👩👩👧👧 *WASU MATAN* 👩👩👧👧
@2021
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
*Story and Writting*
by
*Zainab sardaunerh*
بسم الله الرحمن الرحيم
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai 📚
_________________
______
🅙︎𝗮𝗿𝘂𝗺𝗮𝗶 🅦︎𝗿𝗶𝘁𝗲𝗿𝘀 🅐︎𝘀𝘀𝗼𝗰𝗶𝗮𝘁𝗲𝗱📚🖊
https://www.facebook.com/101679598253281/posts/101680068253234/?app=fbl
_Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa illmantarwa, nishadantar tare da fadakarwa da jama'a bisa harshen hausa_
🏔🅙︎🅦︎🅐🏔
*Follow this link to join my* *whatsApp group*
https://chat.whatsapp.com/LXIF4UAUqeGCWONjQCrG4Y
*Follow this link to join my* *WhatsApp group* : https://chat.whatsapp.com/J7fqJ9AqzNTGfSryVEm4dZ
*Join me on Telegram*
https://t.me/joinchat/yZ0tHN29JA4wMzZk
*Join me on Whattpad*
https://www.wattpad.com/
*Page* 24~~25
Ga wata shawarar"mi zai hana ki barta ta ringa tara samari kamar yadda hindatu keyi...!
"wa ni rufan asiri irin wannan abun da hindatu keyi abu sai kace a kuya...
"y'ar tawace a kuyar ?
"nidai bance ba kama kawai nace,kuma walla koda mallam bai hana ba ni bazan barta tayi ba wallahi,ko da ba yata ce ta cikina ba ai hannuna ta tashi,so kike hala innna fita a dunga nuni ana cewa ga babar wance chan,ina ni gaskiya wannan shawarar bata yiba,ni da keson in na fita a dinga nuna ni ana cewa ga hajiya saude nan amma kina wannan batu,balle ma yarinyar da ko gyale bata fita dashi har zakice in bari ta tara samarii...chanza wata dai.
"hmmm ni Saude wace shawarar kuma zan baki..yanxu gabana kika zagi y'ata wai kamar akuya ko kunyata ba kiji ba sannan kike batun wata shawara"
"ke laure matsalata da ke abu bai wucewa gareki wlh,kinsan halina sarai bakina bai haila bale jinin biki,sanin kanki ne in abu baimin ba fad'a nake kar na cuci kaina,da nayi gulmarka bayan ka gara nayi gaban ka ehhe,ai ba karya na yi ba duk unguwar nan maganar hindatu ake yi,in yau mai kalar waccan mota yazo gobe wani zai zo shine abinda ake ta fada a unguwarnan kunki yi mata aure sai dai bata nan bata chan"
"duniya munafukai sunyi yawa wlh,in banda munafurci me yasa baza azo a taras dani a fada gabana ba sai dai a bayana"
"nima dai shi nagani shiyasa banason wannan abun dan kinsanni sarai bana daukar reni wlh domin duk y'ar iskar da tace ta zagan ni da itane ba kyalewa zanyi ba.
"tou ai shikenan tunda wad'annan shawarwarin basu miki ba sai nemo wata shawarar da kanki dan ke ba'a iya miki"
"hhhhh baki fadi karya ba laure,amma ai nasan zaki sake bincikomin wata,Laure tawa ni da ke muta karaba"
Dariya inna Laure tasa tana cewa "wlh Saude baki da dama,kinsan yadda zaki tunzura mutum lokaci guda kuma ki sashi ya sawko"dariya itama inna Saude ta saka suka ci gaba da firar su.
kiran sallar la'asar ya tada ni daga baccin da ya d'aukeni,dama ni bana da nauyin bacci kamar salmat sometimes da an kirani nake farkawa,ko da nafito daga d'aki haryanzu inna laure na nan bata tafi ba.Alwala na d'auro domin nayi sallah,bayan na idar ne nayi azkar dina sannan na fito domin na d'aura tukunyar abinci,anan waje na riske su inna Saude Suna alwala,kara gaidasu nayi sannan na tambayi inna miza'a dafa yau"tuwo da miyar d'anyar kubewa"da "tou"na amsa na nufi madafi.
Wuta na hasa sannanna fara d'aura tuwon shinkafar kamin salmat ta dawo ta siyomin saura kayan miyar.
Ina wankin shinkafa Salmat Ta shigo gidan,labari ta fara bani na wasan kwaikwayon da suka kalla a gidan inna dije wani abun in tafada sai nayi murmushi muna cikin haka inna ta fito zata na bayi taga Salmat"ke y'ar albarka da samu yau she kika dawo gidan?"
"la tund'azu na dawo ai,nadai tsaya ba Adda labarin abunda na kalla"
"tou, na d'auka yanzun kika shigo ai"
"a'a"
"zo ki amnashi kud'i ki sayo mata kayan miya"
"tou inna"tafada tare da bin bayan inna Saude da tayi hanyar d'akinta.
Kudin ta karbo na lisafa mata a bunda zata siyomin,duk da kudin ba wani yawa ne da su ba amma zasu isa girkin mai karamin karfi ba tare da ya takurawa kansa ba,fita tayi domin siyo abunda na lisafa mata ni kuma naci gaba da kimtsa gidan,tas na share tsakar gidan sai kyalli yake na d'an kimtsa dakin mu duk da ba wani hargitsewa yayi ba na d'auko yar kwalbar turarena na fisawa gidan .Aduniya ina mahaukacin son kamshi fiye da tinanin mai tinani,Allah ya shiryamin son kamshi a rayuwata amma duk da haka bana sa turare in zan fita domin hakan bai dace ba ko a addinance,ko minti biyu banyi da zaunawa ba bayan nagama shara sai ga Salmat Ta shigo "yanzu nake zancen ki a zuciyana ina cewa wai ina kika tsaya haka"
"Allah Adda kinsan wajen layi ke gareshi saida na jira"
"ok,kin siyo kayan magin?"
"i'm sorry my Adda wlh mantawa nayi gaba daya bari nayi sauri yanzun nan na karbo miki"
"ok plss kar ki jima kinji"
"inshaallah Adda"
Abangaren Abban Khaleel kuwa ya na ajiye su Khaleel a school d'in su mai suna ( *JAMA'A* *NUSERY AND PRIMARY SCHOOL* )dake nan mabeera bayan ya tabbatar da sun shige class d'insu ya wuce direct gidan su ya nufa domin jiya bai samu damar zuwa ya gaidasu ba.
Cikin gidan ya shiga da sallama mama dake nan waje ita da Aisha suka amsa durkusawa yayi yana "cewa mama ina kwana antashi lafiya"
"lfy lau Abubakar ya kabaro iyalin naka dafatan kowa lafiya"
"lfy lau suke mama,Azeema tace tana gaida ke"
"ina amsawa,ina kishiyata hala sunmin yaji sun bar zuwa"
Murmushi yayi yana cewa"duk suma qalau suke mama,inshaallah zasu zo muku weekend a satinnan"
"tou Allah kaimu"
"ameen mama"
Juyowa yayi inda Aisha dake cewa "yaya barka da safiya"
"barka dai Aisha,ai na d'auka yau baza'a gaidani ba "
"a'a babban yaya,nama isa..!baka dai ji bane amma tin d'azu na gai da kai"
"ok na yarda,ina su fareeda ne bangan su ba"
"sun tafi makaranta"
"ke miya hana miki zuwa?yafada ya tsura mata ido becox ko kad'an bayasan kannen nasa na wasa da karatu,musamman Aisha gashi ba lafiya bata ishe taba"
"bana jin d'adi ne yaya,idan ma baka yadda ba tambayi mama"
"kinci arziki nad'auka karya kike haka kawai ne kika ki zuwa da na saba miki"murmushi kawai tayi cikin ranta kuwa Allah take godewa da yasa mama bata karyata taba da kashinta ya bushe wurin yaya Ab,
tasan halinsa sarai bayasan wasa da karatu gashi ko wane hukunci zai musu mama goya masa baya take.
mikewa yayi ya wuce dakin Umma(mahaifiyar sa kenan)da sallama ya shiga dakin nata,zaune ya risketa bisa kujera ta cika tayi fam kamar ta fashe take ji,miyasa Abubakar baya jin maganarta ne,tace bata san alakarsa da mama Hawwa ko kad'an, bata son ya rabesu amma baya jin maganarta,tun da ya shigo gidan ta fito daga kuryar dakin ta tana jiran ya shigo domin dama tana nemansa amma shine ya shareta ya kusan kwashe rabin awa inda hawwa da shegiyar yarinyar chan fitsararriya ma'ana (Aisha),ita yabari zaune tana jirainai (niko nace ikon Allah,baima san tanayi ba)duk inda rai ke baci na Umma Hadiza ya baci a yau,bai ankara da yanayin da take ciki ba ya sake maimaita sallama domin duk a tinanin sa bataji bane amma har yanzu shiru ta matsa "Umma barka da safiya an tashi lafiya"ko kala batace masa ba duk da hakan ya kara maimaitawa cikin muryar dake nuna bacin rai da hasala take cewa"ban..................................✍️✍️✍️
*Zeesardaunerh ce*
( ~Y'ar karamar su babbar su~ 👧🥰🤩)
# _comment_
# _like_
# _share_
*comment and vote d'inku shike* *karamin karfin guiwar* *typing* 💋
YOU ARE READING
WASU MATAN✔
Kısa Hikayeبسم الله الرحمن الرحيم WASU MATAN Littafi ne da ya kunshi halayen matan mu na yanxu ko nace matan zamani,halaye masu kyau da ma akasin su. Wannan littafi ya kunshi Kishi,kiyayya,tausayi,dama sauran su. INA ROKON UB...
