Aura

196 14 0
                                    

🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Silver construction company suna da wani al'ada da duk sabon maaikaci da yazo company se ya horu da aiki, yanayin juriyar ka ne ze sa ka samu ci gaba da karin girma.

Tunda Abdulkareem ya rako khairi daga karban abinci ya kulla alaka da reception. Bini bini za'a ganshi ya sauko kasa yana shawagi har Allah yasa yaci karo da ita, wani lokaci har office dinsu yake shiga yayi zagaye da gaishe gaishe sannan ya fito duk dan ya ganta. Shi kanshi mr patric yana mamakin yawan shigowar sa office din har ya fara tunanin ko Yana supervising aikin da sukeyi ne

Duk sanda Ummulkhairi ta ganshi zatayi masa murmushi idan suna kusa ma har ta gaishe shi, Wani lokacin ma buya yakeyi kar ta ganshi, ya fi so shi yayi ta kallon ta ba tare da sanin ta ba

Khairi bata san sunan sa ba amma ta tabbatar a office din yake aiki amma bata san wani aiki yakeyi ba. Tun ranar da ya taimake ta take gaishe shi idan ta ganshi. 

Tun barin ta bwari secret admirer ta ya dawo yi mata messeges abun har ya fi na da ma. A rana se yayi mata message sau 20, kamar bashi da wani aiki se yi mata message.
Yau ma haka ya turo mata message cewar

" whenever i see you. My heart race's and whenever I talk to you my heart melts"

Murmushin mugunta tayi zaka ga melt kuwa ba se ka kara gani ba tukuna ta fada a ranta.
Ta tura wayar a jakar ta sannan ta nufi hanyar fita daga building din, yau da wuri ta gama aiki ta fito dan tafiya gida. A bakin titi ta a tsaya neman adaidaita sahu dayake office din a bakin titi yake, bata cika dadewa ba take samun abun hawa amma yau abun mamaki babu motoci sosai a titin.
Tana tsaye taji tsayuwar mota a gabanta, a hankali glass din motar ya sauka. Khairi tayi saurin hade rai duk da bata ga mutumin da ke motar ba.

"Barka da rana..... emmmm ..... tafiya zakiyi ne?
Abdulkareem ya tambaya kamar me jin tsoron yi mata magana , tun da yaga ta hada rai ya ji tsoron yi mata magana. Yana ganin ta fito ya labe yayi mata message. da ya ga alamar tafiya zatayi shiyasa ya dauko motar sa ya biyo ta don ya gwada sa'ar sa.

Tana ganin shi ne ta saki murmushi
"Ina yini sir"
Ta gaishe shi da fara'a

Murmushin da tayi ne yasa zuciyarsa ta sake hankalin sa ya kwanta. Shima murmushin yayi mata sannan ya ansa
"Lafiya kalau, tafiya zakiyi ne"

"Eh"
Ta ansa a takaice.

"Bari na rage miki hanya"
Yana magana yana kallon yanayin fuskarta kar ya fusata ta.

"Aa, ba komai zan hau adaidaita sahu, nagode sosai"
Khairi ta bashi answer tare da murmushi.

Abdulkareem ya tsaya shiru bayan minti kadan cikin murya me cike da karaya da disappointment yace

"To shikenan..... se gobe"

"Allah ya kaimu"
Khairi ta amsa tare da murmushi

Cikin sanyi jiki ya ja motar sa ya bar gurin, baya so ya sa tayi abun da batayi niya ba amma yaso ta shiga motar sa ya kaita gida

Bayan tafiyar Abdulkareem ta ci gaba da tsayuwa a gurin tana jiran adaidaita sahu. Daga gefen ido ta hango mota tana tunkarar ta, ta dauke kanta har motar ta karaso ta tsaya a gaba da ita, a ranta ta fara tunanin waye ya tsaya kuma.

Bayan minti kadan taga umar ya ya nufo inda  take tsaye, kallo daya yayi mata ya watsar. Ita ma kuwa kallon banza ta bi shi.
Se da yazo daf da ita sannan ya juyo ya kalleta, a lokacin itama shi din ta kalla Idonsu ya hadu,
A take taji gabanta ya fadi , Tayi saurin kawar da kanta daga kallon sa ta fara kallon wani gurin daban

Duk da mumunan faduwan da gabanta yakeyi be hana ta mazewa ba ta kara hade rai.
Umar ya wuce ta ya shiga bayan motar da ta tsaya sannan me motar yaja suka tafi.

Suna tafiya ta sauke nauyeyen ajiyar zuciya, wannan wani irin mutum ne, duk lokacin da ta hadu da shi se taji wani irin yanayi. Gaba dayan sa kamar ba mutum ba. Wani irin cold aura yake emitting wanda ke tsinkar da  zuciya. Tana son sanin waye shi, tana son sanin abubuwa da dama game da shi.

Se da tayi kusan minti 20 a tsaye a bakin titin, ta manta ma adaidaita sahu take nema, ta fada wani tunanin daban. Daga bisani kuma ta tare wani empty adaidaita ta shiga.

Abdulkareem da daman ganin fitar ta ce tasa ya dauko mota ya biyo ta, da ta ki shiga motar ya tafi yayo U turn ya dawo company, parking motar sa a can nesa yadda bazata ganshi ba. So yake yaga tafiyar ta shiyasa ya tsaya se yaga ta hau mota tukunna. Ya ga lokacin da umar ya fito, yaga irin kallon da sukayi ma juna duk da kallo ne na dan sakwanni, kallon da umar yayi mata  yasa yaji zuciyar sa ta sosu.

🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Bintu. A
09034346763

SarkakiyaWhere stories live. Discover now