Punishment

161 9 0
                                    

🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Da asuba khairi ta kalli bashariya taga yadda take bacci kamar mattaciya, yadda take bacci ba tafiya ba ko sukuwa ake a kan gadon da take kwance baza ta ji ba saboda nauyin bacci. Da kyar khairi ta iya tashin ta tayi sallah, bayan sallah suka koma bacci gaba daya se past 8 khairi ta tashi, bashariya kuwa se 9.
Bashariyyya ta tafi kitchen yin aikace aikacen ta. Khairi na ganin bashariya ta fita kitchen ta sa key a dakin ta shiga wanka.

Ta fito daga wanka daga ita se towel din da ya tsaya iya cinya. Ta tafi gaban mudubi tana shafa mai hankalin ta a kwance. kamar daga sama ta ga umar a bayan ta a tsaye ta jikin mirror, cikin mamaki ta juyo dan ta tabbatar shi din take gani.

Ya Hade fuska babu alamar wasa kamar umar din da ta sani a farko. Ya tako har inda take a gadarar ce sannan ya  miki mata handle din kofar dakin gaba daya tare da fadin
"Kinyi tunanin rufe dakin da key ne ze hana ni shigowa?

Kallan sa ta tsaya yi baki a wangale cike da mamaki wato don ta rufe  dakin da key shine ze banbare lock din dakin gaba daya? Se kuma ta tuna this is umar kadan daga cikin abun da ze aikata ne

A hankali ya kara matsowa daf da ita ya kasance babu wani space tsakanin su, jikin ta har bari yakeyi saboda tsoron abun da ze iya mata gashi daga ita se towel.
Umar ya zagayo ta bayanta yayi huging dinta tare da shakar sanyayyen kanshin jikin ta, ta so ta kwace amma ya riga ya sakalo hannu a  kugun ta ya rike ta gam.

A sanyaye ya rada mata a kunne
"Get ready for today's punishment"

Idanun ta ne suka fito waje
"Dan Allah kayi hakuri"
Ta fara bashi hakuri. idonun sun yi rau rau tana shirin kuka.

A hankali ya fara sensually kissing din wuyanta zuwa kafadun ta, har da bayan ta inda towel din be rufe ba.
Jiki da jini, nan da nan jikinta ya mutu, this is the first time she is experiencing this. da yawan mata nan ne weak spot dinsu and khairi is no exception. Tun tana bashi hakuri har maganar ta dena fitowa daga bakinta se soft moans. Duk da haka ta rike towel dinta gam dan ze iya faduwa a ko wani lokaci

Shima umar din ya shiga wani yanayi na daban. Idanun sa suka kada sukayi ja, he desperately wants to delicately touch and kiss every inch of her body. She has this perfect body da ze rikita duk wani namijin da ya gani
Beyi intending yayi mata wani abu ba, he doesn't even wants to sleep with her. Saboda a nashi reasons din ze cutar da ita idan yayi hakan

For him this is just a punishment, punishment din zancen Abdulkareem da tayi. Yana so ya mantar da ita existence din Ak gaba daya, let her focus on him alone tunda shine mijin ta.

Ya juyo da ita a hankali yadda zatayi facing dinshi, ya ci gaba da kissing kumatun ta, habar ta, ko ina ya samu a fuskar kawai kissing yake.
Idanun ta a rufe suke gam, wani irin transmission connection take ji yana tsarga mata to the extent da duk abun da ze mata a ranar baza ta iya hana shi ba.

Ya dago da habar ta sama yadda ze ga fuskar ta da kyau tunda ya fi ta tsaho sosai, she looked soo innocent and pure. Idanun ta a rufe suke still, zara zaran gashin idon ta sun kwanta gwanin kyau. Her lips were inviting and he couldn't resist them tempting him.
Ya sunkuyo a hankali yayi kissing dinta. Kiss din yau ba irin na jiya bane da akayi shi roughly, kiss din yau is soo passionate da har taji kafafuwan ta sunyi sanyi kamar ba za su dauke ta ba.

Shima ji yayi kamar ya dauke ta ya kaita gado komai ma ya faru.Da kyar ya iya sakin ta saboda baya son ya wuce gona da iri, baya son ya keta wannan line din da ya ja. Ya haramtawa kansa abun da Allah ya hallarta masa
A hankali khairi taji ya sake ta sannan ya matsa daga kusa da ita, kamar anyi ruwa an dauke. kunya ta hana ta bude ido hade da Haushin kanta da ta fara ji kuma.
Ta yaya gangar jikin ta ze yi betraying zuciyar ta, ya akayi tayi falling for temporary lust haka. Ji tayi kamar ta mari kanta saboda takaici

Cikin deep husky voice taji maganar umar
"Ki shirya zamu je gidan su umma daga nan zamu je cikin gari mu gaishe su suma"

Ya kara ruko ta jikin sa ya manna karamin  kiss a lebe sannan yace
"Ina jiran ki a parlor"

Yana fita daga dakin ta sulale ta zauna a kan gado don zaman take bukata a lokacin. He has messed her head really bad.
Tafi minti 20 a zaune tana reminiscing abun da ya faru, haushin kanta ta ji da har ta tsaya ta barshi yayi yadda yaso da jikin ta, her own body? wannan wani irin abun kunya ne.

Bayan lokaci kadan ta shiryo a cikin doguwar riga abaya sabuwa da Aunty M ta siyo mata. Jeans da vest ta sa a ciki sannan ta dauko black after dress ta saka. Ta janyo jaka da slippers dinta masu kyau ta zura suma duk sababbi.
Face dinta ma ba wani kalliya tayi ba, powder ta shafa se kwalli se lip gloss da ta shafa a slightly puffy lips dinta.

A parlor ta tarar da shi shima ya shirya a manya kanya, kayan da be cika sawa ba. Yayi kyau dan kyau amma wannan ba damuwar ta bane.

Shi kuwa Gani  yayi kamar an canza ta, kamar ba ummulkhair din da ya bari dazu a daki ba, tayi wani irin kyau na musammam me kashe ido. abayar da tasa ya tuno masa da lokacin da ya siyo mata abaya a Abuja lokacin da tayi staining kayanta. Kamar ma ya fasa fita ya sa ta a gaba da kallo kawai.

A mota duk jikin ta a mace yake, gani take kamar taci amanar Abdulkareem, be kamata ta bar umar yazo kusa da ita ba idan har da gaske ba son shi take ba. Daga yau ta yanke shawarar baza ta kara bari umar yayi kusa da ita ba bare har ya taba ta.

Tare da bashariyya suka fito suka rage mata hanya sanna sukayi cikin gari family house din su. A can ma kowa se yabawa da son barka yake, duk wanda ya gansu tare yasan sun dace da juna gashi har dan kama suke abun ka da jini, Sai dai umar ba fari bane irin su irin caramel color ne shi ba baki ba shi ba fari ba.

Iyaye da kakanni suka ta yi musu Addua da fatan Alkhairi. Har tsokanar su ake Allah ya kawo kazantar daki.
Umar ya kalli iya falmata sanna yace
" menene kazantar daki kuma"

Iya tayi dariya sannan tace
"Kunsan mutumin naku bature ne ku dinga yin hausar da ze gane, cewa sukayi Allah ya kawo yara"

Kowa ya fashe da dariya a dakin

Da jin an ambaci yara fuskar umar ta chanza, ran sa ya baci har se da khairi ta lura da hakan, ragowar mutanen dakin basu kula ba saboda hayaniyar surutu da ake tayi ana ta dariya

An gama gyaran family house har sun koma ma, gida yayi kyau dan kyau kamar ba gidan ba. Anyi furnishing ko wani part dai dai wanda ze ishi mutum zaman duniya.
Branch din su umar na kano ne sukayi aiki. tunda company ne it took them less than a month aka gama komai, basu cika yin residental aiki haka ba inde ba mansion mutum ze gina ba ko estate

Sukayi sallama da kowa a gidan sannan suka wuce gidan su khairi, tayi missing din gidan duk da har yanzu bata gama hakura da abun da akayi mata ba, tayi missing rayuwar ta a baya, rayuwar kafin ta fara service.

Har yanzu abba kunyar hada ido yake da ita, umma kuwa ta maida komai ba komai ba se nan nan take da su. Se bayan magrib sannan sukayi musu sallama.
Khairi ta fito daga gidan tana mamakin wai ita ce yau zata koma gidan umar da kafar ta? abun har daure mata kai yake. Lallai rayuwa abun tsoro ce, kana naka Allah na nashi

Da daddare khairi tsoron bacci tayi saboda yau babu bashariyya gashi dan security da take tunkaho da shi umar ya girgide, ze iya shigowa dakin kai tsaye idan yayi niya. A haka har bacci ya kwashe ta.

A cikin bacci taji kamar an daddaure ta ga wani dumi da take ji, tana bude ido taji umar a bayan ta ya rukunkume ta. Bata san lokacin da ya shigo ya kwanta a kusa da ita ba har ya samu daman hugging dinta haka. Da sauri ta kalli jikin ta don ta tabbatar kayan ta is intact saboda nayin bacci gare ta umar ze iya mata wani abun bata sani ba. kayan ta na nan intact dan da jeans din ta kwana saboda tsaro.

Cikin muryar bacci me kashe jiki taji yayi magana kasa kasa a kunen ta
"Good morning babes"

Saboda takaici kasa ansawa tayi se balle hannun sa daga rukun da yayi mata a kugu tayi sannan ta mike tayi toilet.
se da taji fitar sa daga dakin ta dauro Alwala ta fito yin sallah asuba

🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Bintu. A
09034346763

SarkakiyaWhere stories live. Discover now