Rashin lafiya 2

153 9 0
                                    

🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Washe gari da safe ya kira umma ya sanar da ita khairi ba lafiya kuma bata cin abinci. Umma tace yazo gida ya karbar mata kunun tsamiya.
Umar ya fita ya tafi gidansu khairi, tunda akayi auren be je ba se yau. Ya shiga ya gaishe da su tare da basu hakuri a bisa yadda yanayi ya kasance.
Umma da abba sukayi mishi nasiha tare da addu'an zaman lafiya
Umma ta dauko kunu da kosai a flask ta bashi ya kai mata.

Yana dawowa ya shiga dakin dan ya duba ta, a nan ya tarar da ita a cikin bargo ta rufe har kai, har ze juya don yayi tunanin bacci take yaji tana sauke ajiyar zuciya a hankali.
Ya dawo ya saka hannun sa cikin bargo dai dai kafar ta don ya taba yaji ko har a lokacin da zazzabin a jikin ta. Yana tabawa yaji zafi zau.

Jin muryar ta yayi a kasalance tana cewa
"Rufe sanyi nake ji"
Umar ya rufe sannan ya dawo inda kanta yake yana mata sannu.

Cikin hanzari Ya koma kitchen ya dauko bowl da ruwan dumi hade da towel ya dawo dakin ze mata towel bath
Da kyar khairi ta bari yayi mata towel bath.

Umar ya fara da kanta zuwa wuya da hannaye, cikin jikin nata ma yana bukatar towel bath saboda zazzabin ya sauka.
A hankali umar ya fara zura towel din cikin rigar ta yana shafawa. Wuyan rigar bubun da ta sa jiya baya barin shi ya sa hannun sa sosai
Da kyar da lallami hade da lallashi khairi ta bari ya cire bubun daga jikin ta ya zama daga ita se vest da underwear,
Umar ya kula da kunyar da take ji saboda ta kasa sakewa kwata kwata. Intentionally ya jika vest din da ke jikin ta da ruwa saboda yasan baza ta barshi yayi mata towel bath a gurin ba. ya dinka shafa mata towel din kusan ko ina, har cinyoyi da bayan ta amma ko da wasa be taba kirjin ta ba, ya de jika da ruwa

Bayan ya gama ya lallabeta ta sha kunun kadan sannan ya ballar mata magani ta sha. Ya duba wordrop dinta ya dauko mata wani kayan, da vest da Wani underwear hade da wata daguwar rigar mara nauyi saboda vest din da skirt din sun jike. Ya ajye a kan gado yace mata ta saka yana so ya kaita asbiti.

Khairi ta saka kayan, ba lefi jikin ya danyi mata dadi, ta zuro slippers dinta ta kara sweater a jikin ta sanna ta same shi a parlor yana jiran ta.
Yana ganin ta ya tashi da sauri ya ruko hannun ta har jikin mota sannan ya bude ya kwantar mata da seat din gaba, ta shiga a hankali tana yamutsa fuska saboda ciwon da take ji. ya zagayo ya shiga motar se asbiti.
A hanya yayi ta mata sannu, ita kuma tana kwance ta lafe a jikin gujerar Ita kadai tasan me take ji dan zazzabi ba karami ciwo bane

Asbitin da umar ya kwanta nan ya kaita itama. Dr ilyasu ya duba ta ya rubuta magunguna sannan suka dawo gida.

Haka umar yayi ta dawainiya da ita har dare
Yayi mata se da safe wajen karfe 10 na dare sanan Ya dawo dakin shi don yayi bacci shima.

Yana kwanciya hoton yanayin da ya ga khairi jiya da towel da yau da yayi mata towel bath se dawo masa yake. Ya tuno yadda yayi mata towel bath da ruwan ya jika farar vest din ta, abubuwan da ake ta boyewa suka bayyana. Da taimakon Allah ya gama towel bath dinnan saboda irin yanayin da ya shiga. Ga yadda cinyoyin ta suka haukata shi.
Ya ci gaba da juyi a kan gado har bacci ya kwashe shi da kyar.

umar ya ci gaba da dawainiya da ita har taji sauki ta warware. Wata rana Abba da umma suka zo duba ta wanda Umar yayi musu iso har cikin daki inda khairi ke kwance. Tana ganin su ta saki kuka, ta rasa kukan me takeyi ma, umma da abba sukayi ta lallashin ta suna bata hakuri daga bisani sukayi musu sallama suka tafi.
Umar yayi yayi ya maida su gida abba ya ki yarda.
Bayan sun koma gida bakin abba yaki rufuwa se murna yake, yace da umma

"Baki ga yadda yaran nan suka saki jiki da juna ba, Naji dadin yadda na gansu"

Umma na murmushi tace
"Baka ga yadda umar yake nan nan da ita ba. Nima naji dadin yadda na gansu gaskiya se dai muyi ta musu adduan Allah ya kauda duk wata fitina ya hada kawunan su ya zaunar da su lafiya"

Abba ya amsa da ameen yana jin dadin adduan da umma tayi. Abba yayi kasa kasa da murya kamar me yin rada
"Amma zarah bakya ganin kamar ciki ne da khairi kuwa. Na tuna kema hake kike ciwo idan kin samu ciki"

Umma ta sheke da dariya jin theory abba
"Haba abba, yaushe yaushe akayi auren, du du du bata fi sati 2 da zuwa gidan ba. Idan ma ciki ne ay baze nuna kanshi da wuri haka ba. Kai abba dadi na da kai ka iya zumudi wlh"

Shima abban dariya ya dinga yi
"Ta ina zan gane abubuwan ku na mata, saura kiris na kira Alhaji nayi mishi albishir"

Umma ta saki baki tana kallon abba
"Ahhh lallai a gaishe ka abba, kun cika sirikan zamani, a ina na taba jin anyi irin wanann kwabar"
Suka kwashe da dariya gaba daya.
🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒

A can Abuja magana ta gama yaduwa MD ya auri secretary dinsa ummulkhair a kano. Ma'ikatan sun sha mamakin yadda abu ya juye haka, a iya sanin su SS sun zo sun tafi da khairi bayan lokaci kadan se labarin aure suka ji. Wasu suna tausaya mata ganin irin baudadden hali na umar wasu kuma suna ganin ta tsinci dami a kala.

Intisar tafi kowa mamaki saboda a iya sanin ta ba wani abu bene tsakanin su, though de ranar da umar yace ta kaishi gidan su khairi tayi suspecting wani abu amma daga baya ta kawar da wannan tunanin ganin alakar ummulkhair da oga Ak.
Tayi fushi da khairi sosai a tunanin ta khairi ta boye mata auren ne saboda wani abu, shiyasa itama tace baza ta kira ta ba.

A bangaren jidda kuwa babu Wanda ya kaita farin cikin auren nan, ina ganin ko shi angon be kai ta murna ba Kamar ta zuba ruwa a kasa ta sha, tana ta hamdala ga ubangiji da ya sa haka ta faru. Yanzu Ak is free, abun da ya rage mata shine yadda zata cusa kanta gare shi har ya fara son ta. Babbar obstacle dinta ta ta kau. Allah Allah take oga Ak ya dawo aiki ta fara baza nata salon.

Abdulkareem har a lokacin be koma aiki ba, wadanda suka je paris tare duk sun koma aiki bayan dawowar su da kwana biyu banda Abdulkareem, kuma be bada reason na rashin dawowar sa ba hasali ma baya daga waya idan an kira shi. Har an rubuta query akan sa Alh ibrahim yace a bari, a kyale shi duk lokacin da ya dawo shikenan.

ALH ibrahim ne kadai yasan dalilin rashin dawowar sa aiki and his anger is justified. Shi kan shi Alhjin kusan kullum se ya kira Ak baya dagawa, yayi masa messages da yawa Beyi reply ba. Tun yana kano bayan auren su khairi Alhaji yaso ya hadu da shi face to face suyi magana amma abu ya gagara

A lokacin Abdulkareem ya gama fita daga hayyacin sa, ya rame yayi duhu sosai, yan uwan sa suna yawan zuwa gida a hadu a parlor ko dakin sa ayi ta hira duk dan a debe mishi kewa amma Ak be san suna yi ba, yana zaune a gaurin ne kamar mutum mutumi babu uhm babu uhm uhm. Idan ya gaji da surutun ma se ya tashi ya basu guri.

Hajja ta shiga cikin damuwa itama sosai da har wani lokacin se taji gwara taje gidan su khairi da kanta ta tambayi me yasa sukayi ma danta haka, danta be cancanci irin wannan yaudarar ba. He is completely broken in and out. Meyasa suka bashi false hope? suka lasa masa zuma sananna suka bashi madaci daga baya.

Alhaji wada ma baya san zuwa duba Ak saboda duk sanda yazo se yayi ta masifa tare da kwashe ma dangin ummulkhair Albarka gaba dayan su.

🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Bintu. A
09034346763

SarkakiyaWhere stories live. Discover now