Chanjin yanayi

206 6 0
                                    

Haka ya cire kayansa ya maida jallabiya ya koma gado ya kwanta. Ranar gaba daya kasa moruwa yayi, hajja ma ta dauka ya wuce Abuja sa se da akayi kiran la'asar sannan taga ya fito daga dakin da jallabiya ze je massalaci.
Hajja ta wangale baki
"Ai daman ba tafiyar kayi ba?"

Ak ya sosa kai sannan yace
"Wani abu ya tsare ni amma gobe zan tafi insha Allah, naji an tada ikama bari nayi sauri"

Hajja ta kalle shi tana mamakin sabon halayar da ya dauka. Se ta kira me aikin ta tace ta shirya masa abinci a kai dakin sa.
Ak yana dawowa daga massalaci ko abincin be kula ba ya zuba shadar sa da hula ya shiga mota se hanyar gidan su khairi.
Yana cikin tuki yaji an kira shi, be tsaya duba waye ba ya d'aga saboda hankalin sa yana kan tukin da yake

"Assalamu Alaikum"
Muryar maryam yaji tayi sallama a sanyaye, ya dago da wayar ya kalli screen don ya tabbatar ita din ce, b wayar ya speaker ya ajye a cinyar sa, jin shirun yayi yawa ne yace

"Ina jin ki maamah, ya akayi?"

A dayan bangaren maganar da yayi has completely shattered her broken heart, wai wannan ne mijin da zata aura nan da kwana biyar. Yadda taji tambayar da yayi mata kamar irin damun shi take

Da kyar ta iya tattaro courage tace
"Dan Allah yaya ina so muyi magana ne, idan kana da lokaci ko zaka iya zuwa gidan mu?

Fuskar Ak a daure yace
"Ina yin wani abu ne yanzu bazan samu damar zuwa ba gaskiya"

Kwallar da maryam take ta tare wa ce ya tsiyayo daga idanun ta, tayi shiru na dan lokaci sanan ta share hanci irin na masu kuka sanna tace

"To shikenan yaya nagode"
Tana gama fadin haka ta kashe wayar.

Bayan ta kashe wayar se kuma yaji ba dadi saboda yaji kamar kuka take, be saba yi ma mutane rashin mutunci ba shiyasa yaji gaba daya babu dadi.
Wayarsa ya dago sannan yayi dailing number ta

Bugu na farko na biyu yaji maryam ta dauka, be bari tayi magana ba yace
"Gani nan karasowa nan da minti 10, ina sauri ne dafatan maganar taki baza ta dauki lokaci ba"

"Baza ta dauka ba Insha Allah"
Ta fada a sanyaye.

******* Bayan wata 6 *******

A zaune take an yaryada mata lalle kafa da hannu fuskar ta cike da fara'a. Duk wanda ya ganta yasan tana cikin matsanaicin farin ciki.
Umma ce ta goya zuhra tana ta rigima se taje gurin mamanta

"Wai lallen nan awa nawa ake so yayi ne, ukhty ta gaji wallahi awa nawa ana abu daya"

Khairi tayi murmushi sannan tace
"So nake lallen ya kama sosai n, ita ma rigima ce kawai ba ta ci abin ci ba, ni me zan mata yanzu"

Kawar khairi bilkisu tace da umma
"Rabu da ita umma kinsan jin kanta take wai ita amarya"

Khairi tayi wani murmushi tare da rolling idanun ta tana fadin
"Gulmammiya se kiyi ay"

Ana cikin haka wayar khair da ke cinyar ta tayi kara, khairi tace da bilkisu
"Billy dan Allah daga ki sa min wayar a kunne"

Billy ta daga mata wayar ta sa mata a kunne, daga billy har me lallen se dariya suke. Billy tace da me lallen,
"Su gama wayar nayi musu bill din daga wayar nan da nake, waya taki karewa minti daya minti biyu se ya kira"

Khairi ta harareta sannan ta maida hankali a kan habibinta da ya kira

"Kin ci abincin kuwa?"
Tambayar da Abdulkareem yayi mata kenan

Cike da shagwaba khairi tace
"Ina naci bilkisu se wulakanci take min wai baza ta bani a baki ba"

Billy ta hangame baki jin yadda khairi zata kulla mata sharri sannan tace
"Ahh lallai sharrin da zaki min kenan? To ki fada mishi ga abincin a gaba na wayar da yakeyi bini bini ne baze bari ma kici abincin ba. Lefin ba nawa bane nashi ne"

SarkakiyaWhere stories live. Discover now