Tafiya takeyi a hankali saboda yadda take jin jikinta babu kwari bayan ta gama fada da iskan da take kokarin daga ta. Hadari ya hadu sosai, sararin samaniya yayi duhu mutum zeyi zaton magrib ce, nan kuwa laasar ce sakaliya.Ta daga kai taga yadda hadarin ya hadu tasan cewar tabbas ruwan nan ze sauka kafin ta karasa gida duk da tafiyar da ta rage mata kadan ce. Tana cikin wannan tunanin ne taji yayyafi ya fara sauka nan da nan ta daga kafa ta fara sauri kada ruwan yayi karfi bata samu mafaka ba.
Tana yin gaba kadan ta hango rumfar leman maman mumina me gasa masara a gefen titi. wadda daman ta gama hada kayanta zata tafi ruwan ya riske ta. Da gudu gudu ta karasa karkashin lemar don ruwan yayi karfi yanzu.
suka gaisa da maman sikira sannan suka fara tattauna yanayin yadda hadari ya hadu cikin kankanin lokaci har ruwan ya cin musu.Jim kadan ba dadewa sukaji an fado cikin lemar a guje kamar wanda aka biyo, hankalin su yana kan labarin da sukeyi hakan yasa suka razana. Ta dago kai don ta duba waye ya shigo musu ba sallama.
saurayi ne jike tsamo tsamo a jike se diga yakeyi, farin yadin da yasa ya gaurawa da kasa har baka gane fari ne ko brown ne, Kamar wanda yayi burgima a cikin kasa, Slipper's din da ke kafarsa a tsinke.
Ko inda suke be kalla ba balle yasan da mutane a gurin. Ta juya daga kallon sa domin taga babu amfanin yi masa magana. Kamar an tsunkureta ta sake juyowa cikin fushi tace
"haba mallam ka razanar da mu"
Kamar tayi magana da dutse don ko kiftawa beyi ba, mutum se ya rantse ko numfashi bayayi. Bakin ciki ya kamata ta juya tana me jin haushin kanta da tayi masa magana.
Bayan lokaci kadan taga kamar mutumin kusa da ita yana kokarin kifawa. Yana wani irin layi kamar tabbabe ko mara lafiya, ba shiri ta matsa kusa da maman mumina domin mutumin ya fara bata tsoro
Sun rabe a kasan lemar na kusan minti 20 babu wanda ya sake cewa komai daga ita har maman mumina, kowa da abun da yake sakawa a cikin ransa.
Suna tsayen ne suka ji karar mata, A razane mutumin ya kalli farar jeep da ta taho a guje take tunkararsu . Ya juyo ya kalle ta da idanun sa jawur wanda yasa gabanta ya fadi da suka hada ido saboda tsoro.
Da sauri sauri ya fita daga kasan leman ya fara gudu. Yana gudu kamar ze fadi saboda layin da yakeyi. Abunka da mota ce nan da nan motar ta sha gabansa ta tsaya.
wani jibgegen mutum da bakin kaya ya fito daga bayan motar ya bar kofar motar a bude, da hanzarin sa ya kai ma saurayin nan cafka. ya fara jansa yana kokarin tura sa cikin motar shi kuma saurayin yana tirjewa. Haka sukayi ta fama har wannan katon mutumin yayi nasarar saka saurayin cikin motar .
Cikin tashin hakali da razana maman mumina da Ummulkhairi suka dibi gudu kowa ya kama hanya daban. Tana cikin wannan gudun ne taga mai adaidata sahu tayi saurin tsayar da shi.
shima me adaidata se da ya tsorata yadda yaga gudun da takeyi kamar an biyo ta.
Bata bari adaidata ya tsaya gaba daya ba ta kama karfen adaidaitan ta dane.Shigarta ke da wuya taji ana cewa " muje muje" da karfi, a lokacin ne ta kula ashe da passenger a cikin adaidaita.
hannunta tasa a kan kirjinta saboda yadda takeji kamar zuciyarta zata fita. Ga tsoro ga gudu, sannan ta fara maida numfashi.Cikin zakewa mai adaidaitan ya fara tambaya lafiya
"lafiya!!!!! Me ya faru????"Passenger ne ya dakatar da shi
"Haba malam ka barta ta nutsu mana, baka ga halin da take ciki ba ne"A lokacin ita ba nutsuwa take bukata ba domin nutsuwa baza ta samu a nan kusa ba. Burinta a ceci wannan mutum da akayi kidnapping. Tabbas kidnapping dinsa akayi.
Magana take yi da sauri numfashi na katsewa ga haki da takeyi take nunawa da hannunta,"motar can........ wani........ sun dauka..... sun dauke shi.... Wayyo!!! Wayyo Allah!!!!!."
passenger ya kara tambayarta
"wa aka dauka? Su waye?."Murya na rawa tace
"wani kato...... yayi kidnapping....... Sunyi kidnapping wani....... a chanwani zazzafan kuka ya kwace mata ta fara yinsa ba tsayawa.
Cikin adaidaitan yayi tsit se shashekar kukanta ke tashi. Tasa kanta a gwiwa se da tayi me isarta sannan ta dago ta fara juye juye tana so ta gane a inda ake. Nan kuwa ta lura an wuce inda ya kamata ta sauka, tace da mai adaidaitan zata sauka. Ba musu mai adaidaitan ya tsaya ta sauka da saurinta.passenger yana mata magana bata ji shi ba. Kafin ya sauko ya bita ta shiga wani lungu ta bace batt.....
YOU ARE READING
Sarkakiya
RomanceLabarin tsantsar soyayya me cike da sarkakiya ce ta kullu a tsakanin su. Ummulkhair ta zamo Allura cikin ruwa wanda me rabo ne ze dauka. Shin wa zata zaba a cikin su? Boyayyen masoyi Abdulkareem wanda yayi dakon soyayyar ta na tsahon lokaci ko kuma...