Ranar juma'a da azahar khairi ta Isa abuja, bwari ta wuce dan daukar ragowar kayan ta sannan tayi ma su inna asabe sallama. Ta fada musu zata koma gurin aunty ta a cikin garin Abuja. su ma sun dawo daga kano washegarin ranar da khairi ta bar gidan sa'adatu
Tana shiga gidan ta tararkowa na hidiman gaban shi kamar basu san daga tafiya ta dawo ba. Ta gaishe da inna asabe. Inna asabe ta kalle ta a wulakance sanan tace
"Saadatu tace baki da lafiya shiyasa kika tafi kano""Eh.... Eh hakane"
Ta fada har da i'ina. Ta godewa Allah da saadatun ta fadi haka domin kuwa batayi tunanin karyar da zata fada ba idan an tambaye ta.
Daga nan ne ta sanar ma inna asabe cewar zata koma gidan Aunty maimuna a cikin gariInna asabe ta sake tabe baki sannan tace
"Can kuma zakiyi yanzu? a sauka lafiya, umma ta gaida ashha"
Ta fada tare da shiga daki tana hankado labule don haushi, bata ji dadin tafiyar ta ba saboda tasan tana morar ta.A ranar khairi ta bar bwari ta shigo cikin abuja, tare da kwatancen da aunty maimuna tayi mata har ta isa gidan.
Gida ne estate me dan karin kyau, bata taba zuwa gidan aunty maimuna ba se ranar, abujan ma bata taba zuwa ba se a dalilin service
Aunty maimuna kanwar umman su ce ta 4. Ba wata babba bace shekarun ta 32,yaranta ma duk kanana ne. Mijinta kuma ba'a kasar yake aiki ba sede yazo lokaci zuwa lokaci ko su suje su same shi idan anyi hutun makaranta.Estate din hawa 3 ne, gidan aunty maimuna a hawa na biyu yake. Taji dadin zuwan khairi matuka Haka yaran ta ma,
Cikin mita aAunty M tace
"Ay nayi tunanin baza ki zo ba ni da akayi ma alkawarin a nan zaki zauna"Khairi tana dariya ta bata hakuri
"Kiyi hakuri Aunty M, lefin NYSC ne da sukayi posting dinta wajen gari amma daman naso nazo nayi miki sati guda ma""Karyar banza kawai, ni zakiyi ma dadin baki"
Fadin Aunty M
Sukayi ta dariya suna hira gwanin shaawa, haka khairi tayi weekend dinta cikin kwanciyar hankali, har ta fara mantawa da wani Alh Audu.🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Tun asuba Abdulkareem ya tashi ya fara shiri, se zumudi yakeyi. Zumudin da be tabbatar ze ganta ko baze ganta ba, ya shirya tsaf da kayan sa 'one in town' na kasan woredrop. Dark blue din yadi ne anyi masa irin dinkin zamani na south south. Ya ci flat slippers dinsa masu kyau, simple Amma unique. Sannan ya kafa hular sa da tayi dai dai da kayansa. Ya taje Sajen da ya kwanta a fuskarsa.Baki ne shi amma ba wuluk ba. Ba wai wani shahararren kyakkawa bane amma yana da wani sirrin kyawu na daban. Allah ya azurta shi da manyan fararen idanun masu haske
Ba ko wani namiji bane Allah yake masa irin wannan baiwar kyan. Ko a cikin kyawawan akan rasa masu kayun idanun shi masu kunshe da nutsuwa.
Dogo ne sosai don kafin ka samu me tsawon sa ko a cikin maza se an tona. Tabarakallah masha Allah. Ya kai cikakken namiji me kwarjini da haiba.Tunda ya isa office ya kasa tsaye ya kasa zaune, agogon hannun sa kawai yake dubawa restlessly. interview din karfe goma na safe zaa fara, a zuciyar sa se Addua yake Allah yasa ta zo, don idan bata zo ba be san bakin cikin da ze yi ba.
9:00 dai dai na yi ya sauko kasa ya fara safa da marwa a reception. Daga bisani ya koma office ya dauko computer sa sanan ya dawo reception ya zauna a kujerun da aka tanada don baki.
Ya kunna laptop ya fara danne dannen da shi kan sa be san me yake yi ba. hankalin sa yana kan entrance din building din.Daga sama yaji ance
"Good morning sir" ta fada tana murmushi
( ko baa fada ba kunsan mutuniyar ce)"Morning jidda"
Ya maida mata gaisuwan da murmushi"Sir lafiya kake zaune a reception" ta tambaya
Memakon ya amsa mata se ya dora da tashi tambayar
"Masu interview din sun zo ne?""Zuwa na kenan amma banga Alamar su ba , se 10 ne interview by now de ya kamata su fara zuwa" ta fada yana waige waige
Se da ta gama bashi ansa sannan ya tuna itama ta tambaye shi
"Babu network ne"
Ya fada a gajarce"Naam??"
Ta tambaya ciki confusion"Kin tambaye ni me nakeyi a kasa, babu network ne a sama shiyasa na sauko kasa zanyi aiki a computer"
Ya fada a duburburce kamar wanda yayi ma me gari karya"Ohh na gane, ni ma zan hau sama yanzu, take care sir"
Ta fada tare da juyawa ta fara tafiya hanyar bene
Bata so barin shi ba amma dole ta tafi saboda Bata son Alh ibrahim yazo be same ta a office ba.A kullum son shi karuwa ya ke a zuciyar ta. Yau yayi wani irin kyau, Idan zata kwana tana kallon sa baza ta gaji ba. Tana tafe tana juyawa don ta sake kallon shi
Shi kuwa Ak Allah Allah yakeyi ta tafi saboda ya maida hankalin sa akan kofa.
Mutane biyu suka shigo cikin building din sukayi ma receptionist magana. Ta nuna musu guri su zauna a gurin da aka tanada kusa da Abdulkareem. Suma da alama candidates din interview ne
A hankali a hankali mutane sukayi ta shigowa amma be ganta ba, Addua ya ci gaba da yi Allah yasa ta zo dinKarfe 9:45 ta shigo, a hankali take tafiya cikin nutsuwa da kamala. Black Abaya ta saka sannan tayi rolling mayafin abayar a rataya jak a kafadar ta. Fuskar ta kamar ko yaushe babu makeup se kwalli da ta sa a idon, se lip balm dake lips din ta. Yo dama khairi wani kwalliya take bukata.
Tun shigowar ta yake binta da ido, YA SALAM!!!. Gani yayi ta koma masa sabuwa fill, ji yayi ya kara rolla mata, ya kara fadawa tsundum cikin rijiyar kaunar ta wanda babu wanda ya isa ya tsamo shi.
Wayyo Allah wayyo.
Ya ci gaba da binta da ido har taje wajen receptionist sukayi magana sanan ta nuna mata gurin zamaA hankali ta tako har inda kujerun suke. hankalin ta a kwance ta nimi gurin zama.
🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
ASSALAM MASOYA KARATUN LABARIN SARKAKIYA. ALLAH YA KAWO MU LOKACIN DA DUK ME KARANTA LABARIN NAN YAKE JIRA. HADUWAR KHAIRI DA ABDULKAREEM.TO KU SANI FA YANZU AKA FARA. HAUSAWA SUKA CE "WASA FARIN GIRKI"
😂😂😂😂😂
Taku a kullum
Bintu. A
09034346763
YOU ARE READING
Sarkakiya
RomanceLabarin tsantsar soyayya me cike da sarkakiya ce ta kullu a tsakanin su. Ummulkhair ta zamo Allura cikin ruwa wanda me rabo ne ze dauka. Shin wa zata zaba a cikin su? Boyayyen masoyi Abdulkareem wanda yayi dakon soyayyar ta na tsahon lokaci ko kuma...