Rikici master

193 13 0
                                    

🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Se bayan bagrib sanan ta isa kano. Tunani kawai take yi a hanya tana godewa ubangiji da rahmarsa. Lallai Allah ya taimake ta da ta tsallake rijiya da baya.

Yau kam da alhaji Audu ya keta mata mutunci bata san inda zata tsoma ranta ba, ga kuma hiv da zata iya dauka daga jikinsa. Ita kam aure ma ya fara bata tsoro, wani irin masifa alumman mu take ciki?, wani irin rayuwar aure ake yi a zamanin nan.

Tana mamakin yadda mace zata zauna da miji mazinaci alhalin ta sani kuma ta ci gaba da zama da shi. Duk da ba ita ce a matsayin sa'adatu ba amman tana ganin baza ta iya zama da mijin da ta san mazinaci ne.

duk yadda zata juya abun a ranta bazata iya yin irin rarraunan tunani irin na saadatu ba. Ko dan ba ita ce a cikin matsalar ba oho.
Addua ta dinga yi Allah ya tsare ta ya tsare zuriyar ta, wadanda sukeyi kuma Allah ya shirye su ya ganar da su gaskiya, mata kuma da suke cikin irin wannan matsala na rayuwa Allah ya yaye musu, ya kawo musu mafita sannan yasa hakurin ya zame musu sillar shiga aljanna.
Zikirin ALHAMDULILLAH, ASTAGFURULLAH tayi ta maimaitawa har suka iso kano.

Tana isa gida ta tarar da umma tana wanke mangwaro a bakin fanfo, umma tayi mamaki matuka da ta ga khairi a wannan lokacin.

"Lafiya ??? Lafiya kika dawo yau?"
Abinda ta fara ce mata kenan

Khairi ta kwakulo murmushi sannan tace
" lafiya kalau umma, nazo na gan ku ne"

Umma ta kashe famfo tare da mikewa daga durkushen da take
"Gaskiya bana son dawowar ki nan da bakya fada se de mu ganki a gida, hankali na baya kwanciya. Gashi yau ma tafiyar daren kikayi
Umma ta fada da lafazin fada

"Haba ummana kiyi hakuri to"
ta karasa ta rugumi umma tana dariya

"Sake ni dallah, iskancin banza"
Umma ta fada tana dariya ita ma

Abinda umma bata sani ba rugumar da tayi mata kwalla ce ta cika mata ido, kuma bata san umma ta gani se tayi saurin rungumar ta. Ko da ta rungumeta share hawayen tayi da sauri sannan ta dago

"Muje ciki umma" ta fada tare rike mata kwanon mangoron
🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒

Rikici master, yau ma rikicin ne ya tashi a office din. Se masifa yakeyi ma maryam secretary dinsa, ita kuwa ba abinda take cewa se "sorry sir". Wani abun ma idan yana magana da sauri ba ganewa takeyi ba.
Turancin yafi karfin ta

Ba don rikicin sa ba da ko wace mace a company se ta folla masa. Yana da tsayi daidai gwargwodo ga kyaun shi shima abun yabawa ne. Gashi ba baki bane colour sa tayi kama da na black Americans. Idan yana magana da turanci duk abun ka se ka juya ka kalle shi. Wani ma ze iya rantsewa ba dan kasar bane musamman idan yayi magana.

To masifa irin tashi ma baza ta bari wata mace ta rabe shi ba, kowa tsoransa yakeyi a company. Wani lokaci yayi ta rikici da masifa. Wani lokacin kuma kamar gawa, se ya ki kula kowa ba ko da kuwa gaishe shi akeyi baze answer ba. Idan ya rufe office dinsa ko secretary sa maryam bata isa ta shiga office din ba.

Maryam a fusace ta bar office din ta nufi nata office din sannan ta rubuta resignation latter (takardar barin aiki) yau ya kaita bango, ko a chanza mata wani office ko ta bar aikin gaba daya.
Ta samu jidda a office dinta ta mika resignation letter akan a bawa Alh ibrahim, Jidda ta bude baki cike da mamaki sannan tace

"Kin manta deal dinku da Alhaji ne?"

"Jidda bazan iya ba na gaji, MD ba mutumin da zan iya jurewa aiki da shi bane" maryam ta fada sannan ta nimi kujera ta zauna.

Jidda ta dauki wayar telephone da ke kan table dinta ta kira Alh ibrahim ta wayar sa na office, ta sanar da shi abunda maryam take shirin yi.
Ta san Alh ibrahim baya wasa da lamarin da ya shafi umar, duk aikin da yakeyi ze tsayar da shi don ya saurari maganar shi Balle ma shi yasa maryam personally a matsayin secretary sa domin ta dinga monitoring duk wani abun da yakeyi saboda be yarda da umar ba, yasan ze iya yi mishi illah babba.

Jidda ta ajye wayar sannan tace da maryam ki shiga office ki same shi yanzu

Maryam ta shiga office din a sanyaye inda ta tadda ALH ibrahim yana mata murmushi sannan ya nuna mata wajen zama. Ta zauna a takure ba sakin jiki ba

"Me yasa kike son barin aikin da na saki"
Ya tambaye ta

"Sir MD yana da wuyar shaani ne, sannan kullum masifar sa karuwa takeyi, duk abunda nayi a cikin fada ne"

Alh ya nisa sannan yace
" me kike so ayi miki, zan kara miki salary don ki zauna kiyi min aiki da na saki" ya fada yana murmushi

"Ba haka nake nufi ba sir, Ina tunanin ya fara ganewa ina spying a kansa shi yasa yanzu fadan nashi ya fi yawa"

Damuwa ce ta bayyana a fuskar Alhaji sannan yace
"Ya akayi kika bari ya gane ?"
Ya tambaya tare da mikewa ya fara zaga office din cike da damuwa

A tsorace maryam tace
"MD be yarda da ni ba kwata kwata tun farko, duk sanda nayi kokarin shiga cikin lamuran sa se yayi min cin mutunci sosai, shiyasa nake tunanin ko ya fara gane akwai wani abun ne"

Alhaji ibrahim yayi shiru na dan lokaci sannan yayi magana

"To ina ganin lokacin barin ki office dinsa yayi, zansa a chanza miki office amma ina son maganar da mukayi a baya ta tsaya a tsakanin mu, kar ki sake na ji shi a wani gurin"

Yana magana yana murmushi amma a bayan murmushin sako ne wanda yake nuna idan ta bijire masa baza ta ga da kyau ba

"Yes sir, insha Allah baza'a ji komai daga baki na ba"

🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Bintu. A
09034346763

SarkakiyaWhere stories live. Discover now