Page 13&14

298 39 0
                                        

👩‍👩‍👧‍👧 *WASU MATAN*  👩‍👩‍👧‍👧
          @2021

~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤

*Story and Writting*
           by
*Zainab sardaunerh*

   بسم الله الرحمن الرحيم
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai 📚

         _________________      
       ______
🅙︎𝗮𝗿𝘂𝗺𝗮𝗶 🅦︎𝗿𝗶𝘁𝗲𝗿𝘀 🅐︎𝘀𝘀𝗼𝗰𝗶𝗮𝘁𝗲𝗱📚🖊
https://www.facebook.com/101679598253281/posts/101680068253234/?app=fbl
_Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa illmantarwa, nishadantar tare da fadakarwa da jama'a bisa harshen hausa_

                 🏔🅙︎🅦︎🅐🏔
*Follow this link to join my* *whatsApp group*
https://chat.whatsapp.com/LXIF4UAUqeGCWONjQCrG4Y

*Join me on Telegram*
https://t.me/joinchat/yZ0tHN29JA4wMzZk

*Join me on Whattpad*
https://www.wattpad.com/

*Page* 13~~14

    Ta jiyo muryar su khaleel suna cewa "oyooyo Abba sannu da  zuwa"

  Alokacin da ya shigo cikin gidan wani sanyayyen kamshi ne ya doke hancisa tare da masa sannu da zuwa.k'ayataccen murmushi ya saki yana kara gode ma Allah da ya mallaka masa Azeema A matsayin matarsa.
   
    Da sallama ya shiga cikin palon yayin da yaransa suke masa sannu da zuwa,amsa musu yayi yana shafa kansu.

   Wani sihirtaccen kamshi ne ya ziyarci hancinsa yayin da Umman Khaleel ta fito daga kuryar dakinta zuwa in da yake tana rusunawa tare da cewa...
"Abban Khaleel Sannu da zuwa ya hanya?"
"yawwa Umman khaleel "da murmushi a fuskarsa yake cewa "hanya Alhmdllh, kina tambayar hanya kamar wani gari naje"

  Chan kasa da muryar yadda yaran baza su jiba tace "a wurina wani gari kaje kam har na kosa ka dawo"

"ok dame-dame a ka tana darmin  yau"

"Abubuwa "

"ko"

"eh mana,amma muje ka fara watsa ruwa sannan"

"ok dear, kinyi kyau sosai"

Murmushi tayi tare da yin fari da i'danunta ta kashe masa daya tana cewa "muje ka fara wankan"
Allah yasani har cikin ranta taji dadin yabon da ya yi mata .

Ruwan wanka takaimasa bayi,ya shiga domin watsa ruwa koda ya fito ta fiddo masa kayansa tare da fesa musu turare,ita ta taya shi sa kayan kafin suka fito palon domin cin abincin dare.

A cikin plate daya ta zuba musu ita da hubbynta sannan ta zubawa su Khaleel na su a dayan plate,bisimilla sukayi tare da fara cin abincin.
     
      Ba yan sun idar ne suka danyi fira har yaran sukayi bacci.

Dakinsu takaisu wanda ke kusa da nata,Addu'o'i ta musu tar da lullube su da bargo becouse lokacin sanyi ne,ta fito tare da rufe musu kofar.

Dakin ta ta nufa, ta dauko duk wani a bunda zata bukata kafin ta wuce dakin Abban Khaleel.
  (Ni ko nace Asubah ta gari lovers)

    Bayan sun isar da sallar magrib bai fita a masallacin ba sai da ya yi sallar isha'i sannan ya fita.

   Room d'insa ya nufa ya sauya dressing zuwa kananan kaya,yasa facing cap dan baya san yawan kallo.

     Gurin motarsa ya nufa ya shiga,mai gadi ya bude masa gates ya cilla kan motarsa waje.
     
         *Shanghai Bakery and* *Restaurant* ya nufa dake cikin garin na sakkwato,bayan yayi parking ne ya nufi ciki, Already sunsan da zuwansa bai tsaya b'ata lokaci ba ya fito tare da ledar take-away "tsaki yayi saboda i'danun da  yan matan wajen suka zuba masa.
Bayasan yawan kallo a rayuwarsa.
Mortarsa ya shiga tare da cilla ta bisa titi yana tuki slowly.

  

   Allah yasan baya san abincin restaurant,amma ba yadda ya i'ya ne, Suhailat bata jin magana ko girki bata iya ba kuma ta koya taki,wai ita ba yar wahala bace kuma ba aikatau aka kawota ba. Ya kori yan aiki dan kawai tayi girki da kanta but nothing change,Alway's yana Restaurant.
    Shine a bunda yafi kona masa rai a rayuwa in ya yi magana mommy tace mai yai hakuri kuruciya ce ke damunta dat's why yasa mata i'do yaga iya gudun ruwanta.

   Itace ko da yaushe cikin yawo,bata Abuja,sokota kano e.t.c
   Alway's yawo sai shegen d'aukar photo gashi bata damu da shi ba kamar ba mijin ta ba .

  Dogon tsaki yaja "msstwwss" a lokacin da ya cilla motarsa a harabar gidan,har yanxu bata dawo ba.

    Part dinsa ya wuce,ruwa yad'an wasa kafin yasa sleeping dress ya hau bed d'insa.

    Duk inda ake san namiji yakai to haidar yake,Allah ya masa baiwar kyau,kwarjini tare da haiba, ga karfaffan jiki, dole duk macen da ta gansa sai ta rufta kansa bcox ya chan-chanci haka.

   Abuncin yad'an tsakura yaci sannan ya d'auko system d'insa tare da rufe kafafunsa da blanket mai taushi, ya jingina kansa a gadon tare da daura system din a kan laps d'insa .

    Agogo dake manne a bangon dakin nasa ya kalla,almost 12am amma bata dawo ba.

      Bayan an tashi islamiyya ne su Aleeya suka nufo gida da yake ba wani tazara tsakaninsu da makarantar da kafa zuka iso kuma kodama akwai tazarar to basu damu ba dan sun saba abunka da talaka da ke bid'ar abunda yaci.

Da guda guda duk abokanan tafiyarsu suka nufi gida ya rage daga Aglaa sai salmat,Amina and Bilkisu.
      Suna isowa garkar gidan su Amina su ka shige suna musu sai da safe,ya rage daga Aglaa(Aleeya ) sai salmat.

   Bakinsu d'auke da salama suka shiga cikin gidan,bappa suka samu kishingide yana hutawa,"Bappa barka da dare"Aleeya tace tana durkusawa  itama salmat yanda ya'yarta tayi hakan itama tayi .

    Amsa musu bappa ya yi yana cewa "harkun dawo? "

"eh bappa,ya hutawa?"

"Alhmdllh mamana ya karatu"

"muna nan munayi "inji salmat yayin da take nuna mai hadisin da aka musu.
  
Dakin inna  Saude ta shiga tana cewa cikin muryarta mai sanyi "Assalamu Alaikum"
"wa'alakissalamu"inna Saude Ta amsa mata,dukawa tayi tana cewa "inna mundawo" "tou"tace tare da gyara konciyarta tana cewa"Abincin ku na nan cikin madafi ku d'auko kuci "
"tou inna " Aleeya tace tare da mikewa tsaye.

Dakinsu ta nufa ,ta cire uniform na islamiyya kana ta saka na gida.Wata doguwar riga tasa wadda bata ji jiki sosai ba tayane kanta da mayafin ta,ta nufo waje .

Abincin su ta d'auka ta nufo inda salmat take tare da bapannata tana cewa...................................✍️✍️✍️

    *Zeesardaunerh ce*
  
         ( ~Y'ar karamar su babbar su~👧🥰🤩)

# _comment_
# _like_
# _share_

*comment and vote dinku shike* *karamin karfin guiwar typing💋*

WASU MATAN✔Stories to obsess over. Discover now