Tashin Hankali

165 9 0
                                    

🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Alh shehu ya kira Alh wada ya bashi hakuri da cewar su dakata da zuwa goben saboda yar matsala da aka samu. Ko be fadi dalili ba Alh wada ya gane inda maganar ta dosa. Alh wada ya so yaji dalilin cewa su dakata din har ya fara tunanin ko Abdulkareem yayi wani laifin ne. juyin duniyar Alh shehu yace wlh matsalar ba daga gurin Abdulkareem bane, kawai yar matsala ce ta taso daga wajen su shiyasa har aka bukaci su dakata din.

Alh wada ya kira hajja ya sanar da ita abun da aka ciki, hajja bata ji dadi ba kwata kwata amma tayi addua Idan da rabo a tsakanin su Allah ya tabbatar idan babu Alkhairi Allah ya hada kowa da mafi Alhkairi. Alh wada yace da hajja tasan dabarar da za tayi ma Abdulkareem kar abun yayi mishi shock.

Abdulkareem ma a lokacin yana gidan su khairi suna ta zuba love hankalin su gaba daya a kwance.

Khairi cikin muryar shagwaba take magana
"Ni wlh wata biyun nan da kace kamar yayi sauri, ka dan kara zuwa wata 5 haka mana"

Ak yayi murmushi ganin yadda shagwabar tayi mata kyau, gani yayi kamar ta kara kyau kwana biyun da be ganta ba. Yana isowa kano gida yaje yayi wanka sannan ya karaso gidan su khairi.

"Da zaa bi ta ni da yau an daura auren nan a masallacin juma'a"

Khairi ta zare ido
"Haba haba. Kamar wadda akayi sadakan ta"

Suka kwashe da dariya.
"Wa ya isa yayi sadakar ki, Allah ya sakawa Abba da Alkhairi da yayi min Alfarma ya bani ke"

Ak yayi ta tsokanar ta saboda yadda take maganar shagwabar tana birge shi
"Su ummulkhair amare, ni gani nayi ma kamar kin rame"

Khairi ta harare shi
"Ba shiyasa nace maka lokacin yayi min kadan ba, se an kawo maka ni kamar mahaukaciya sannan zaka gane lokacin be ishe ni ba"

Cikin dariya Ak yace
"me yasa zaki fadi haka, ba wani abun wahala ay. Daga mothers eve din da kika ce se daurin aure, ko ba haka kika tsara bikin ba"

Khairi ta kara hararar sa na wasa
"To ay wannan din ma akwai aiki"

"Kar ki damu zan dauki annual leave kafin bikin, duk inda zaki zan zama hand bag dinki"

Suka ci gaba da hira cikin jin dadi da annashuwa tare da tsara yadda suke son bikin nasu ya kasance. Se da suka dade suna hira sannan Ak yayi mata sallama ya koma gida cike da farin ciki

Yadda hajja ta ganshi cikin walwala tasan be san abun da aka tattauna ba.
Ya cire kwalliyar da yayi ya sako jallabiya sannan yazo ya samu hajja a parlor an jera masa abinci akan carpet
Ak ya zauna tare da bude flask din da hajja ta jere sannan yace
"Hmm shiyasa nake ta jin kamshi na tashi tunda na shigo ashe masa ( wainar shinkafa) kikayi mana, banyi niyar cin abinci ba da yawa ba amma ganin masar nan se naji sabon yunwa"

Ak ya zuba wainar shinkafa da miyar taushe yaci sosai saboda yana son masa, masar ma irin tasu ta mutanen Azare na bauchin yakubu.

Se da hajja ta bari ya ci abincin sosai sannan ta fada masa abunda Alh wada ya fada mata cikin magana me kwantar da hankali

"Hajja ban gane a dakata da zuwa gobe ba, akwai wani mtsalar ne? da na je gidan su khairi ma bata nuna min akwai wata matsala ba fa. Kuma har abban ma mun hadu da shi a massalaci mun gaisa kuma banga chanji a fuskar sa ba"

Hajja ta nisa sannan tace
"Ko basu gama shiryawa bane, kaima kace aure wata biyu kamar tashin duniya. kasan shaanin aure se an shirya fa"

Ak ya girgiza kansa tare da fadin
"Aa hajja ba wannan bane dalili , nide ina tunanin akwai wata matsalar.

Ak ya dauko wayar sa ya kira khairi ya fada mata abun da hajja ta fada masa. Itama khairi tayi mamaki saboda babu wanda ya fada mata a gida daga abba har umma. Cikin tashin hankali ta samu abba a parlor se kuma ta kasa tambayar sa saboda kunya, se gwalala ido take.

SarkakiyaWhere stories live. Discover now