Station

169 7 0
                                    

🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Tun bayan fitar hajja daga dakin Ak ya zama completely useless, ko idanun sa baya san budewa, sallah magrib da isha kadai ya iya tashi yayi, ko abinci be nema ba haka ya kwata.
Washegari hajja tana ta sa idon ta ganshi ya fito be fito ba, ta aika me aikin ta ta kai mishi abinci saboda har yanzu fishi take da shi itama. Abincin kadan ya iya ci sannan yasa me aiki ta fita da sauran, ya ci gaba da kwanciya a daki kamar ruwa sallah ne kadai yake fito da shi, ya kare ranar a haka babu kuzari kwata kwata

A gefan  khairi itama haka ta kwana cike da damuwa, soyayyar Abdulkareem ta dawo mata sabuwa, tasan ba karamin son kai zatayi ba idan tace tana son Ak ya aure ta yanzu da ta zama bazawarar har da yar ta guda

Har aka kwana biyu gaba daya babu walwala a tattare da ita, ba abun da ta bawa mahimanci inba kula da yar ta ba se kuma kwanciya idan zuhra tayi bacci ko tana hannun umma.

Bayan kwana uku da zuwan Ak khairi na zaune a parlor ta saka zuhra a cikin swinger tana mata wasa. zuhra tayi kiba tayi bulbul har a lokacin kamar su daya da umar, ko da ana cewa jarirai na chanza kammanni zuhra bata chanza ba. Babancin ta da umar shine haske, fara ce kal har ta fi mamanta haske. Yarinyar tabarkallah inde kyau ne.

Kallo suke a parlor da ita da hajja da Abdullah, gata de a gaban tv amma bata san me akeyi ba saboda hankalin ta baya wajen. Gani sukayi aminu ya shigo parlor ransa a bace, jiya Aminu ya dawo daga Abuja don Alh ibrahim ya dauke shi aiki a company shima

Umma ta kalle shi
"Kai kuma ya akayi ka shigo mana haka, me ya faru?

Aminu ya karasa kusa da khairi tare da miko mata envelope, khairi ta bude envelope din ta zaro card din da ke ciki. Idanun ta ne yaka kan sunan Abdulkareem nan da nan ta mike tsaye tana kara karanta abun da aka rubuta a jikin card din. Card din invitation ne na auren Abdulkareem.
Umma ta mika hannu ta karbi card din daga hannun khairi da ta sankare a tsaye ta karanta, umma tayi jugum daga baya ta ce da Aminu

"A ina ka samu iv dinnan"

Cikin baccin rai Aminu yace
"Kanin Abdulkareem ne saddiq ya zo har majalisar mu ya bani, ni ban san shi ba ma se da naga kammaninsa da Ak. Tare da fada min bakabken maganganu har yana bani sako na baki cewar dan uwanshi zeyi aure kuma shima yar uwarsa ze aura bayan cuta da yaudarar da mukayi masa  Allah ya saka masa da wadda ta fiki Alkhairi. Ko da basu da kudi su mutane ne masu karamci da mutunci"

Umma ta bude baki
"Au haka ya ce maka shi kanin Abdulkareem din?

"Haka ya fada da wasu bakaken maganganu dan mun kusan kaurewa da dambe yan majalisa suka raba"

Khairi ta fashe da kuka tana cewa umma
"Umma gani sukeyi kamar yaudarar shi nayi, kamar kudi muka bi shiyasa na auri Umar bayan Allah ya sani ba haka bane"

Aminu ne yayi magana cikin fushi
"Suyi ta yi mana me zakiyi da wani Abdulkareem ay kin fi karfin ajinsa wallahi. Dallah kiyi shiru ki dena bata hawayen ki akan yan wahalar nan"

Umma tayi saurin dakatar da shi
"Ya isa haka Aminu ban ga lefin su ba saboda mu muka fara aikata musu ba daidai ba"

"Umma ya zaki ce haka, Aure ba nufi bane na ubangiji? Allah yayi ba matar sa bace ba shikenan ba. mene na zuwa yana fadan bakaken maganganu, shima Abdulkareem ba gashi auren zeyi ba"

Umma ta kara cewe
"Ya isa nace, mu bar maganar nan kawai Allah ya rufa asiri shi kuma Allah ya basu zaman lafiya da matar da ze aura"

Maganar umma ta karshe ce tasa Khairi ta kara realizing da gaske fa auren za'ayi dan gashi har tana musu addu'an zama lafiya. Ji tayi wani zazzafen hawaye ya biyo kuncin ta, da gudu ta bar parlor tayi dakinta. tana shiga ta zauna a gado ta tsurawa iv ido hawaye na sharara, to meyasa zata ji babu dadi bayan shima yana da damar da zeyi aure ya samu farin ciki? She doesn't have the right to be hurt saboda zeyi aure.
Ji take zuciyat ta na zafi, se kuma ta fara tausayin kanta don bata tunanin akwai wani da namiji da zata so a duniya bayan Abdulkareem da umar. She is completely broken.

SarkakiyaWhere stories live. Discover now