🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
"Sake min hannu!
Ta fada da karfi bayan umar ya janyo ta wajen farfajiyar da ake parking motoci,"Ka sake min hannu nace!!!!
Ta kara masa ihu tana kokarin fizge hannun daga rukon da yayi mata har ta samu ta iya kwatar hannun. Ba wai karfin ta bane yasa ta iya, gajiya yayi da mutsu mustun da takeyi yasa ya saki hannun ta.Yana sakin hannun ta juya da zummar komawa cikin hall din, sai ta koma gurin Ak sede duk abunda zeyi yayi.
Cikin zafin nama ya sha gabanta ya tsaya, tayi dama ya tokare ta. Tayi hagu shima ya kara tokarewa."Wai me kake so ne, menene damuwar ka"
Ta fada a hankali saboda ta gaji da yin ihu, Tun da suka fito take ihun ya sake mata hannu, se da yaga dama ya sake ta"Ke ce damuwa ta, ke kike damun zuciya ta, ke kike hana ni kwanciyar hankali. Ke, ke, ke"
Ya fada yana nuna ta da dan yatsaDariyar takaici tayi dan Babu tantama yana da tabin kwakwalwa.
"Ka bani guri na wuce, a iya sani na ban taba damun ka ba hasali ma kaine ka addabi rayuwa ta. ban san meyasa kake muzguna min haka ba, ban san me nayi maka ba."
Muryar ta har ta na rawa kamar zatayi kukawe are leaving this place this instant"
Ya fada da dakakkiyar murya kamar wani ubanta"We? Kai da wa?"
Ta tambaya tare da auno masa wani kallon banza, ragowar girman da take bashi ya zube. Dan mutuncin sa da ya rage a idon ta ya tsiyaye saboda abunda yayi mata Don haka zata fada masa duk abunda ya fito bakin ta saboda shi ya janyoKara damkar hannun ta yayi ya fara ja zuwa gurin motar sa ita kuma tana cijewa , da kyar ta iya fizgewa daga rukon da yayi mata.
Hannun yayi jaa yana mata radadi abunka da farar fata. Hawaye ne ya fara sauka daga idonta saboda takaici, da muryar kuka tace
"Ina zaka kai ni, meyasa kake min haka, me nayi maka??"Because i love you!!!!"
Ya fada da karfi, har tana jin echo muryar sa a kwakwalwar ta. idonsa yayi ja.Sankarewa tayi ta kasa motsi a wajen, ta zura masa ido kamar me neman wani abu a idonsa. Har yanzu abunda ya fada be gama clicking a kwakwalwar ta ba.Even in her wildest imagination bata taba zaton abunda ze fada ba kenan. He must either lying or mad
A sanyaye ya kamo hannun ta duka biyu ya rike a hankali kamar ya rike kwai, ya tsura mata ido, a hankali ya cigaba da magana
"i love you so much and i can't help been head over heels for you, can't you see i am running mad for you"
Ya tsaya na dan seconds yana kallon ta wadda ita saboda shock ma ta kasa motsi, se kif kifta ido kawai takeyi.
Kamar an tsunkure shi yayi sauri ya sake hannu ta. Hannu biyu yasa a kansa tare da juya mata baya
"Ohh Allah!! What am i even saying, me nake fada ne wai?
Ya fada a hankali, daga ji kasan da kanshi yake magana. Be san ya akayi har maganar ta subuce daga bakinsa ba, beyi niyar fada mata yanzu ba. Ko da ze fada not in a chaos situation like this.Ya kasa juyowa Yayi facing dinta, aikin gama ya gama. Be san da wani idon ze kalle ta ba kuma.
yana tsayen ya juya mata baya yaji muryar Abdulkareem yana cewa"Zo mu tafi"
Yana juyowa yaga Abdulkareem a tsaye kusa da khairi ya miko mata hannun. A sanyaye khairi ta rike hannun da ya miko mata suka juya lokaci daya suka fara tafiya, suka bar umar sororo a gurin.
Umar ya kasa magana saboda sabon bacin rai da ya shiga wanda ya wuce wanda ya ji a cikin hall din dazu. Hoton yadda khairi ta rike hannun Ak se rewinding yake a kwakwalwar sa. Wani tsananin kishi ya mamaye shi, tabbabs se yayi maganin Ak don ya shige masa hanci da kudindini
Abdulkareem ya bude mata kofar motar sa ta zauna a ciki sannan ya zagayo ya shiga gurin tuki ya ja motar a guje suka bar farfajiyar event center.
Babu wanda yayi magana a cikin su, kowa yana ta sake sake a ranshi. Tun da take bata taba ganin bacin rai irin haka a fuskar Abdulkareem ba ko don shi me fara'a ne da sakin fuska, Yau da ta ga yadda ya hade rai abun yaso ya bata tsoro.
Basu dade da tafiya ba ta fara kuka, kukan na takaici ne. Kukan ne ze samar mata lafiya, shi ze saukar mata da bakin cikin da taji ya tokare mata a kirji.jin sheshekar kukanta ne yasa ba shiri ya nima guri yayi parking a gefen titi
"Ummulkhair"
Ya kira sunanta"Naam"
Ta ansa dukda kukan takeyi"Kalle ni"
A hankali ta dago da kanta ta kalle shi, ta sha kuka don idon duk ya baci da kwalli, eye liner da maskarar duk sun zazzago, se ta koma kamar boka. Kwalliyar da Aunty m ta biya ta tashi daga aiki"me yasa zaki bata hawayen ki a kan wanda be san darajar mutane ba"
Cikin shasheka tace
"Kana ganin abun da yayi min, A cikin mutane fa ya janyo ni kamar wata property dinsa"Ta kara fashewa da kukan. Cikin kukan ta ci gaba da cewa
"I hate him, i hate him wlh. I hate him"
Tayi ta maimaitawa har se da Ak ya ce mata"Shhhhh, ya isa. Hate him as much as you can, ni de burina yanzu kiyi shiru ki dena kukan da kikeyi dan Allah. Bana son ganin ki a cikin yanayin nan"
Haka yayi ta lallashin ta, se da suka shafe kusan minti 30 a gefen titi yana bata hakuri da lallashi.
Da ace yana da dama hannu ze sa ya goge mata hayaen da ke zuba sannan ya janyo ta girjinsa yayi hugging dinta tightly yana lallashinta, kukan ta ya daga masa hankali. Gaba dayan sa a dagule yake.Ba don shi namiji bane ay da taya ta kukan ze yi, don shima ya shiga yanayin da ya kamata ace yayi kukan ko ze samu sassaucin kunar da zuciyar sa takeyi.
Se yau ya tabbatar da shi babban dolo ne, dolon da yayi ta dakon soyyayyar ta na tsawan watanni.Dolon da ya samu dama iri iri da ze iya sanar da ita sirrin zuciyar sa amman beyi ba.
Dolon da ya boye mata identity dinshi saboda tsoron tunkarar ta da zancen soyayya.
Dolon da gata a kusa da shi a yanzu amma har a lokacin ya kasa iya budar baki ya fada mata.
Dolon da ya bari umar ya fara sanar da ita yana son ta kafin shi ya fada mata.
Umar din da be yi cikakken wata 3 da sanin ta ba. umar din da ya tabbatar be san darajar khairi ba, don da ya sani baze jaa ta haka ba a gaban mutane. Sai umar din da ita kanta khairi ba kaunar ganin sa take ba.
🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Bintu. A
09032326763
YOU ARE READING
Sarkakiya
RomanceLabarin tsantsar soyayya me cike da sarkakiya ce ta kullu a tsakanin su. Ummulkhair ta zamo Allura cikin ruwa wanda me rabo ne ze dauka. Shin wa zata zaba a cikin su? Boyayyen masoyi Abdulkareem wanda yayi dakon soyayyar ta na tsahon lokaci ko kuma...