👩👩👧👧 *WASU MATAN* 👩👩👧👧
@2021~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
*Story and Writting*
by
*Zainab sardaunerh*بسم الله الرحمن الرحيم
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai 📚_________________
______
🅙︎𝗮𝗿𝘂𝗺𝗮𝗶 🅦︎𝗿𝗶𝘁𝗲𝗿𝘀 🅐︎𝘀𝘀𝗼𝗰𝗶𝗮𝘁𝗲𝗱📚🖊
https://www.facebook.com/101679598253281/posts/101680068253234/?app=fbl
_Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa illmantarwa, nishadantar tare da fadakarwa da jama'a bisa harshen hausa_🏔🅙︎🅦︎🅐🏔
*Follow this link to join my* *whatsApp group*
https://chat.whatsapp.com/LXIF4UAUqeGCWONjQCrG4Y*Follow this link to join my* *WhatsApp group* : https://chat.whatsapp.com/J7fqJ9AqzNTGfSryVEm4dZ
*Join me on Telegram*
https://t.me/joinchat/yZ0tHN29JA4wMzZk*Join me on Whattpad*
https://www.wattpad.com/*Page* 41~~42
Ai ko yana fita inna Saude Ta buga tsalle tana cewa,
"Alhamdulillah,Alhamdulillah,Alhamdulillah"
tare da yin guda tana k'ara damke kudin a hannunta kar yazamana mafarki take ta farka basu a hannunta an kwace,Salmat ma ihun murna tasa tare da tsalle tana cewa "yeeee Adda Agla munyi kud'i ,wayyo ni salmat y'ar inna da Bappa dad'i bar ni da raina kar na sheka ban shirya ba,inna ta cinye kudin baki d'aya "tafa da cikin farin ciki da zolaya amma inna Saude bataa kula ta ba.Murna kawai Salmat ke yi ta kasa zaune balle tsaye.
Murmushi ne ya subucemini ina kallon innata da k'anwata da farin ciki mara iya ka ya wanzu a fuskokin su.
Ihun murnar da Salmat keyi shi ya tabbatar wa inna Saude dake tunanin mafarki take ba hakan bane gaskiya ne,kasa naga inna Saude tayi tare da yin sujjadar shukur tana cewa,
"Allah na gode maka,wai ni Saudatu nice keda kudi kimanin dubu daya-daya har dubu ashirin kai Allah na gode maka"
bayyana farin cikin inna saude ma b'ata lokacine domin fa ta fara ganin alamun cewa burinta na zama *HAJIYA SAUDE* zai tabbata ga alamu nan ta fara gani (sannunki dai amaryar Bappa hajiya saude🤣).Bangaren Bappa kuwa bayan fitarsu daga gidan suka k'ara yin sallama da juna Abba muktar yace,
"inshaallah duk lokacin da na shigo sokoto zan d'inka biyowa""na gode sosai ,Allah yabar zumunci"
"Ameen" Abba yace sannan ya shiga cikin motarsa.Zagayowa gefen taga Bappa yayi sanadiyar kiran da Abba yayi masa,duko kainai yayi Abba ya miko masa kudi kimanin dubu saba'in.
Suman tsaye Bappa yayi yana kallon kud'in da ke a hannunsa dakyar ya kakalo miyau a bakinsa da nufin yace wani abu amma kash sai Abba ya rigasa da cewa,
"don Allah in har ka dauke ni matsayin d'an uwa ba aboki ba kar kace bazaka amsa ba"
rasa abun cewa Bappa yayi , dakyar ya bud'i ba yace,"amma .....'
"Don Allah nace"
hadiye sauran maganar Bappa yayi ya chanza da yin addu'oi kala-kala tare da fatan alkhairi ga abokinsa,sannan Abba ya tada motarsa ya wuce yana murmushi.Ya jima tsaye a wurin sannan ya samu damar d'aga kafarsa yayi cikin gidan.Sallama yayi amma Aliya ce kawai ta'amsa ya yin da Salmat da inna basu san ma yayi ba,tsayawa yayi yana kalon su,fuskar su kawai ta isa bayyanar da farin cikin dake cikin zukatansu.Dakinsa Bappa ya shiga domin yasan a wannan lokacin ko yayi musu magana ba ganewa za suyi ba.
YOU ARE READING
WASU MATAN✔
Historia Cortaبسم الله الرحمن الرحيم WASU MATAN Littafi ne da ya kunshi halayen matan mu na yanxu ko nace matan zamani,halaye masu kyau da ma akasin su. Wannan littafi ya kunshi Kishi,kiyayya,tausayi,dama sauran su. INA ROKON UB...