umm.. yau waccan matar saida ta kirani"
"wace matar?"
"dije mana ta gidansu kabeer"
"oh na tina ta,mi tace miki hala?"
"wai cewa tayi na tashi tsaye in ba haka wai sai dai naji ana gudaa"ta karishe maganar cikin takaici .
    "To mi take nufi"
"ina na sani nasan bai wuce wadancan shashashun uwayen nasa susa ya kara aure,tunda ba so na suke ba"
"bai isa ya yimiki kishiya na kyaleshi ba wlh,na shiga na fita na hana ama 'ya'yan wasu kishiya bale tawa 'yar "
"shiyasa fa mama bandamu ba,saboda nasan ina da ke,abunda yafi tad'an hankali shine kar aikin da akayi masa na farko ya warware,kinga ma yanxun yana yawan zuwa inda mahaifansa"
"ki kwantar da hankalinki shalele bana san kinasa damuwa a ranki,yanxu yaxunan bada jimawa ba zan dau hanyar niger "
"yawwa ummata,kinsan ance da zafi-zafi ake dukan karfe"
"hakan kuwa,sai kinjini"
"ok bye" ta katse wayar.
       Wani sanyayyen murmushi Maryama ta saki,gani take matsalarta ta kau yanxun,sanadiyar sanar da mahaifiyarta da tayi.

   Abangaren hajiya hawwa wato mahaifiyar maryama kuwa suna gama waya da maryama ta mike bedroom d'inta ta nufa,mayafinta ta d'auka ta fito,da Nafeesat karamar yarta suka hadu tace "inna ina za kije yanxu"
"inda kika aikan"
"a'a ni ban aikeki ko ina ba,kawai naga baki dade da dawowa ba,Allah yakai lapiya"
"Ameen"tace tana nufar parking lot.
   "Allah ya shiryaku keda sis gimbiya inkuna da rabon shiriya" tayi shigewarta dakin su.

      Karfe biyu dai dai aka tada su daga makaranta suka dawo gida.Bayan sun gaida inna saude ne suka wuce domin yin sallar azahar,alwala sukayi tare da yin sallah bayan sun idar sukaci abinci sannan salmat ta wuce gidan Fa'ixa kawarta(Idan mai karatu bai manta ba inna saude da inna laure abokanan juna ne) Gidansu na da tv,chan take  zuwa tana kallon wani shiri da ake cewa wai *DADIN KOWA* salmat na isa gidan suka hadu da inna laure zata fito waje,durkusawa salmat tana cewa "inna barka da yini"
"barka dai Salamatu kina lpy"
"lpy lau inna"
yanzu kuwa gidanku zanje,dafatan innarki na nan?"
"eh tana nan inna"tafada tana shigewa dakin inna laure,duk haushi ya cika ta na saida ita da inna tayi.
       Dakin ta shiga da sallama,da sauri Fa'ixa Ta taso inda take tana cewa "k'awalliya ya ankayi kika jima gashi har an fara shirin"
"kedai bari k'awas wlh tun dazu nazo innarki ta tsai dani a waje"
"ok,naganta zata fita tace gidanku zataje"
"eh wai hakan naji"suka maida hankalinsu kan shirin da ake.

   "Salamu Alaikum masu gida"
"Wa'alaikissalam,inna inayini"Aliya Da ta fito daga daki sana diyyar sallamar da inna laure tayi ta fada,"lfy lau,ya gida"
"Alhmdllh"
"Saude na ciki ne ?"
"eh inna yasu Fa'iza"
"lfy lau suke"tafada tare da nufar dakin inna Saude.
    Zaune ta iske ta bisa katifar ta "ashe ma idanunki biyu"
"eh wlh tunda kikayi sallama nafarka dama baccin baiyi nisa ba"
"ok,suka cigaba da fira irin tasu ta k'awaye.
       Daki na koma bayan mungama gaisawa da inna Laure domin nasamu nadan yi bacci kafin la'asar tayi na dora girkin dare,muryar inna laure naji tana cewa inna Saude "Ke bakiji miya faru da mai sunanki ba hala"
"wacce badai Saudi ba ko..!
"ita kuwa"
"miya faru da ita kuma"
"hhhhhhhh kinsan dai labarin bazai wuce tsakaninta da luba ba"
"mi akace tayi kuma yanzun"
"kedai bari,wai ibrahim ya shiga dakin luba sai yaga layoyi har ukku,sai ya tambayeta wad'annan na miye ne,kesan daga budar bakinta mitace mai"
"a'a sai kin fada"
"ce mai tayi wai na mallakar ka ne"
"tou shi kuma mi yace mata"
ce mata yayi "na mallaka ta kuma?"
tace ma "eh walla na in mallake kane"kinsan ba hankali ga luba ba,shikuma ibrahim ba mutunci ya ishe shi ba,daga tashi yayi yatafi gidan Saudi ya sallama mata suka gaisa yace mata" dan Allah tazo su tafi gidanai",bata kawo komi cikin ranta ba tunda kinga kamar kane yake a gareta,bayan sun isa gidanne ta zauna yace mata "wadan nan layun na miye ne? "ta kallesu ta kalle luba tace"luba ba layoyin ki bane na muggan mafarkan da kike"
daga buda bakin luba sai tace "a'a wallah ba haka bane",
ke in takai ce miki baran-baran akayi.
  Hmmmmm abun mamaki baya karewa ni bansan lokacin da luba zatayi hankali ba wallahi,kesan haka akayi case dinga da ita wai da daddare miji ya siyo mata kaza sai ta boye kingi tare da laidar ta sai da safiya ta waye tazo tana gwadawa sarakkuwarta  tace "ba kece duk abunda ya siyomin sai ya siyo miki ba,to kingani gashi ya siyomin jiya bai siyo miki ba"
dariya inna laure tasa tana cewa Allah dai yama ta hankali"Ameen"inna saude tace suka cigaba da firar su kala ina jinsu sama sama har bacci yayi awon gaba dani.
   A bangaren su inna saude kuwa dan muskutawa inna laure tayi tace "dama batun yarinyar nan ne Aliya ke tafe dani"
"umhmm ina jinki"
"wai cewa nayi tunda sunkusa kare makaranta baza ki kaita aikatau ba irin gidannan na masu kudii,kega in akayi sa'a dan gidan yaganta yace yanaso kega ke haye ai"
"tou laure banki ta taki ba amma kinsan yadda malam yake ji da ita bazai yarda ba,niko gaskiya a yanzun bazan tada hankali na ba saboda naga take-taken salamatu so take ya kara aure,gara dai na kwantar da hankalina tunda inason abina kuma ban rasa ci ba matsala dai yan kyale-kyalen nan ne na zamani dake burgeni bamuda amma nasan komi lokacine inshaallah ni Saude sai nayi kudii "dariya inna laure tasa tana cewa "Allah ya gwada muna lokacin kawata"su ka taba, inna saude na cewa sai dai ki kawo wata shawarar dai.
"tou naji ga wata shawarar mi zai hana ki.................................✍️✍️✍️

      *Zeesardaunerh ce*

          ( ~Y'ar karamar su babbar~ ~su~ 👧🥰🤩)

# _comment_
# _like_
# _share_

*comment and vote dinku shike* *karamin karfin guiwar typing*💋

WASU MATAN✔Where stories live. Discover now