Dalili

170 8 0
                                    

🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Bayan tafiyar umar khairi ta sake ta wala a gidan ita da bashariyya. Daman tun tafiyar sa taje ta samu maman bashariyya ta roke ta ta bar ta suna kwana kafin umar ya dawo. A kasan ranta tasan gidan ya zama boring ta fara missing dinsa amma a zahiri taki accepting haka.

Kullum da safe Abdullah ze zo su fita koyan mota tare, da tsoro da tsoro har hannun ta ya fara kwari. Kafin tafiyar umar ma ya sa a gyara gidan su khairi, ya siya gidan dake jikin nasu an hada duka biyun an bige zaa daura sabon gini.
Su umma suka koma family house da zama kafin a gama nasu. Takan je gidan jifa jifa tayi hira sannan ta dawo, haka umma zata tayi mata nasiha da lallashi, hade da lallama tabi mijin ta.

Rayuwar ta ta fara daukar seti, ta mayar da komai ba komai ba ta rungumi kaddarar ta.
Umar Sati daya shiru, sati biyu shiru kai har wata daya shiru, gashi tun da ya tafi be kira ta a waya ba, tun bata damuwa har ta fara damuwa ko lafiya.Se da umar yayi wata 2 cif cif ba tare da kira ba ko wani bayani, ranar da taje gida umma take tambayar ta yaushe umar ze dawo tayi mata karyar se wani satin saboda bata so ta nunawa iyayen ta ko waya basa yi. Ya saba mata da presence dinshi yanzu ya barta da kewar shi.

ranar wata Alhamis da yamma tana zaune taji kira da number da bata sani ba. Ta daga tare da sallama, mutumin ya ansa mata sallama tare da cewa
"Sunana ibrahim mijinyawa"

Nan da nan gaban ta ya fadi, rabon ta da Alh tun a company. Har akayi auren aka gama bata ganshi ba, bayan auren ma be taba kiran ta ba balle itama tayi tunanin kiran shi, daman a kullace take da shi tun abun da ya faru na case din SS.

Khairi ta gaishe da Alh sannan tayi shiru tana sauraron me ze ce
" zan turo wani gidan ku gobe insha Allah, ze kai ki immigration office saboda ina so ayi miki visar tafiya US. Ina so kizo ki samu mijin ki"

"Khairi cikin mamaki tace
"to Alh Allah ya kaimu goben dafatan komai lafiya?"

Alh ya danyi murmushi tare da fadin
"Lafiya idan kika zo zaki ji komai"

Sukayi sallama da khairi sannan ta zauna tana tunanin meyasa zata tafi US. Me yasa umar be kira ta ba se Alh ibrahim. A yadda umar yake nuna yana son ta bata taba tunanin ze iya kwana ba tare da ya kira ta ba amma se gashi har sunyi wata biyu be kira din ba.
Taso ta kira ta ji ya yake amma bata san number nashi na can ba, kuma tayi mishi magana ta whatsapp kwanaki amma babu reply dan ko gani beyi ba balle tayi tunanin ze bata ansa.

Washe gari da safe Alhaji ya turo wani har gida ya kaita immigration office suka gama process din capturing data da komai a kwana 2. Bayan sati 2 kuma komai nata ya zama ready har da tickets dinta a hannu

Ranar tafiya Khairi tayi sallama da kowa a gida, daga nan Abdullah ya kaita Airport. Tana ta fargaba saboda yau ne ranar da zata taba hawa jirgi, tana ta tsoron kar ta kwafsa. Cikin yardar Allah komai ya zo mata da sauki tun Daga boarding, luggage clearance, Immigration komai de Alhamdulillah.
Tun tana kirga awoyin da suka rage suyi landing har ta hakura ta dena. Tafiya ce me nisan more than 9 hrs gashi Sunyi transit a Ethiopia tunda ethiopian airline ta shiga, suka kara tsayawa Amsterdam Diban wasu passengers Daga nan basu kara tsayawa ba se a Hartsfield Jackson international airport da ke Atlanta Georgia.

A Airport ta tarar da wanda Alh ibrahim yasa ya jira ta, shima bahaushe ne. Taji dadin yadda yayi mata sorting luggage da komai de komai sannan ya tare musu taxi daga airport ya fada masa inda ze kaisu.

Taxi ya ajye su a gaban wani dogon gini a jiki an rubuta Emory University hospital, Ahmad Yayi leading hanya har suka shiga asbitin Tana ta mamakin me ya kawo su asbiti.
ba wajen umar za'a kai ta ba? Kode umar dinne ba lafiya. Haka tayi ta tunanin har suka hau elevator zuwa dakin da zasu je.

A bakin kofar dakin Ahmad ya tsaya sannan yace mata zata iya shiga ciki, khairi ta bude kofar dakin a hankali tare da zura kai tana lekawa.
A kwance ta hango umar a kan gadon asbiti idanun sa a rufe alamar bacci yake, A jikin hannun sa kuma igiya ce sakale da ledar jini ana masa blood transfussion.

SarkakiyaWhere stories live. Discover now