Gyara

184 12 0
                                    

🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
"Yaya Ummulkhairi?"

Alh ibrahim ya tambayi jidda da ke zaune a kujerar da ke kallon sa

"Lafiya qalau sir, nothing out of the ordinary"
Jidda ta amsa masa

Alhaji yaja dogon numfashi sannan yace
"Ina so a maida ta matsayin secretary din umar, ina so ta saba da aiki da shi kafin lokacin anniversary"

Alh ibrahim ya fada ba tare da wasa a fuskarsa ba
Jidda da ke zaune batayi mamaki ba domin tasan target dinsa baze wuce akan umar ba. Tun bayan tafiyar tsohuwar secretary sa maryam baa kara bashi wata secretary ba.
Tun sanda Alh ibrahim  yace a dauke khairi a aiki tasan saboda umar yayi hakan. Ta dade tare da ogan nata zata iya gane motive dinshi ko beyi magana ba

"Okay sir"
Jidda ta ansa domin tasan umarni ne ya bayar ba shawara yake nima ba.

Tana zuwa office dinta ta kira human resource ta fada musu abunda Alh yake so ayi don su karasa formalities din. Babu wanda ya isa ya tanka umarnin sa, sun san khairi a matsayin copper take a company ba ma cikakkiyar ma'aikaciya ba, akwai mamaki ace an bawa copper matsayin secretary, secretary din ma ta MD. To amma wa ya isa ya ja da EXECUTIVE DIRECTOR. CEO din company gaba daya

Alh ibrahim yaso ta karasa service dinta a office din su mr peter (planning department) . Idan an dauketa full aiki kuma se a dauke ta a matsayin secretary ta umar. Amma da dukkan alamu lokaci yana kure masa domin ya fara ganin alamun shirye shiryen da umar yakeyi ta karkashin kasa, Shiyasa ya zabi Ummulkhairi saboda rashin tsoron ta, yasan itace zata iya handling umar a matsayin secretary.

🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒

Ummulkhairi na zaune a office  suna wani aiki da intisar a computer  jidda ta shigo office dinsu da takarda a hannun ta.
Jidda kan kiyaye abinda ze hada ta da khairi, saboda duk sanda ta ganta se ta tuno rawar kan da AK yake yi a kanta kuma abun bakanta mata rai yakeyi.

Khairi na  ganin ta ta washe baki sanna ta gaishe ta,  a girme jidda zata girmi khairi don jidda ta kai shekara 29, Ita kuwa khairi na 23

Jidda ta ansa da sakin fuska amma ta kasa maida mata murmushin, Allah Allah takeyi tayi abunda ya kawo ta ta bar kusa da khairi

"An canja miki aiki zaki koma wani office din yanzu, na riga nayi magana da mr patric so daga gobe zaki koma sabon office din da aka maida ke"
Jidda ta fada tare da miko mata takarda, khairi ta mika hannu ta karba sanna tace

"Ina aka maida ni"

"Ki bude cikin takardar zaki ga komai"
Jidda ta bada ansa tana tafiya saboda magana da khairi ma haushi yake bata. Bata son kara minti daya a kusa da ita.

Itisar ce tayi wuff ta karbi takarda tana kokarin dubawa
"Ina aka maida ki kuma......."
Idanun intisar ne suka fito zuru zuru kamar taga horror  ganin  abunda aka rubuta a cikin takardar
Khairi ta matso ta karba

"Me ya faru naga fuskarki haka"
Itama ta fara karanta abunda aka rubuta a takardar

"Secretary kuma???" Ni aka bawa secretary? Meyasa to, yaushe ma na fara aiki?
Khairi ta fada fuska cike da mamaki.

"Ba zama secretary bane ze baki mamaki, zama sacretary MD ne ze baki mamaki"
Intisar ta answer mata

"MD kuma?"
khairi ta kara tambaya cikin mamaki sanan ta ci gaba

"Waye MD din, anya ma ni aka kawowa paper nan kuwa"
Khari ta fada tana sake karanta abun da aka rubuta a zuci

"Kece mana, ga sunan ki a jikin takardar"
Intisar  ta nuna mata inda aka rubuta sunan ta a jikin paper sanna ta ci gaba

"Hmm kina da babban aiki a gaban ki, kin san waye MD kuwa"

"waye shi"
Khairi ta tambaya

"Mutum ne me wuyar sha'ani, Allah ya baki ikon iya aiki da shi kawai"

Intisar tana gama magana mr patric ya kirata ta tafi ta bar khairi da takarda a hannu, Khairi ma ajye takardar tayi ta ci gaba da aikin da takeyi, koma yaya boss din nata yake idan Allah ya kaimu gobe ta ganshi. Amma a bayan ranta tana son sanin meyasa intisar ta fadi hakan

Washe gari da wuri ta zo gurin aiki, bata san office din MD din base da ta tambayi mahmud abokin aikin ta sannan ya kwatanta mata. office din secretary ne a farko sannan office din MD a jikin sa. Kowani office akwai kofar sa daban ta waje sannan ta ciki akwai kofar da ta hada su. Ta cikin office din secretary zaka iya shiga office din MD.

Tana shiga ta tarar da ko ina da kura kamar wanda aka shekara baa share ba ga takardu an wargatse a kasa, office din kwata kwata kamar baa company ba. Ta murda kofar office din MD taji a kulle.
Ko de MD din baya gari ne shiyasa office din baa share shi. Ta gama tunani tunanin ta sannan ta sa sauka kasa, a kasa taci karo da jidda tana cika tana batsewa. Ta gaishe da ita sannan ta sanar mata yadda ta ga office din, jidda tace zata turo cleaners su zo su gyara

Khairi ta dawo office ta tsaya saboda babu wajen zama ko ina da kura.
Bayan minti kadan cleaners 2 suka shigo gyara gurin, suka gaishe da khairi sannan suka fara aikin su.

Suka gama gyara office din khairi sannan tace musu
" ina so a gyara cikin office din can shima"
ta nuna office din umar

Daya daga cikin cleaners din ya  karbo  spare key aka bude office din umar suka fara gyara shi, khairi ta bisu cikin office din tana ganin yadda suke gyarawa
"Ya akayi baa gyara gurin nan"
Khairi ta tambaye su

"An ce mu dena shiga gyara office dinne shiyasa"
Daya daga cikin Cleaner ya bata answer

"Wa ya hana gyarawa"

"MD din da kansa"
Ya amsa mata tambayar da tayi

Shiru tayi don bata san me zatace ba kuma, lallai ta tafka babban kuskure a ranar ta ta farko garin iyayi. Ita batayi tambaya ba tayi gaban kanta

"Yana gari ne"
Ta tambayi cleaners din

"Eh yana nan"

Dankari kenan!! Amma ya zaayi mutum ya zauna da datti haka, wani irin kazami ne MD din,  fatan ta de Allah yasa ba lefi tayi ba da tasa a gyara office din, baza ta iya aiki a office da datti haka ba. Tana cikin wannan tunanin ne taji an murdo kofa. Da wa Allah ya hada ta.... UMAR!!!!

🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Bintu. A
09034346763

SarkakiyaWhere stories live. Discover now